Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Kada ku maida gidajanku kaburbura, kuma kada ku maida kabari na idi, ku yi salati a gareni; domin cewa salatinku a gareni yana isomin a duk inda kuke

عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «لَا تَجْعَلُوا بُيُوتَكُمْ قُبُورًا، وَلَا تَجْعَلُوا قَبْرِي عِيدًا، وَصَلُّوا عَلَيَّ؛ فَإِنَّ صَلَاتَكُمْ تَبْلُغُنِي حَيْثُ كُنْتُمْ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kada ku maida gidajanku kaburbura, kuma kada ku maida kabari na idi, ku yi salati a gareni; domin cewa salatinku a gareni yana isomin a duk inda kuke".
Abu Dawud ne Ya Rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana yin hani daga wofintar da gidaje daga sallah sai su zama kamar makabartu, da ba'a sallah a cikin su. Kuma ya yi hani daga maimaita ziyarar wani kabari da taruwa a wurinsa ta fuskar al'ada; domin hakan hanya ce zuwa ga shirka, Ya yi umarni da yin salati da sallama a gare shi a kowane wuri anan doron kasa; domin cewa hakan yana isa gare shi daga na kusa da na nesa duk daya ne, babu bukatuwa zuwa kaikawo a kabarinsa.

Fa’idoji
  1. Hani daga wofintar da gidaje daga bautar Allah - Madaukakin sarki -a cikinsu.
  2. Hani daga tafiya dan ziyarar kabarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -; domin cewa shi ya yi umarni da yin salati a gare shi kuma ya sanar da cewa shi yana isowa zuwa gare shi, kadai ana daure sirdi ne dan nufin masallaci da kuma sallah a cikinsa.
  3. Haramcin sanya ziyarar kabarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - idi, ta hanyar maimaita ziyararsa ta kebantacciyar fuska a wani zamani kebantacce, hakanan ziyar kowanne kabari.
  4. Girman Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga Ubangijinsa, ta hanyar shara'anta yin salati da sallama a gare shi a kowanne zamani da kuma kowanne wuri.
  5. Yayin da cewa hanin game da sallah a wurin kaburbura hakika ya tabbata a wurin sahabbai; saboda haka Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya hana maida gidaje tamkar makabartun da ba'a sallah a cikin su.
Madogara

سنن أبي داود (3/ 385) (2042). الجديد في شرح كتاب التوحيد، لمحمد القرعاوي (ص202). الملخص في شرح كتاب التوحيد، لصالح الفوزان (ص185).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALOLIN AYYUKA NAGARI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com