Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Salloli biyar, da Juma'a zuwa Juma'a, da Ramadan zuwa Ramadan, masu kankare a binda ke tsakaninsu ne idan ya nisanci manyan zunubai

عن أبي هريرة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم كان يقول: «الصَّلَوَاتُ الْخَمْسُ، وَالْجُمُعَةُ إِلَى الْجُمُعَةِ، وَرَمَضَانُ إِلَى رَمَضَانَ، مُكَفِّرَاتٌ مَا بَيْنَهُنَّ إِذَا اجْتَنَبَ الْكَبَائِرَ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce "Salloli biyar, da Juma'a zuwa Juma'a, da Ramadan zuwa Ramadan, masu kankare a binda ke tsakaninsu ne idan ya nisanci manyan zunubai".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa; Salloli biyar ababen faralantawa a yini da dare ne, da sallar Juma'a a kowane mako, da azimin watan Ramadan a kowacce shekara, masu kankare abinda ke tsakaninsu ne na kananan zunubai da sharadin nisantar manyan zunubai. Amma manyan zunubai kamar zina da shan giya ba mai kankaresu sai tuba.

Fa’idoji
  1. Zunubai daga cikinsu akwai kananu a kwai kuma manya.
  2. Kankare kananun zunubai abin shardantawane da nisantar manyan zunuban.
  3. Manyan zunubai su ne zunuban da haddi yazo a cikinsu, ko narko a lahira ya zo a cikinsu, ko fushi, ko akwai tsawatarwa a cikinsu, ko la'anta ga mai aikatasu, kamar zina da shan giya.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 209) (233). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 183). نزهة المتقين بشرح رياض الصالحين، لمصطفى سعيد الخن (1/ 158). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص108). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم بن عيد الهلالي (1/ 209).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALOLI DA LADUBBA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com