Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Kowa ne aikin alheri sadaka ne

عن جابر بن عبد الله رضي الله عنهما عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «كُلُّ مَعْرُوفٍ صَدَقَةٌ».
Daga Jabir ɗan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Kowa ne aikin alheri sadaka ne".
Bukhari ne ya ruwaito shi daga hadisin Jabir, kuma Muslim ya ruwaito shi daga hadisin HuzaifaDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa dukkanin kyautatawa da amfani ga wasu na magana ne, ko na aiki yana zama sadaka, kuma a cikinsa akwai lada da sakamako.

Fa’idoji
  1. Lallai sadaka ba ta taƙaituwa a abin da mutum yake fitar da shi daga dukiyarsa, kai, yana tattaro kowane alherin da mutum zai aikatashi, ko ya faɗeshi ya sadar da shi zuwa wasu.
  2. A cikinsa akwai kwaɗaitarwa a kan yin aikin alheri da dukkanin abin da a cikinsa akwai amfani ga wasu.
  3. Rashin wulaƙanta wani abu daga aikin alheri ko da ya zama ƙarami ne.
Madogara

صحيح البخاري (8/ 11) (6021). صحيح مسلم (2/ 697) (1005). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (10/ 117). توضيح الأحكام من بلوغ المرام، للبسام (7/ 341).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALOLIN AYYUKA NAGARI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com