Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Ibada a cikin rashin zaman lafiya kamar hijira ce zuwa gareni

عَنْ مَعْقِلِ بْنِ يَسَارٍ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «الْعِبَادَةُ فِي الْهَرْجِ كَهِجْرَةٍ إِلَيَّ».
Daga Ma'ƙil ɗan Yasar - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ibada a cikin rashin zaman lafiya kamar hijira ce zuwa gareni".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nunar zuwa ibada da yin riƙo da ita a cikin zamanin rashin zaman lafiya da fitina da yaƙe-yaƙe da cakuɗewar al'amuran mutane, kuma cewa ladanta kamar hijira ce zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, hakan domin cewa mutane suna rafkana daga gareta, suna shagaltuwa daga gareta, babu mai ƙoƙari gareta sai ɗaiɗaiku.

Fa’idoji
  1. Kwaɗaitarwa akan ibada da fuskanta zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki - a kwanukan fitintinu; dan neman kariya daga fitintinu, da kuma kiyayewa daga ɓarna.
  2. Bayanin falalar ibada a lokutan fitintinu da lokutan rafkana.
  3. Yana kamata ga musulmi ya kaucewa guraren fitintinu da rafkana.
Madogara

صحيح مسلم (4/ 2268) (2948). كشف المشكل من حديث الصحيحين (2/ 42). البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (45/ 5). بهجة الناظرين (2/ 455). نزهة المتقين (ص942).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALOLIN AYYUKA NAGARI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com