Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Ku ji tsoron Allah ku sallaci (sallolinku) biyar, ku azimci watanku (Ramadan) ku bada zakkar dukiyoyinku, ku bi shugabanku, zaku shiga aljannar Ubangijinku

عَن أَبِي أُمَامَةَ رضي الله عنه قَالَ: سَمِعْتَ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَخْطُبُ فِي حَجَّةِ الوَدَاعِ فَقَالَ: «اتَّقُوا اللَّهَ رَبَّكُمْ، وَصَلُّوا خَمْسَكُمْ، وَصُومُوا شَهْرَكُمْ، وَأَدُّوا زَكَاةَ أَمْوَالِكُمْ، وَأَطِيعُوا ذَا أَمْرِكُمْ تَدْخُلُوا جَنَّةَ رَبِّكُمْ».
Daga Abu Umama - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana huduba a hajjin bankwana sai ya ce: "Ku ji tsoron Allah ku sallaci (sallolinku) biyar, ku azimci watanku (Ramadan) ku bada zakkar dukiyoyinku, ku bi shugabanku, zaku shiga aljannar Ubangijinku".
Tirmizi da Ahmad sun rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi huduba a ranar Arfa, a hajjin bankwana, shekara ta goma daga hijira, an ambaceta da hakan; Domin cewa shi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi wa mutane bankwana a cikinta, ya umarci mutane gaba daya da su ji tsoron Ubangijinsu ta hanyar kamanta umarninSa da nisantar haninSa. Kuma su sallaci salloli biyar din da Allah - Mai girma da daukaka - Ya wajabta musu a yini da dare. Kuma Su azimci watan azimi (Ramadan). Kuma Su bada zakkar dukiyoyi ga wadanda suka cancanta kada su yi rowarta. Su kuma bi wadanda Allah Ya sanya su shgabanni akansu inba sabon Allah ba ne, wanda ya aikata wadannan abubuwan da aka ambata to ladansa shi ne shiga aljanna.

Fa’idoji
  1. Wadannan ayyukan suna daga sabubban shiga aljanna.
Madogara

سنن الترمذي (1/ 602) (616). مسند أحمد (36/ 486) (22161). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (1/ 534). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 105).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALOLIN AYYUKA NAGARI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com