Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Kada a bar wuyan wani raƙumi da wani abin wuya na tsirkiya, ko wani abin wuya dai sai an yanke shi

عن أبي بَشير الأنصاري رضي الله عنه: أَنَّهُ كَانَ مَعَ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي بَعْضِ أَسْفَارِهِ، قَالَ: فَأَرْسَلَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ رَسُولًا -وَالنَّاسُ فِي مَبِيتِهِمْ-: «لَا يَبْقَيَنَّ فِي رَقَبَةِ بَعِيرٍ قِلَادَةٌ مِنْ وَتَرٍ أَوْ قِلَادَةٌ إِلَّا قُطِعَتْ».
Daga Abu Bashir mutumin Madina, Allah Ya yarda da shi: Cewa ya kasance tare da Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a wasu tafiye- tafiyansa, ya ce: Sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya aika a lokacin munane suna wurin baccinsu Kada a bar wuyan wani raƙumi da wani abin wuya na tsirkiya, ko wani abin wuya dai sai an yanke shi.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance a wata tafiyarsa a lokacin mutane suna wurin baccin su inda suke bacci a bukkokinsu da shemominsu. Sai ya aika wani mutum don ya sami mutane ya umarcesu da yanke kowanne abu da aka rataya a wuyan raƙumi, shin na tsirkiya ne, ko wani abu kamar ƙararrawa ko takalmi, domin sun kasance suna yi musu rataye saboda tsoron kambun baka, sai aka umarce su da su yanke, domin babu abin da take karawa, kuma anfanarwa da cutarwa suna hannun Allah ne Shi kadai.

Fa’idoji
  1. Haramcin rataya tsirkiya da abin wuya domin janyo amfani ko kuma tunkuɗe cuta domin haka nau'i ne na shirka.
  2. Sanya abin wuya wanda ba tsarkiya ba, idan ya kasance domin ado ne ko jan dabba ko ɗaureta, to, wannan babu komai.
  3. Wajibcin hana ɓarna gwargwadon iko
  4. Wajibcin ɗamfaruwar zuciya da Allah shi kaɗai babu abokin tarayya da shi.
Madogara

صحيح البخاري (4/ 59) (3005). صحيح مسلم (3/ 1672) (2115). القول المفيد على كتاب التوحيد، لابن عثيمين (1/ 179). الملخص في شرح كتاب التوحيد، لصالح الفوزان (ص77). الجديد في شرح كتاب التوحيد، لمحمد القرعاوي (ص89).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
Kaɗaita Allah cikin bauta

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com