Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Babu wasu musulmai biyu da zasu haɗu sannan su gaisa hannu da hannu sai an gafarta musu kafin su rabu

عَنِ الْبَرَاءِ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَا مِنْ مُسْلِمَيْنِ يَلْتَقِيَانِ فَيَتَصَافَحَانِ إِلَّا غُفِرَ لَهُمَا قَبْلَ أَنْ يَفْتَرِقَا».
Daga Bara'u - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce -: "Babu wasu musulmai biyu da zasu haɗu sannan su gaisa hannu da hannu sai an gafarta musu kafin su rabu".
Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne a baki dayan hanyoyin sa
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari: Cewa babu wasu musulmai biyu da zasu haɗu a wata hanya da makamancinta ɗayansu ya yi wa ɗayan sallama, gaisuwa hannu da hannu sai an gafarta musu kafin su rabu da jikkuna ko da gama gaisuwar.

Fa’idoji
  1. An so gaisawa hannu da hannu a lokacin haɗuwa, da kwaɗaitarwa akanta.
  2. AlManawi ya ce: Sunnah ba ta samuwa sai da sanya (hannun) dama a (hannun) dama inda babu wanu uzuri.
  3. kwaɗaitarwa akan yaɗa sallama, da bayanin girman ladan gaisawar musulmi hannu da hannu ga ɗan uwansa musulmi.
  4. An togance musafahar da aka haramta, kamar musafahar mace manisanciya.
Madogara

سنن أبي داود (7/ 502) (5212). سنن الترمذي (4/ 447) (2727). سنن ابن ماجه (4/ 654) (3703). مسند أحمد (30/ 517) (18547). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 152). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 680).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALOLIN AYYUKA NAGARI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com