Annabi - tsira da amincinAllah su tabbata a gare shi - ya sanar game da darajarsa a wurin Allah - Madaukain sarki -, kuma cewa ita takai mafi kololuwar darajojin soyayya, kamar yadda (Annabi ) Ibrahim - amincin Allah ya tabbata a gare shi - ya sameta, saboda haka ne ya kore ya zama cewa yana da wani badadi wanin Allah; domin cewa zuciyarsa ta cika da soyayyar Allah - Madaukakin sarki - da girmama Shi da saninsa, to ba ta yalwatuwa ga wani koma bayan Allah. Da a ce yana da wani badadi daga halitta da ya zama sayyidin Abubakar - Allah Ya yarda da shi -. Sannan ya yi gargadi daga ketare iyakar da ta halatta a cikin soyayya kamar yadda Yahudawa da Nasara suka aikata a kaburburan Annabawansu da salihansu har suka maida su alloli na shirka ana bauta musu koma bayan Allah, kuma suka sanya siminti da kayan alatu a kaburburan dake masallatai da guraren ibada, kuma tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana al'ummarsa da su aikata irin aikinsu.
- Falalar Sayyidina Abubakar Siddik - Allah ya yarda da shi -, kuma cewa shi ne mafificin sahabbai kuma mafi cancantar mutane da Halifancin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bayan mutuwarsa.
- Lallai cewa gina masallatai akan kaburbura yana daga abubuwanki daga al'ummata da suka gabata.
- Hana maida kaburbura guraren ibada da za'a dinga sallah a wurinsu ko zuwa gare su, kuma ana gina masallatai ko kubbobi akansu, dan gujewa afkawa a cikin shirka saboda hakan.
- Gargadi daga zurfafawa a salihai bayi, domin hakan na kaiwa zuwa shirka.
- Hadarin abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi gargadi yayin da ya karfafa hakan kafin mutuwarsa da darare biyar.
صحيح مسلم (1/ 377) (532). شرح النووي على مسلم (5/ 13). الجديد في شرح كتاب التوحيد، لمحمد القرعاوي (ص188). الملخص في شرح كتاب التوحيد، لصالح الفوزان (ص172).