Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Babu ciratar cuta kuma babu camfi, fatan alkairi yana birgeni" ya ce: A ka ce : Menene fatan alkairi? sai ya ce: "Magana mai dadi

عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «لَا عَدْوَى، وَلَا طِيَرَةَ، وَيُعْجِبُنِي الْفَأْلُ» قَالَ قِيلَ: وَمَا الْفَأْلُ؟ قَالَ: «الْكَلِمَةُ الطَّيِّبَةُ».
Daga Anas Ɗan Malik Allah Ya yarda da shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Babu ciratar cuta kuma babu camfi, fatan alkairi yana birgeni" ya ce: A ka ce : Menene fatan alkairi? sai ya ce: "Magana mai dadi".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah agare shi - yana bada labarin cewa ciratar cutar da mutanen Jahiliyya suke ƙudircewa da cewa cuta tana cirata da kanta zuwa wani ba tare da ikon Allah ba da cewa batacce ne, (ba haka ba ne). kuma camfi batacce ne, shi ne camfi na kowanne abu, abin ji ne ko abin gani, na tsuntsaye ne ko dabbobi ko masu tawaya ko lambobi ko ranaku ko wanin hakan, kadai ya ambaci canfi ne domin cewa shi ne ya fi shahara a lokacin Jahiliyya, asalinsa shi ne sakin tsuntsu a lokacin fara wani aiki na tafiya ne ko kasuwanci ko makamancin hakan, idan ya tashi ta bangaren dama sai ya yi yunkuri ya ci gaba da abinda yake nufi, idan ya tashi bangaren hagu sai ya camfa ya ki yin abinda yake nufi. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bada labarin cewa shi fata na gari yana ƙayatar da shi, shi ne abinda yake faruwa ga mutum na farin ciki da nishadi na wata magana mai dadi da zai ji ta, ta kuma sanya shi ya dinga kyautata zato ga Ubangijinsa.

Fa’idoji
  1. Dogaro ga Allah - Madaukakin sarki -, kuma ba mai zuwa da alheri sai Allah, kuma ba mai tunkude sharri sai Allah.
  2. Hani daga camfi, shi ne abinda mutum yake camfa shi, kuma yake hana aiki.
  3. Fata na gari ba shi daga cikin camfin da aka hana, kawai shi yana daga yi wa Allah - Madaukakin sarki - kyakkyawan zato ne,
  4. Kowanne abu yana faruwa ne da ikon Allah - Mai girma da daukaka - Shi kadai baShi da abokin tarayya.
Madogara

صحيح البخاري (7/ 135) (5756). صحيح مسلم (4/ 1746) (2224). فتح المجيد شرح كتاب التوحيد، لعبد الرحمن التميمي (ص310). القول المفيد على كتاب التوحيد، لابن عثيمين (1/ 570). الملخص في شرح كتاب التوحيد، لصالح الفوزان (ص230). الجديد في شرح كتاب التوحيد، لمحمد القرعاوي (ص255). التمهيد لشرح كتاب التوحيد، لصالح آل الشيخ (ص333).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
Kaɗaita Allah cikin bauta

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com