Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wata rana wani mutum yana tafiya sai ya wuce wani reshen bishiya a cikinsa akwai ƙayar da take cutar da musulmai, sai ya kawar da ita daga hanyar, sai Allah Ya yaba masa kuma Ya gafarta masa.
- Falalar gusar da cuta akan hanya, kuma hakan sababi ne na (samun) gafarar Allah.
- Rashin wulaƙantar da ayyukan alheri koda sun kasance kaɗan ne.
- Musulunci addini ne na tsafta da kare yanayi da aminci na gaba daya.
صحيح البخاري (1/ 132) (652). صحيح مسلم (3/ 1521) (1914). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 156). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 175). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 207).