Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Allah - Maɗaukakin sarki - Zai cewa mafi ƙanƙantar 'yan wuta azaba a ranar lahira: Shin da ace duk abinda ke cikin ƙasa naka ne shin zaka fanshi kanka da shi? Sai ya ce: Eh

عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «يَقُولُ اللَّهُ تَعَالَى لِأَهْوَنِ أَهْلِ النَّارِ عَذَابًا يَوْمَ القِيَامَةِ: لَوْ أَنَّ لَكَ مَا فِي الأَرْضِ مِنْ شَيْءٍ أَكُنْتَ تَفْتَدِي بِهِ؟ فَيَقُولُ: نَعَمْ، فَيَقُولُ: أَرَدْتُ مِنْكَ أَهْوَنَ مِنْ هَذَا، وَأَنْتَ فِي صُلْبِ آدَمَ: أَلّاَ تُشْرِكَ بِي شَيْئًا، فَأَبَيْتَ إِلَّا أَنْ تُشْرِكَ بِي».
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Allah - Maɗaukakin sarki - Zai cewa mafi ƙanƙantar 'yan wuta azaba a ranar lahira: Shin da ace duk abinda ke cikin ƙasa naka ne shin zaka fanshi kanka da shi? Sai ya ce: Eh, Sai ya ce: Na so ƙasa da hakan daga gareka alhali kai kana cikin tsatson (annabi) Adam: Kada ka ka yi min tarayya da wani abu, sai kaƙi sai dai ka yi shirka daNi".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Zai cewa mafi ƙanƙantar 'yan wuta a zaba bayan shigarta: Da ace duniya da abinda ke cikinta nakane shin zaka fanshi kanka da ita daga wannan azabar? Sai ya ce: Eh, Sai Allah Ya ce: Haƙiƙa Na nema daga gareka kuma Na umarceka da mafi sauƙi daga hakan lokacin da aka karɓi alƙawari gareka alhali kai kana cikin tsatson (annabi) Adam da kada ka yi shirka daNi da wani abu; sai kaƙi lokacin da Na fitar da kai zuwa duniya sai dai shirka.

Fa’idoji
  1. Falalar Tauhidi da sauƙin aiki da shi.
  2. Haɗarin shirka da Allah - Maɗaukakin sarki - da ƙarshenta.
  3. Allah Ya riƙi alƙawari ga 'ya'yan Adam a bayan babansu Adam da rashin yin shirka.
  4. GargaɗI akan shirka kuma cewa duniya gabaɗayanta ba zata wadatar da kafiri da komai ba a ranar lahira.
Madogara

صحيح البخاري (8/ 115) (6557). صحيح مسلم (4/ 2160) (2805). عمدة القاري شرح صحيح البخاري، لبدر الدين العيني (15/ 213). معجم اللغة العربية المعاصرة، لأحمد مختار(2/ 1311). معارج القبول بشرح سلم الوصول إلى علم الأصول، لحافظ الحكمي (1/ 96).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
Kaɗaita Allah cikin bauta

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com