عَنْ عُمَرَ بْنِ الْخَطَّابِ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِنَّ اللهَ عَزَّ وَجَلَّ يَنْهَاكُمْ أَنْ تَحْلِفُوا بِآبَائِكُمْ»، قَالَ عُمَرُ: فَوَاللهِ مَا حَلَفْتُ بِهَا مُنْذُ سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ نَهَى عَنْهَا ذَاكِرًا وَلَا آثِرًا.
Daga Umar Dan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai Allah - mai girma da daukaka - yana hanaku ku rantse da iyayenku", Umar ya ce: Na rantse da Allah ban yi rantsuwa da su ba tunda na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana hani daga garesu da gangan ko ina mai ciratowa (daga wanina).
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Madaukakin sarki - Yana hani daga rantsuwa da iyaye, duk mai nufin yin rantsuwa kada ya rantse da kowa sai da Allah, kada ya rantse da waninsa. Sannan Umar Dan Khaddab - Allah Ya yarda da shi - ya ambaci cewa shi bai sake rantsuwa da su ba tunda ya ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana hani game da hakan, bada gangan ba, ba kuma yana mai cirato rantsuwa da wanin Allah daga waninsa ba.
Fa’idoji
- Haramcin rantsuwa da wanin Allah, an kebanci rantsuwa da iyaye; domin ita tana daga al'adun Jahiliyya.
- Rantsuwa: Ita ce rantsuwa da Allah ko da sunayen Allah ko da siffofin Allah akan wani al'amari daga al'amura dan karfafashi.
- Falalar Umar - Allah Ya yarda da shi - da gaggauta barin abinda aka hana da kyakkyawan fahimtarsa da kuma tsantseninsa.
Madogara
صحيح البخاري (8/ 132) (6647).
صحيح مسلم (3/ 1266) (1646).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص684).
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (2/ 134).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن عائشة أم المؤمنين وعبد الله بن عباس رضي الله عنهما قالا: لَمَّا نَزَلَ بِرَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ طَفِقَ يَطْرَحُ خَمِيصَةً لَهُ عَلَى وَجْهِهِ، فَإِذَا اغْتَمَّ بِهَا كَشَفَهَا عَنْ وَجْهِهِ، فَقَالَ وَهُوَ كَذَلِكَ: «لَعْنَةُ اللَّهِ عَلَى اليَهُودِ وَالنَّصَارَى، اتَّخَذُوا قُبُورَ أَنْبِيَائِهِمْ مَسَاجِدَ» يُحَذِّرُ مَا صَنَعُوا.
Daga Nana A'isha da Abdullahi Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - sun ce: Lakacin da (wafati) ya saukar wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya fara yana rufe fuskarsa da wani mayafinsa, idan ya ji ya yi masa tsanani sai ya yaye shi daga fuskarsa, sai ya ce yana hakan: "Tsinuwar Allah ta tabbata a kan Yahudawa da Nasara, sun riƙi kaburburan Annabawansu masallatai" yana gargaɗi game da abin da suka aikata.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Nana A'isha da Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - suna ba mu labarin cewa lokacin da wafati ya halartowa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya fara sanya wani yanki na riga a kan fuskarsa, idan numfashi ya wuyata a gareshi saboda magagin mutuwa, sai ya gusar da shi daga fuskarsa, sai ya faɗa a wannan halin mai tsanani: Allah Ya tsinewa Yahudawa da Nasara, ya koresu daga rahamarSa; domin su sun gina masallatai a kan kaburburan Annabawansu, da ba don haɗarin al'amarin ba da bai ambace shi a irin wannan lokacin ba, saboda haka Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya hana al'ummarsa da kamanceceniya da wannan aikin; domin yana daga aikin Yahudawa da Nasara, kuma hanya ce da za ta kai zuwa ga shirka da Allah - mai girma da ɗaukaka.
Fa’idoji
- Hani daga riƙon kaburburan Annabawa da salihai masallatan da za a dinga sallah a cikinsu; domin hakan hanya ce zuwa shirka.
- Tsananin himmatuwar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da kulawarsa a kan Tauhidi, da kuma tsoronsa daga girmama kaburbura; domin hakan yana kai wa zuwa shirka.
- Halaccin la'antar Yahudawa da Nasara, da wanda ya aikata irin aikinsu na gini a kan kaburbura da kuma rikonsu masallatai.
- Gini a kan kaburbura yana daga dabi’un Yahudawa da Nasara, a cikin Hadisin akwai hani daga kamanceceniya da su.
- Daga cikin riƙon kaburbura masallatai akwai yin sallah a wurinsu, da kuma zuwa garesu (wato kallonsu), ko da ba a gina masallaci ba.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 95) (435)، (2/ 102) (1390).
صحيح مسلم (1/ 377) (531)، (1/ 376) (529).
الملخص في شرح كتاب التوحيد، للشيخ صالح الفوزان (ص170).
الجديد في شرح كتاب التوحيد، لمحمد بن عبد العزيز السليمان القرعاوي (ص185).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «قَالَ اللهُ تَبَارَكَ وَتَعَالَى: أَنَا أَغْنَى الشُّرَكَاءِ عَنِ الشِّرْكِ، مَنْ عَمِلَ عَمَلًا أَشْرَكَ فِيهِ مَعِي غَيْرِي تَرَكْتُهُ وَشِرْكَهُ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Allah - alherinSa ya yawaita Ya girmama - Ya ce: Ni ne mafi wadatar abokanan tarayya daga shirka, duk wanda ya aikata wani aiki ya hada ni da wani a aikin to Zan bar shi da shirkarsa".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana sanar da cewa Allah - alherinSa ya yawaita Ya girmama - Ya ce: Lallai cewa Shi ne mafi wadatar abokanan tarayya game da shirka, to Shi ne Mawadaci daga dukkanin komai, kuma cewa mutum idan ya aikata wani aiki na biyayya kuma ya sanya shi ga Allah da kuma wanin Allah; to Zai bar shi ba zai karba daga gare shi ba, kuma Ya miyarwa da mai shi; To tsarkake aiki yana wajaba ga Allah - Madaukakin sarki -; domin cewa shi Allah tsarki ya tabbatar maSa ba ya karba sai abinda ya zama tsarkakakke ga zatinsa Mai girma.
Fa’idoji
- Gargadi daga shirka da dukkanin ire-irenta; kuma cewa ita tana hana karbar aiki.
- Jin wadatar Allah da Girmansa yana daga abinda yake taimakawa ga ikhlasi a cikin ayyuka.
Madogara
صحيح مسلم (4/ 2289) (2985).
شرح النووي على مسلم (18/ 115).
الملخص في شرح كتاب التوحيد، لصالح الفوزان (ص287).
الجديد في شرح كتاب التوحيد، لمحمد القرعاوي (ص325).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن جندب رضي الله عنه قال: سَمِعْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَبْلَ أَنْ يَمُوتَ بِخَمْسٍ وَهُوَ يَقُولُ «إِنِّي أَبْرَأُ إِلَى اللهِ أَنْ يَكُونَ لِي مِنْكُمْ خَلِيلٌ فَإِنَّ اللهَ تَعَالَى قَدِ اتَّخَذَنِي خَلِيلًا كَمَا اتَّخَذَ إِبْرَاهِيمَ خَلِيلًا، وَلَوْ كُنْتُ مُتَّخِذًا مِنْ أُمَّتِي خَلِيلًا لَاتَّخَذْتُ أَبَا بَكْرٍ خَلِيلًا! أَلَا وَإِنَّ مَنْ كَانَ قَبْلَكُمْ كَانُوا يَتَّخِذُونَ قُبُورَ أَنْبِيَائِهِمْ وَصَالِحِيهِمْ مَسَاجِدَ، أَلَا فَلَا تَتَّخِذُوا الْقُبُورَ مَسَاجِدَ! إِنِّي أَنْهَاكُمْ عَنْ ذَلِكَ».
Daga Jundub - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Naji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - kafin mutuwarsa da (darare) biyar alhali shi yana cewa: "Lallai ni ina barranta zuwa ga Allah da ya zama ina da badadi daga cikinku, to lallai cewa Allah - Madaukakin sarki - hakika Ya rike ni badadi, kamar yadda Ya riki (Annabi) Ibrahim badadi, da na kasance mai rikon badadi daga al'ummata da na riki Abubakar badadi, ku saurara lallai wadanda suka gabace ku sun kasance suna maida kaburburan Annabawansu da salihansu masallatai, ku saurara kada ku maida kaburbura masallatai, lallai ni ina hanaku hakan".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincinAllah su tabbata a gare shi - ya sanar game da darajarsa a wurin Allah - Madaukain sarki -, kuma cewa ita takai mafi kololuwar darajojin soyayya, kamar yadda (Annabi ) Ibrahim - amincin Allah ya tabbata a gare shi - ya sameta, saboda haka ne ya kore ya zama cewa yana da wani badadi wanin Allah; domin cewa zuciyarsa ta cika da soyayyar Allah - Madaukakin sarki - da girmama Shi da saninsa, to ba ta yalwatuwa ga wani koma bayan Allah. Da a ce yana da wani badadi daga halitta da ya zama sayyidin Abubakar - Allah Ya yarda da shi -. Sannan ya yi gargadi daga ketare iyakar da ta halatta a cikin soyayya kamar yadda Yahudawa da Nasara suka aikata a kaburburan Annabawansu da salihansu har suka maida su alloli na shirka ana bauta musu koma bayan Allah, kuma suka sanya siminti da kayan alatu a kaburburan dake masallatai da guraren ibada, kuma tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana al'ummarsa da su aikata irin aikinsu.
Fa’idoji
- Falalar Sayyidina Abubakar Siddik - Allah ya yarda da shi -, kuma cewa shi ne mafificin sahabbai kuma mafi cancantar mutane da Halifancin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bayan mutuwarsa.
- Lallai cewa gina masallatai akan kaburbura yana daga abubuwanki daga al'ummata da suka gabata.
- Hana maida kaburbura guraren ibada da za'a dinga sallah a wurinsu ko zuwa gare su, kuma ana gina masallatai ko kubbobi akansu, dan gujewa afkawa a cikin shirka saboda hakan.
- Gargadi daga zurfafawa a salihai bayi, domin hakan na kaiwa zuwa shirka.
- Hadarin abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi gargadi yayin da ya karfafa hakan kafin mutuwarsa da darare biyar.
Madogara
صحيح مسلم (1/ 377) (532).
شرح النووي على مسلم (5/ 13).
الجديد في شرح كتاب التوحيد، لمحمد القرعاوي (ص188).
الملخص في شرح كتاب التوحيد، لصالح الفوزان (ص172).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ حُذَيْفَةَ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «لَا تَقُولُوا: مَا شَاءَ اللهُ وَشَاءَ فُلَانٌ، وَلَكِنْ قُولُوا: مَا شَاءَ اللهُ ثُمَّ شَاءَ فُلَانٌ».
Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ku ce : Allah Ya so wane ma ya so, saidai ku ce: Allah ne Ya so, sannan wane ma ya so".
Abu Dawud da Nasa'i cikin alkubra haka Ahmad suka ruwaito shiDarajaIngantacce ne a baki dayan hanyoyin sa
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana musulmi ya ce a zancensa: Allah Ya so wane ma ya so", ko Allah Ya so da wane; hakan domin ganin damar Allah da nufinSa a wawaice suke, wani ba ya tarayya daShi a cikinsu, a cikin amfani da Waw (da) a adafi alamtarwa ne na hada wani tare da Allah da daidaitawa a tsakaninsu. Saidai ya ce: Allah ne Ya so, sannan wane ma ya so, Sai ya sanya ganin damar bawa mai bi ce ga ganin damar Allah ta hanyar fadin: "Sannan" canjin "da"; domin "sannan" tana fa'idantar da bibiya da kuma jinkiri.
Fa’idoji
- Haramcin fadin: "Allah Ya so kaima ka so" da makamancin hakan daga lafazukan da acikinsu akwai adafi ga Allah da Waw; domin cewa shi yana daga Shirka ta lafazi da maganganu.
- Halaccin fadin: "Allah ne Ya so sannan ka so", da abinda ke kama da hakan daga abinda a cikinsa akwai adafi ga Allah da Summa (sannan); dan koruwar abinda ake gudu a cikinsa.
- Tabbatar da ganin damar Allah, da kuma ganin damar bawa, kuma cewa Mashi'ar bawa mai bi ce ga Mashi'ar Allah - Madaukakin sarki -.
- Hani daga tarayya da halitta a cikin Mashi'ar Allah koda da lafazi ne.
- Idan mai fada ya kudirce cewa Mashi'ar bawa kamar Mashi'ar Allah ce - Mai girma da daukaka - daidai da ita a gamewa da wawaita, ko cewa bawa yana da Mashi'a tsayayya to wannan babbar shirka ce, amma idan ya kudire cewa shi koma bayansa ne; to shirka ce karama.
Madogara
السنن الكبرى للنسائي (9/ 361) (10755).
سنن أبي داود (7/ 334) (4980).
مسند أحمد (38/ 299) (23265)، (38/ 364) (23339).
الجديد في شرح كتاب التوحيد، لمحمد القرعاوي (ص368).
الملخص في شرح كتاب التوحيد، لصالح الفوزان (ص329).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن عبد الله بن مسعود رضي الله عنه قال: "لأن أحلف بالله كاذبًا أحب إليَّ من أن أحلف بغيره صادقًا".
Daga Abdullahi Dan Mas'ud -Allah yarda da shi ya ce: "a rantse da Allah ina mai karya shi ne mafi soyuwa a gareni da na rantse da waninsa
Ibnu Abi Hatim ya rawaito shi - Abdurrazak Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Dan Mas'ud yana cewa Rantsuwa ta da Allah alhalin ina Mai karya cikin hakan asama hakan zai faru to hakan yafi mun soyuwa a gareni da in rantse da wanin Allah akan wani Abu kuma ina da gaskiya a kansa, kuma cewa ya rinjayar da rantsuwa da Allah yana mai karya kan rantsuwa da waninsa yana mai gaskiya; Domin Rantsuwa da Allah cikin hakan akwai a cikinsa wani yanayin aikin lada na kadaita Allah, kuma da laifin Karya a cikinsa, kuma Rantsuwa da waninsa yana mai gaskiya a cikinsa akwai ladan gaskiya kuma da laifin Shirka, kuma ladan kadaita Allah yafi girma kan ladan gaskiy, kuma laifin karya yafi sauki akan laifin shirka
Madogara
كتاب التوحيد للإمام محمد بن عبد الوهاب ص252 ت: د. دغش العجمي . مكتبة أهل الأثر , الطبعة الخامسة , 1435ه
الجديد في شرح كتاب التوحيد لمحمد بن عبد العزيز السليمان القرعاوي, ت: محمد بن أحمد سيد , مكتبة السوادي، الطبعة: الخامسة، 1424ه
الملخص في شرح كتاب التوحيد للشيخ صالح الفوزان , دار العاصمة , الطبعة الأولى 1422ه
المصنف لابن أبي شيبة, ت: كمال يوسف الحوت, مكتبة الرشد, الطبعة: الأولى، 1409
إرواء الغليل للألباني , المكتب الإسلامي , ط2, 1405ه
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَن عُمَرَ بنِ الخَطَّابِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قال: سَمِعْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «لَا تُطْرُونِي كَمَا أَطْرَتِ النَّصَارَى ابْنَ مَرْيَمَ؛ فَإِنَّمَا أَنَا عَبْدُهُ، فَقُولُوا: عَبْدُ اللهِ وَرَسُولُهُ».
Daga Umar Ibnu Khaddab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Naji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Kada ku wuce gona da iri wajen yabona, yadda Nasara suka maida Dan Maryam, ni kawai bawa ne, to ku ce: Bawan Allah kuma ManzonSa".
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana hani daga wuce gona da iri da kuma ketare iyakar shari'a a yabonsa da kuma siffanta shi da siffofin Allah - Madaukakin sarki - da kuma ayyukansa wadanda suka kebanta da shi, ko cewa shi yana sanin gaibu, ko a kira shi tare da Allah, kamar yadda Nasara suka aikata tare da Isa Dan Maryam - amincin Allah ya tabbata a gare shi -. Sannan ya bayyana cewa shi bawa ne daga bayin Allah, ya kuma yi umarni da mu fada game da shi: Bawan Allah kuma ManzonSa.
Fa’idoji
- Gargadarwa daga ketare iyakar shari'a a girmamawa da yabo; domin cewa hakan yana kaiwa zuwa ga shirka.
- Abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi gargadi akan sa ya afku a cikin wannan al'ummar, sai wasu mutane suka wuce gona da iri a Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, wasu mutanen kuma a iyalan gidansa, wasu mutanen kuma a waliyyai, sai suka fada a cikin shirka.
- Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya siffanta kansa da cewa shi bawan Allah ne; dan ya bayyana cewa shi bawa ne wanda yake bauta ga Allah, ba ya halatta a juyar masa da wani abu daga abinda Ubangiji Ya kebanta da shi.
- Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya siffanta kansa da cewa shi Manzon Allah ne abin aikowa daga wurin Allah to gasgata shi da binsa ya wajaba.
Madogara
صحيح البخاري (4/ 167) (3445).
عمدة القاري شرح صحيح البخاري، محمود بن أحمد بدر الدين العيني (16/ 37).
فتح الباري، لابن حجر (6/ 490).
منار القاري شرح مختصر صحيح البخاري، حمزة محمد قاسم (4/ 208).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه أَنَّهُ قَالَ: قِيلَ: يَا رَسُولَ اللهِ، مَنْ أَسْعَدُ النَّاسِ بِشَفَاعَتِكَ يَوْمَ الْقِيَامَةِ؟ قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَقَدْ ظَنَنْتُ يَا أَبَا هُرَيْرَةَ أَنْ لَا يَسْأَلَنِي عَنْ هَذَا الْحَدِيثِ أَحَدٌ أَوَّلُ مِنْكَ؛ لِمَا رَأَيْتُ مِنْ حِرْصِكَ عَلَى الْحَدِيثِ، أَسْعَدُ النَّاسِ بِشَفَاعَتِي يَوْمَ الْقِيَامَةِ، مَنْ قَالَ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ خَالِصًا مِنْ قَلْبِهِ أَوْ نَفْسِهِ»».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Aka ce ya Manzon Allah waye mafi azirtar mutane da cetanka a ranar Kiyama? Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Hakika ya Abu Huraira na yi zatan babu daya da zai tambayeni game da wannan hadisin na farko daga kai, saboda abinda na gani na kwadayinka akan hadisi, mafi arzikin mutane da cetona a ranar Kiyama, wanda ya ce babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, yana mai tsarkakewa daga zuciyarsa ko ransa".
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana sanar da cewa mafi azirtar mutane da cetansa a ranar alkiyama shi ne wanda ya ce: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, yana mai tsarkakewa daga zuciyarsa". Wato babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ya zama kubutacce daga shirka da riya.
Fa’idoji
- Tabbatar da ceto ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a lahira, kuma cewa shi ceton ba ya kasancewa sai ga masu Tauhidi.
- Cetonsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - shi ne tawassalinsa zuwa ga Allah - Madaukakin sarki - ga wanda ya cancanci shiga wuta daga masu Tauhidi cewa ba zai shigeta ba, wanda kuma ya shiga wutar da cewa zai fita daga cikinta muddin yana da Tauhidi.
- Falalar kalmar Tauhidi tsarkakkiyya ga Allah - Madaukakin sarki - da kuma girman tasirinta.
- Tabbatar da kalmar Tauhidi yana kasancewa ne da sanin ma'anarta, da kuma aiki da abinda taka kunsa.
- Falalar Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - da kuma kwadayinsa akan ilimi.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 31) (99).
منار القاري شرح مختصر صحيح البخاري، لحمزة محمد قاسم (1/ 197).
القول المفيد على كتاب التوحيد، لابن عثيمين (1/ 343).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com