Daga Sahl ɗan Sa'ad al-sa'idi - Allah Ya yarda da shi - lallai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Zaman dakon yini ɗaya saboda Allah shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke kanta, kuma bigiren bulalar ɗayanku a aljanna shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke kanta, yammacin da bawa zai yi shi saboda Allah ko jijjifi shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke kanta".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa lazimtar gurin da yake tsakanin musulmai da kafirai dan gadin musulmai daga gare su a yini ɗaya yana mai tsarkake niyya saboda Allah, shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke cikinta, kuma bigiren bulalar da zai yi yaƙi da ita saboda Allah a cikin aljanna shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke cikinta, kuma lallai cewa lada da sakamakon tafiya a cikin lokaci daga farkon yini zuwa farkon lokacin azahar, ko yammaci: Daga lokacin azahar zuwa dare saboda Allah sau ɗaya, shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke cikinta.
Fa’idoji
Falalar zaman dako saboda Allah, dan abinda ke cikinsa na sadaukar da rai, dan kuma abinda yake jerantuwa a kansa na ɗaukaka kalmar Allah da taimakon AddininSa; saboda haka lallai sakamakon yini ɗaya, shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke cikinta.
Wulaƙantar duniya dangane da lahira; domin cewa gurbin bulala na aljanna shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke cikinta.
Falalar yaƙi saboda Allah, da girman ladansa; domin ladan yammaci ɗaya ko jijjifi ɗaya shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke cikinta.
Faɗinsa; "Saboda Allah" A cikinsa akwai nuni akan muhimmancin tsarkake niyya, kuma cewa lada mai jerantuwa ne a kansa.
Madogara
صحيح البخاري (4/ 35) (2892).
صحيح مسلم (3/ 1500) (1881).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص739).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com