Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Shin ba na aika ka ba a kan abin da Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya aike ni ba?? Kada ka bar mutum-mutumi sai ka share shi, haka kabari da aka ɗaga shi sai ka daidaita shi (da sauran kaburbura)

عن أبي الهيَّاج الأسدي قال: قَالَ لِي ‌عَلِيُّ بْنُ أَبِي طَالِبٍ: أَلَا أَبْعَثُكَ عَلَى مَا بَعَثَنِي عَلَيْهِ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ؟ أَنْ لَا تَدَعَ تِمْثَالًا إِلَّا طَمَسْتَهُ، وَلَا قَبْرًا مُشْرِفًا إِلَّا سَوَّيْتَهُ.
Daga Abu Hayyaj Al’asadi, ya ce: Aliyu Ɗan Abi Talib, ya ce da ni: Shin ba na aika ka ba a kan abin da Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya aike ni ba?? Kada ka bar mutum-mutumi sai ka share shi, haka kabari da aka ɗaga shi sai ka daidaita shi (da sauran kaburbura).
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana aika sahabbansa a kan kada su bar ((mutum-mutumi)) na wani abu da yake da rai aka gina shi ko ba gina shi aka yi ba, sai sun kawar da shi, sun shafe shi. Kuma kada su bar kabari wanda aka ɗaga shi sai sun daidaita shi da ƙasa, sun rushe ginin da aka yi, ko sun sanya shi a shafe kada ya daga a bayan kasa ɗagawa mai yawa, kawai ya ɗaga kamar ɗani guda.

Fa’idoji
  1. Haramcin suranta abubuwa masu rai, domin suna cikin hanyoyin shirka.
  2. Shar’antuwar gusar da mummunan abu da hannu ga wanda yake da doka ko iko a kan haka.
  3. Kwaɗayin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, a kan gusar da duk wasu alamomi na maguzanci na hotuna da mutum mutumi da gine gine a kan kaburbura.
Madogara

صحيح مسلم (2/ 666) (969). القول المفيد على كتاب التوحيد، لابن عثيمين (2/ 446). الملخص في شرح كتاب التوحيد، لصالح الفوزان (ص402). الجديد في شرح كتاب التوحيد، لمحمد القرعاوي (ص447). كتاب التوحيد، للإمام محمد بن عبد الوهاب (ص138).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
Kaɗaita Allah cikin bauta

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com