عَنْ سَهْلِ بْنِ سَعْدٍ السَّاعِدِيِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «رِبَاطُ يَوْمٍ فِي سَبِيلِ اللَّهِ خَيْرٌ مِنَ الدُّنْيَا وَمَا عَلَيْهَا، وَمَوْضِعُ سَوْطِ أَحَدِكُمْ مِنَ الجَنَّةِ خَيْرٌ مِنَ الدُّنْيَا وَمَا عَلَيْهَا، وَالرَّوْحَةُ يَرُوحُهَا العَبْدُ فِي سَبِيلِ اللَّهِ أَوِ الغَدْوَةُ خَيْرٌ مِنَ الدُّنْيَا وَمَا عَلَيْهَا».
Daga Sahl ɗan Sa'ad al-sa'idi - Allah Ya yarda da shi - lallai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Zaman dakon yini ɗaya saboda Allah shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke kanta, kuma bigiren bulalar ɗayanku a aljanna shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke kanta, yammacin da bawa zai yi shi saboda Allah ko jijjifi shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke kanta".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa lazimtar gurin da yake tsakanin musulmai da kafirai dan gadin musulmai daga gare su a yini ɗaya yana mai tsarkake niyya saboda Allah, shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke cikinta, kuma bigiren bulalar da zai yi yaƙi da ita saboda Allah a cikin aljanna shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke cikinta, kuma lallai cewa lada da sakamakon tafiya a cikin lokaci daga farkon yini zuwa farkon lokacin azahar, ko yammaci: Daga lokacin azahar zuwa dare saboda Allah sau ɗaya, shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke cikinta.
Fa’idoji
- Falalar zaman dako saboda Allah, dan abinda ke cikinsa na sadaukar da rai, dan kuma abinda yake jerantuwa a kansa na ɗaukaka kalmar Allah da taimakon AddininSa; saboda haka lallai sakamakon yini ɗaya, shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke cikinta.
- Wulaƙantar duniya dangane da lahira; domin cewa gurbin bulala na aljanna shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke cikinta.
- Falalar yaƙi saboda Allah, da girman ladansa; domin ladan yammaci ɗaya ko jijjifi ɗaya shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke cikinta.
- Faɗinsa; "Saboda Allah" A cikinsa akwai nuni akan muhimmancin tsarkake niyya, kuma cewa lada mai jerantuwa ne a kansa.
Madogara
صحيح البخاري (4/ 35) (2892).
صحيح مسلم (3/ 1500) (1881).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص739).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن كَعْب بن مالك رضي الله عنه قال: قلتُ: يا رسولَ الله، إن مِن تَوبتي أن أَنْخَلِعَ مِنْ مالي؛ صدقةً إلى الله وإلى رسولِه، فقال رسولُ الله صلى الله عليه وسلم : "أمسِكْ عليك بعضَ مالِكَ؛ فهو خيرٌ لكَ".
Daga Ka'ab Bn Malik -Allah ya yarda da shi- ya ce: na ce: ya manzon Allah lallai ne daga cikin tuba na in rabu da dukkan Dukiya ta; Sadaka saboda Allah da Manzon sa, sai manzon Allah SAW ya ce: "Ka riqe wani vangaren na dukiyarka yafi maka Al-kairi"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara
-صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422ه.
-صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، 1423هـ.
-عمدة الأحكام من كلام خير الأنام صلى الله عليه وسلم لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، ط2، دار الثقافة العربية، دمشق ، بيروت، مؤسسة قرطبة، 1408هـ.
-تأسيس الأحكام للنجمي، ط2، دار علماء السلف، 1414ه.
-تيسير العلام شرح عمدة الأحكام للبسام، حققه وعلق عليه وخرج أحاديثه وصنع فهارسه: محمد صبحي بن حسن حلاق، ط10، مكتبة الصحابة، الأمارات - مكتبة التابعين، القاهرة، 1426هـ.
-الإلمام بشرح عمدة الأحكام, إسماعيل الأنصاري, الطبعة الثانية 1392هـ.
-الشرح الممتع على زاد المستقنع، محمد بن صالح بن محمد العثيمين، دار ابن الجوزي، الطبعة: الأولى، 1422- 1428هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المؤْمِنين رَضيَ اللهُ عنها قَالَتْ: جَاءَتْنِي مِسْكِينَةٌ تَحْمِلُ ابْنَتَيْنِ لَهَا، فَأَطْعَمْتُهَا ثَلَاثَ تَمَرَاتٍ، فَأَعْطَتْ كُلَّ وَاحِدَةٍ مِنْهُمَا تَمْرَةً، وَرَفَعَتْ إِلَى فِيهَا تَمْرَةً لِتَأْكُلَهَا، فَاسْتَطْعَمَتْهَا ابْنَتَاهَا، فَشَقَّتِ التَّمْرَةَ الَّتِي كَانَتْ تُرِيدُ أَنْ تَأْكُلَهَا بَيْنَهُمَا، فَأَعْجَبَنِي شَأْنُهَا، فَذَكَرْتُ الَّذِي صَنَعَتْ لِرَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: «إِنَّ اللهَ قَدْ أَوْجَبَ لَهَا بِهَا الْجَنَّةَ، أَوْ أَعْتَقَهَا بِهَا مِنَ النَّارِ».
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce : Wata miskiniya ta zo wurina tana ɗauke da 'ya'yanta mata biyu, sai na ciyar da ita dabinai uku, sai ta ba wa kowacce ɗaya daga cikinsu su biyun dabinon, sai ta ɗaga dabino zuwa bakinta don ta ci, sai 'ya'yan na ta mata biyun suka nemi ƙara ci daga gareta, sai ta raba musu dabinon da ta so ta ci a tsakaninsu, sai sha'anin ta ya ƙayatar da ni, sai na gaya wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - abin da ta aikata, sai ya ce: «Lallai haƙiƙa Allah Ya wajabta mata Aljanna da shi, ko kuma Ya 'yanta ta daga wuta da shi».
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ambaci cewa wata mata miskiniya tana ɗauke da 'ya'yanta mata biyu sai ta tambayeta, sai ta bata dabinai uku, sai ta bawa kowacce daga cikin 'ya'yan nata mata biyu dabino ɗaya, kuma ta ɗaga ɗayan zuwa bakinta dan ta ci shi, sai 'ya'yan nata mata biyu suka nemi dabinon da take nufin cinsa, sai ta raba dabinon a tsakaninsu, sai lamarinta ya ƙayatar da Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita -, kuma ta faɗawa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - abinda matar ta aikata, sai ya ce: Lallai haƙiƙa Allah Ya tabbatar mata aljanna saboda wannan dabinon, ko kuma ya 'yantata daga wuta.
Fa’idoji
- Falalar sadaka ko da ta kasance kaɗan ce, kuma ita tana nuni akan gaskiyar mumini a cikin imaninsa da Ubangijinsa da kuma amincewarsa ga alƙawarinsa da kuma falalarsa.
- Tsananin jin ƙan iyaye mata ga 'ya'yansu da kuma jin tsoron tozarci garesu.
- Falalar fifita wani akan kai, da kuma jin ƙan yara ƙana, da ƙarin kyautatawa da kuma rangwami ga 'ya'ya mata, kuma cewa hakan sababi ne na shiga aljanna da kuma 'yantuwa daga wuta.
- Kaɗan ba ya hana a yi sadaka da shi saboda ƙanƙantarsa, kai yana kamata ga mai yin sadaka ya yi sadaka da abinda ya sawwaƙa gare shi ya ƙaranta ne ko yana da yawa.
- A cikinsa akwai bayanin abinda ɗakunan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - suke akai kuma ya rayuwarsa take tare da iyalansa alhali a cikin gidansu babu abinda za'a ci inba dabino ba ko dabinai uku.
Madogara
صحيح مسلم (4/ 2027) (2630).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص199).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 111).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 278).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي هريرة رضي الله عنه مرفوعًا: «يقول الله تعالى : ما لِعَبدِي المُؤمن عِندِي جَزَاء إِذَا قَبَضتُ صَفِيَّه مِنْ أَهلِ الدُّنيَا ثُمَّ احْتَسَبَه إِلاَّ الجنَّة».
Daga Abu Hurairah - yardar Allah ta tabbata a gare shi - da isnadi: "Allah Madaukaki Ya ce: Babu wani sakamako ga bawa na mumina idan na kame darajojinsa na mutanen duniya sannan na dauke ta sai Aljanna."
Buhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي، ط1، دار ابن الجوزي، الدمام، 1415هـ.
رياض الصالحين للنووي، ط1، تحقيق: ماهر ياسين الفحل، دار ابن كثير، دمشق، بيروت، 1428هـ.
رياض الصالحين، ط4، تحقيق: عصام هادي، وزارة الأوقاف والشؤون الإسلامية القطرية، دار الريان، بيروت، 1428هـ.
كنوز رياض الصالحين، مجموعة من الباحثين برئاسة حمد بن ناصر العمار، ط1، كنوز إشبيليا، الرياض، 1430هـ.
شرح رياض الصالحين، للشيخ ابن عثيمين، دار الوطن للنشر، الرياض، 1426هـ.
صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422هـ.
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين، ط14، مؤسسة الرسالة، 1407هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ ثَوْبَانَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَفْضَلُ دِينَارٍ يُنْفِقُهُ الرَّجُلُ، دِينَارٌ يُنْفِقُهُ عَلَى عِيَالِهِ، وَدِينَارٌ يُنْفِقُهُ الرَّجُلُ عَلَى دَابَّتِهِ فِي سَبِيلِ اللهِ، وَدِينَارٌ يُنْفِقُهُ عَلَى أَصْحَابِهِ فِي سَبِيلِ اللهِ» قَالَ أَبُو قِلَابَةَ: وَبَدَأَ بِالْعِيَالِ، ثُمَّ قَالَ أَبُو قِلَابَةَ: وَأَيُّ رَجُلٍ أَعْظَمُ أَجْرًا مِنْ رَجُلٍ يُنْفِقُ عَلَى عِيَالٍ صِغَارٍ، يُعِفُّهُمْ أَوْ يَنْفَعُهُمُ اللهُ بِهِ وَيُغْنِيهِمْ.
Daga Sauban - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mafificin dinaren (kudi) da mutum zai ciyar da shi: Dinarin da ya ciyar da shi ga iyalansa, da dinaren da mutum yake ciyar da shi ga dabbarsa a tafarkin Allah, da dinaren da yake ciyar da shi ga abokansa a tafarkin Allah" Abu Kilaba ya ce: "Sai ya fara da iyali, sannan Abu Kilaba ya ce: Kuma wanne mutum ne mafi girman lada kamar mutumin da yake ciyar da iyali ƙanana don ya rufa musu asiri ko Allah Ya anfanar da su da shi, kuma ya wadata su".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
(Annabi) tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi ya bayyana wasu Nau’uka a cikin ciyarwa, ya kuma jerantasu idan fuskokin ciyarwar sun gagara gwargwadan mafi wajabci akanka, sai ya fara da mafi muhimmanci sai mafi muhimmanci; sai ya sanar da cewa mafi yawan dukiya a lada ita ce wadda musulmi yake ciyar da ita ga wanda ciyarwarsa ta wajaba akan shi; kamar mata da ɗa, sannan ciyarwa ga abin hawa wanda aka tanada dan yaƙi a tafarkin Allah, sannan ciyarwa ga abokansa da ayarinsa a halin kasancewarsu mayaƙa a tafarkin Allah.
Fa’idoji
- Jeranta ciyarwa a falala ta fuskar da aka ambata, sai a lura da hakan a lokacin da suka taru.
- Bayanin cancantar ciyarwa ga iyali a falala akan wasunsu.
- Ciyarwa a yaƙi saboda Allah tana daga mafi girman ciyarwa, kamar tanadar kaya da mayaka a Jihadi.
- An ce: Abin nufi da tafarkin Allah dukkanin aikin ɗa'a kamar aikin hajji a misali.
Madogara
صحيح مسلم (2/ 691) (994).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (5/ 315).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 156).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 291).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 374).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «لَا تَجْعَلُوا بُيُوتَكُمْ قُبُورًا، وَلَا تَجْعَلُوا قَبْرِي عِيدًا، وَصَلُّوا عَلَيَّ؛ فَإِنَّ صَلَاتَكُمْ تَبْلُغُنِي حَيْثُ كُنْتُمْ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kada ku maida gidajanku kaburbura, kuma kada ku maida kabari na idi, ku yi salati a gareni; domin cewa salatinku a gareni yana isomin a duk inda kuke".
Abu Dawud ne Ya Rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana yin hani daga wofintar da gidaje daga sallah sai su zama kamar makabartu, da ba'a sallah a cikin su. Kuma ya yi hani daga maimaita ziyarar wani kabari da taruwa a wurinsa ta fuskar al'ada; domin hakan hanya ce zuwa ga shirka, Ya yi umarni da yin salati da sallama a gare shi a kowane wuri anan doron kasa; domin cewa hakan yana isa gare shi daga na kusa da na nesa duk daya ne, babu bukatuwa zuwa kaikawo a kabarinsa.
Fa’idoji
- Hani daga wofintar da gidaje daga bautar Allah - Madaukakin sarki -a cikinsu.
- Hani daga tafiya dan ziyarar kabarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -; domin cewa shi ya yi umarni da yin salati a gare shi kuma ya sanar da cewa shi yana isowa zuwa gare shi, kadai ana daure sirdi ne dan nufin masallaci da kuma sallah a cikinsa.
- Haramcin sanya ziyarar kabarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - idi, ta hanyar maimaita ziyararsa ta kebantacciyar fuska a wani zamani kebantacce, hakanan ziyar kowanne kabari.
- Girman Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga Ubangijinsa, ta hanyar shara'anta yin salati da sallama a gare shi a kowanne zamani da kuma kowanne wuri.
- Yayin da cewa hanin game da sallah a wurin kaburbura hakika ya tabbata a wurin sahabbai; saboda haka Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya hana maida gidaje tamkar makabartun da ba'a sallah a cikin su.
Madogara
سنن أبي داود (3/ 385) (2042).
الجديد في شرح كتاب التوحيد، لمحمد القرعاوي (ص202).
الملخص في شرح كتاب التوحيد، لصالح الفوزان (ص185).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ عَالَ جَارِيَتَيْنِ حَتَّى تَبْلُغَا جَاءَ يَوْمَ الْقِيَامَةِ أَنَا وَهُوَ» وَضَمَّ أَصَابِعَهُ.
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya reni 'yan mata biyu har suka balaga zai zo ranar alƙiyama ni da shi" sai ya dunƙule yatsunsa.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda aka azirta shi da 'yan mata biyu ko 'yan uwa mata biyu sai ya tsaya da ɗawainiya da tarbiyya da nusarwa ga alheri da gargaɗarwa daga sharri da makamancin hakan har suka girma suka balaga; zai zo ranar alƙiyama shi da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kamar waɗannan biyun, kuma sai ya haɗa yatsunsa biyu manuniya da na tsakiya.
Fa’idoji
- Sakamako mai girma ga wanda ya tsaya da kulawa da tarbiyyar 'yan mata har suka yi aure ko suka balaga, haka nan 'yan uwa mata.
- Ladan tsayuwa ga (tarbiyyar) 'ya'ya mata shi ne mafi girma daga ladan tsayuwa akan (tarbiyyar) 'ya'ya maza; dan ba'a ambaci hakan a haƙƙinsu ba; hakan saboda cewa ɗawainiyar 'ya'ya mata da himmatuwa da al'amuransu shi ne mafi girma daga al'amuran 'ya'ya maza; domin cewa su al'aura ne ba zai taɓa al'amuransu ba, kuma ba zasu yi tasarrufi irin tasarrufin 'ya'ya maza ba, haka nan domin uba ba ya kwaɗayin wani agaji da zasu kawo akan maƙiya, da rayar da sunansa, da sadar da nasabarsa, da makancin hakan, kamar yadda yake faruwa ga maza namiji; sai aka buƙaci haƙuri da ikhlasi a cikin hakan daga wanda yake ciyar da su tare da kyakkyawar niyya; sai ladan ya girmama, sai ya zama abokin zaman Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a ranar alƙiyama.
- Alamomin balagar mace: Cikar shekara goma sha biyar, ko ta yi al’ada kafin shekara goma sha biyar, ko kuma gashin mara ya tsiro mata shi ne gashi mai kauri a gefen gaba, ko ta yi mafarki wanda shi ne fitar maniyyi a cikin mafarki.
- Al-Kurɗubi ya ce: Yana nufi da balagarsu (wato) sukai lokacin da zasu tsayu da kansu; hakan kawai yana kasancewa ne a mata har zuwa lokacin da mazajensu zasu yi dukhuli da su, ba ya nufi da hakan isarsu zuwa lokacin da zasu yi al’ada sun balaga ba; dan zata iya yin aure kafin hakan sai ta wadatu da miji daga tsayuwar mai kulawa, kuma zata iya yin al’ada alhali ita ba ta tsayu da kanta ba da wani abu daga maslahohinta (wanda) da za'a barta da ta tozarta kuma halayenta sun ɓaci, kai ita a wannan halin ita ce mafi cancanta da tsari da kiyayewa da kuma tsayuwa akanta dan tsarinta ya cika sai a yi kwaɗayin auranta, saboda wannan ma'anar ne malumammu suka ce ciyarwa ba ta saraya daga mahaifin karamar yarinya da balgarta kai (tana saraya ne) da yin dukhulin miji da ita.
Madogara
صحيح مسلم (4/ 2027) (2631).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 352).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص198).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (5/ 144).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 105).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 276).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ عَبْدِ اللَّهِ بِن مَسْعُودٍ رضي الله عنه قَالَ: سَأَلْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: أَيُّ العَمَلِ أَحَبُّ إِلَى اللَّهِ؟ قَالَ: «الصَّلاَةُ عَلَى وَقْتِهَا»، قَالَ: ثُمَّ أَيٌّ؟ قَالَ: «ثُمَّ بِرُّ الوَالِدَيْنِ» قَالَ: ثُمَّ أَيٌّ؟ قَالَ: «الجِهَادُ فِي سَبِيلِ اللَّهِ» قَالَ: حَدَّثَنِي بِهِنَّ، وَلَوِ اسْتَزَدْتُهُ لَزَادَنِي.
Daga Abdullahi dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Wanne aiki ne mafifici a wurin Allah? ya ce: "Sallah akan lokacinta", Ya ce: Sannan wanne? Ya ce: "Sannan biyayya ga mahaifa" Ya ce: Sannan wanne? Ya ce: Yaki a tafarkin Allah" ya zantar dani su, da na nemi ya kara min da ya karamin.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
An tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Wanne aiki ne mafi soyuwa agurin Allah? Sai ya ce: Sallar farilla a lokukacinta wanda mai shari'a ya iyakance shi, sannan biyayya ga mahaifa, da kyautata musu, da tsayuwa da hakkinsu, da barin saba musu, sannan yaki a tafarkin Allah, dan daukaka kalmar Allah - Mai girma da daukaka -, da kare addinin Allah ma'abotansa, da bayyanar da alamominsa, hakan yana kasancewa ne da rai da dukiya.
Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ya bani labarin wadanan ayyukan; da na ce masa: Sannan wanne? da ya karamin.
Fa’idoji
- Fifikon ayyuka a tsakaninsu gwargwadon yadda Allah yake son su .
- Kwadaitarwar muslmi akan kwadayi akan ayyuka mafifita sai mafifita.
- Fifikon amsawar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da mafifitan ayyuka gwargwadan sabanin mutane da halayensu, da abinda yake mafi yawan amfani ga kowanne daya daga cikinsu.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 112) (527).
صحيح مسلم (1/ 90) (85).
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 70).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص84).
تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (1/ 108).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com