Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Da yawa mutum daƙal-daƙal abin tunkuɗewa a ƙofofi, da a ce zai yi rantsuwa ga Allah da (Allah) Ya kuɓutar da shi

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضيَ اللهُ عنهُ أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «رُبَّ أَشْعَثَ مَدْفُوعٍ بِالْأَبْوَابِ لَوْ أَقْسَمَ عَلَى اللهِ لَأَبَرَّهُ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Da yawa mutum daƙal-daƙal abin tunkuɗewa a ƙofofi, da a ce zai yi rantsuwa ga Allah da (Allah) Ya kuɓutar da shi".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa akwai daga cikin mutane wanda gashin kansa a cukurkuɗe yake, ya yi ƙura, ba ya shafa masa mai, kuma ba ya yawan wanke shi, ba shi da wata daraja a wurin mutane dan haka suke ture shi a bakin ƙofofinsu, suna korarsa dan wulaƙanta shi; saidai cewa shi da ace zai yi rantsuwa akan faruwar wani abu da Allah Ya farar da abun, dan girmama shi da amsa roƙonsa, da kuma kiyaye shi daga warware rantsuwarsa, hakan saboda falalarsa da matsayinsa a wurin Allah.

Fa’idoji
  1. Allah ba Ya duba zuwa surorin bawa saidai Yana duba zuwa zukata ne da ayyuka.
  2. Ya wajaba akan mutum ya kula da aikinsa da tsarkin zuciyarsa sama da kulawarsa ga jiinsa da tufafinsa.
  3. Kanƙar dakai ga Allah da miƙa wuya gare shi to hakan sababi ne na amsa addu'a, saboda haka; Allah - tsarki ya tabbatar maSa - Yana kuɓutar da rantsuwar masu tsoronSa ɓoyayyu.
  4. Bayanin tarbiyyar Annabi ga mutane; dan kada sashinsu su wulaƙanta sashi.
Madogara

صحيح مسلم (4/ 2024) (2622). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (5/ 48). بهجة الناظرين، لسليم الهلالي (1/ 344). نزهة المتقين، لمجموعة من الباحثين (1/ 268) شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 63).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALOLIN AYYUKA NAGARI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com