Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Wanda ya rataya laya to haƙiƙa ya yi shirka

عَنْ عُقْبَةَ بْنِ عَامِرٍ الْجُهَنِيِّ رضي الله عنه: أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَقْبَلَ إِلَيْهِ رَهْطٌ، فَبَايَعَ تِسْعَةً وَأَمْسَكَ عَنْ وَاحِدٍ، فَقَالُوا: يَا رَسُولَ اللهِ، بَايَعْتَ تِسْعَةً وَتَرَكْتَ هَذَا؟ قَالَ: «إِنَّ عَلَيْهِ تَمِيمَةً»، فَأَدْخَلَ يَدَهُ فَقَطَعَهَا، فَبَايَعَهُ، وَقَالَ: «مَنْ عَلَّقَ تَمِيمَةً فَقَدْ أَشْرَكَ».
Daga Uƙuba ɗan Amir Aljuhani - Allah Ya yarda da shi -: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - wasu mutane sun fuskanto gare shi , sai ya yi wa tara daga cikinsu caffa (Mubaya’a) yaki yi wa ɗaya, sai suka ce: Ya Manzon Allah, ka yi wa tara caffa ka bar wannan? ya ce: "Atare da shi akwai laya". Sai ya shigar da hannunsa sai ya yanketa, sai ya yi masa caffa, ya ce: "Wanda ya rataya laya to haƙiƙa ya yi shirka".
Ahmad ne ya rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi

Wasu jama'a sun zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, adadinsu su goma ne, sai ya yi Mubaya’awa tara daga cikinsu (Wato caffa) akan Musulunci da bi, bai yi wa na goman ba, yayin da aka tambaye shi game da sababin hakan sai tsira da amincin su tabbata agare shi ya ce: Lallai atare da shi akwai laya, ita ce abinda ake ɗaurawa ko ake ratayawa na laya (guru ko kamun) ko waninsa don tunkuɗe kanbun baka ko wata cuta. Sai mutumin ya shigar da hannunsa gurin layar ya yanketa ya kuɓuta daga gareta, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi masa caffa, ya ce yana mai gargaɗarwa daga layu yana mai bayyana hukuncinsu: "Wanda ya rataya laya to haƙiƙa ya yi shirka".

Fa’idoji
  1. Wanda ya dogara ga wanin Allah, Allah Zai yi masa mu'amala da saɓanin nufinsa.
  2. Kudirce cewa rataya layu sababi ne na tunkuɗe cuta da kanbun baka to ƙaramar shirka ce, amma idan ya ƙudirce cewa suna amfanarwa da kansu to hakan babbar shirka ce.
Madogara

مسند أحمد (28/ 636) (17422). الملخص في شرح كتاب التوحيد، لصالح الفوزان (ص74). الجديد في شرح كتاب التوحيد، لمحمد القرعاوي (ص85).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
Kaɗaita Allah cikin bauta

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com