Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Ya kai Ruwaifia,watakila rayuwarka tayi tsawo, saboda haka bawa Mutane labarin cewa duk wanda ya daure gemunsa, ko ya daura tsirkiya, ko yayi tsarki turoson dabbobi ko kashi, to babu shi babu Annabi Muhammad

عن رويفع قال: قال لي رسول الله صلى الله عليه وسلم : "يا رُوَيْفِعُ، لعل الحياة ستطول بك فأخبر الناس أن من عَقَدَ لِحْيَتَهُ، أو تَقَلَّدَ وَتَرًا، أو اسْتَنْجَى برَجِيعِ دابة أو عَظْمٍ، فإن محمدًا بريءٌ منه".
Daga Ruwaifi'a ya ce: Manzon Allah ya ce da ni: "Ya kai Ruwaifia,watakila rayuwarka tayi tsawo, saboda haka bawa Mutane labarin cewa duk wanda ya daure gemunsa, ko ya daura tsirkiya, ko yayi tsarki turoson dabbobi ko kashi, to babu shi babu Annabi Muhammad
Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Manzon Allah SAW- yana cewa wannan sahabin zai yi tsawon rai har sai ya fahimci mutanen da suka saba wa koyarwarsa - SAW- a cikin gemun da ke samar da shi da kuma girmama shi zuwa wasa da ita , ta Hanyar da zasu rika kamanceceniya da Baubaye ko ma'abota wasa ko Ma'abota kece raini da Dukiya da kuma karairaya kuma suna keta akidar tauhidi ta hanyar amfani da hanyoyin shirka, kuma suna sanya abun wuya ko suna sanyawa Dabbobinsui, kuma suna neman amfani da haramtattun abubuwa. Ko kuma su aikata abin da annabinsu ya hana su na yin tsarki da kashin Dabbobi. Annabi -SAW- ya yi Wasiyya ga sahabinsa da su isar ga Alumma cewa annabin nata ba ruwansa da wadanda yayi wani abu daga hakan.

Madogara

الملخص في شرح كتاب التوحيد، دار العاصمة الرياض، الطبعة: الأولى 1422هـ. الجديد في شرح كتاب التوحيد، مكتبة السوادي، جدة، المملكة العربية السعودية، الطبعة: الخامسة، 1424هـ/ 2003م. سنن أبي داود، تحقيق: محمد محيي الدين عبد الحميد، نشر: المكتبة العصرية، صيدا – بيروت. السنن الصغرى للنسائي "المجتبى"، تحقيق: عبد الفتاح أبو غدة، نشر: مكتب المطبوعات الإسلامية – حلب، الطبعة: الثانية، 1406هـ – 1986م. مسند الإمام أحمد بن حنبل، تحقيق: شعيب الأرنؤوط - عادل مرشد، وآخرون، نشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة: الأولى، 1421هـ - 2001م. صحيح أبي داود - الأم، للألباني، نشر: مؤسسة غراس للنشر والتوزيع، الكويت، الطبعة: الأولى، 1423هـ - 2002 م.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
Kaɗaita Allah cikin bauta

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com