Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Allah Ya tsinewa Yahudawa da Nasara, sun riƙi ƙaburburan Annabwansu (a matsayin) masallatai

عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المؤْمنينَ رَضيَ اللهُ عنها قَالَتْ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي مَرَضِهِ الَّذِي لَمْ يَقُمْ مِنْهُ: «لَعَنَ اللهُ الْيَهُودَ وَالنَّصَارَى، اتَّخَذُوا قُبُورَ أَنْبِيَائِهِمْ مَسَاجِدَ» قَالَتْ: فَلَوْلَا ذَاكَ أُبْرِزَ قَبْرُهُ، غَيْرَ أَنَّهُ خُشِيَ أَنْ يُتَّخَذَ مَسْجِدًا.
Daga Nana A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗa a cikin rashin lafiyarsa wacce bai tashi daga gareta ba: «Allah Ya tsinewa Yahudawa da Nasara, sun riƙi ƙaburburan Annabwansu (a matsayin) masallatai» ta ce; Da badan haka ba da an bayyanar da ƙabarinsa, sai dai cewa an ji tsoron a riƙe shi a matsayin masallaci.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Nana A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗa a cikin rashin lafiyarsa wacce ta tsananta gare shi kuma ya mutu a cikinta: Allah Ya tsinewa Yahudawa da Nasara, Ya koresu daga rahamarSa; hakan domin cewa su sun riƙi ƙaburburan Annabawansu a matsayin masallatai. Ta hanyar yin gini a kansu ko yin sallah a wurinsu ko zuwa garesu (kallonsu). (Nana A'isha) Allah Ya yarda da ita ta ce: Da badan wannan hanin da gargaɗin daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da tsoron sahabbai kan abinda za’a yi wa ƙabarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kamar yadda Yahudawa da Nasara suka yi wa ƙaburburan Annabwansu ba da anbayyanar da ƙabarinsa kuma an fito da shi.

Fa’idoji
  1. Wannan yana daga wasiyyoyinsa na ƙarshe daga abinda yake nuni akan muhimmancinsu da kuma kulawa da su.
  2. Hani mai ƙarfi, da haramci mai tsanani daga riƙon ƙaburbura masallatai, da nufar yin sallah a wurinsu banda sallar jana'iza; to hakan hanya ce zuwa girmama mamacin da kuma ɗawafi a ƙabarinsa da shafa ƙinshiƙansa da kiran sunansa, kuma dukkanin wannan yana daga shirka da kuma hanyoyinta.
  3. Tsananin himmatuwar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da kulawarsa a kan Tauhidi, da kuma tsoronsa daga girmama ƙaburbura; domin hakan yana kai wa zuwa ga shirka.
  4. Allah - Maɗaukakin sarki - Ya kiyaye Annabinsa - tsira da amincin su tabbata agare shi - da ayi shirka a wurin ƙabarinsa, sai ya cusawa sahabbansa da waɗanda ke bayansu su kiyaye ƙabarinsa da kada a fito da shi.
  5. Aikin sahabbai - Allah Ya yarda da su - da wasiyyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kuma kwaɗayinsu akan Tauhidi.
  6. Hani daga kamanceceniya da Yahudawa da Nasara, da kuma gini akan ƙaburbura yana daga al'adunsu.
  7. Daga cikin riƙon kaburbura masallatai akwai yin sallah a wurinsu, da kuma zuwa garesu (wato kallonsu), ko da ba a gina masallaci ba.
Madogara

صحيح البخاري (2/ 102) (1390). صحيح مسلم (1/ 376) (529). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص292). تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (2/ 376). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 236).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
Kaɗaita Allah cikin bauta

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com