Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Mafificin dinaren (kudi) da mutum zai ciyar da shi: Dinarin da ya ciyar da shi ga iyalansa, da dinaren da mutum yake ciyar da shi ga dabbarsa a tafarkin Allah, da dinaren da yake ciyar da shi ga abokansa a tafarkin Allah

عَنْ ثَوْبَانَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَفْضَلُ دِينَارٍ يُنْفِقُهُ الرَّجُلُ، دِينَارٌ يُنْفِقُهُ عَلَى عِيَالِهِ، وَدِينَارٌ يُنْفِقُهُ الرَّجُلُ عَلَى دَابَّتِهِ فِي سَبِيلِ اللهِ، وَدِينَارٌ يُنْفِقُهُ عَلَى أَصْحَابِهِ فِي سَبِيلِ اللهِ» قَالَ أَبُو قِلَابَةَ: وَبَدَأَ بِالْعِيَالِ، ثُمَّ قَالَ أَبُو قِلَابَةَ: وَأَيُّ رَجُلٍ أَعْظَمُ أَجْرًا مِنْ رَجُلٍ يُنْفِقُ عَلَى عِيَالٍ صِغَارٍ، يُعِفُّهُمْ أَوْ يَنْفَعُهُمُ اللهُ بِهِ وَيُغْنِيهِمْ.
Daga Sauban - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mafificin dinaren (kudi) da mutum zai ciyar da shi: Dinarin da ya ciyar da shi ga iyalansa, da dinaren da mutum yake ciyar da shi ga dabbarsa a tafarkin Allah, da dinaren da yake ciyar da shi ga abokansa a tafarkin Allah" Abu Kilaba ya ce: "Sai ya fara da iyali, sannan Abu Kilaba ya ce: Kuma wanne mutum ne mafi girman lada kamar mutumin da yake ciyar da iyali ƙanana don ya rufa musu asiri ko Allah Ya anfanar da su da shi, kuma ya wadata su".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

(Annabi) tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi ya bayyana wasu Nau’uka a cikin ciyarwa, ya kuma jerantasu idan fuskokin ciyarwar sun gagara gwargwadan mafi wajabci akanka, sai ya fara da mafi muhimmanci sai mafi muhimmanci; sai ya sanar da cewa mafi yawan dukiya a lada ita ce wadda musulmi yake ciyar da ita ga wanda ciyarwarsa ta wajaba akan shi; kamar mata da ɗa, sannan ciyarwa ga abin hawa wanda aka tanada dan yaƙi a tafarkin Allah, sannan ciyarwa ga abokansa da ayarinsa a halin kasancewarsu mayaƙa a tafarkin Allah.

Fa’idoji
  1. Jeranta ciyarwa a falala ta fuskar da aka ambata, sai a lura da hakan a lokacin da suka taru.
  2. Bayanin cancantar ciyarwa ga iyali a falala akan wasunsu.
  3. Ciyarwa a yaƙi saboda Allah tana daga mafi girman ciyarwa, kamar tanadar kaya da mayaka a Jihadi.
  4. An ce: Abin nufi da tafarkin Allah dukkanin aikin ɗa'a kamar aikin hajji a misali.
Madogara

صحيح مسلم (2/ 691) (994). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (5/ 315). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 156). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 291). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 374).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALOLIN AYYUKA NAGARI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com