Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Kada ku yi rantsuwa da ɗagutai, ko da iyayenku

عَنْ عَبْدِ الرَّحْمَنِ بْنِ سَمُرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَا تَحْلِفُوا بِالطَّوَاغِي، وَلَا بِآبَائِكُمْ».
Daga Abdurrahman ɗan Samura - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kada ku yi rantsuwa da ɗagutai, ko da iyayenku".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana hani daga rantsuwa da ɗawagitai, jam'ine na dagutu, sune gumakan da mushrikai suke bauta musu koma bayan Allah, sune sababin shisshiginsu da kafircinsu, kuma tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana yin hani daga rantsuwa da iyaye; inda ya kasance daga al'adar larabawa a Jahiliyya shi ne su yi rantsuwa da iyayensu dan alfahari da girmamawa.

Fa’idoji
  1. Rantsuwa bata halatta sai da Allah da sunayenSa da siffofinSa.
  2. Haramcin rantsuwa da ɗawagitai, da kuma iyaye da shugabanni da gumaka, da abinda ke kama da su daga dukkan ƙarya.
  3. Rantsuwa da wanin Allah yana daga ƙaramar shirka, takan iya zama shirka babba, idan akwai girmama wanda aka yi rantsuwa da shi a cikin zuciya, kuma shi yana girma shi kamar yadda yake girmama Allah, ko cewa shi yana ƙudirce wani abu a cikinsa na bauta.
Madogara

صحيح مسلم. نزهة المتقين، مجموعة من الباحثين (2/ 1166). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (6/ 451). سبل السلام، لمحمد الصنعاني (2/ 545). المنهاج شرح صحيح مسلم، للنووي (11/ 108).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
Kaɗaita Allah cikin bauta

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com