Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Duk wanda ya gamu da Allah ba ya hada wani abu da shi to kuskurensa ba zai cutur da shi tare da shi ba, wanda kuwa ya mutu alhali yana yin shirka da shi wani kyakkyawan aikinsa ba zai amfane shi tare da shi da komai ba

عَنْ عَبْدَ اللهِ بْنِ عَمْرٍو رَضيَ اللهُ عَنْهُمَا يَقُولُ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ لَقِيَ اللهَ لَا يُشْرِكُ بِهِ شَيْئًا لَمْ تَضُرَّهُ مَعَهُ خَطِيئَةٌ، وَمَنْ مَاتَ وَهُوَ يُشْرِكُ بِهِ لَمْ يَنْفَعْهُ مَعَهُ حَسَنَةٌ».
Daga Abdullahi Ibnu Amr Ibnul Aas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Duk wanda ya gamu da Allah ba ya hada wani abu da shi to kuskurensa ba zai cutur da shi tare da shi ba, wanda kuwa ya mutu alhali yana yin shirka da shi wani kyakkyawan aikinsa ba zai amfane shi tare da shi da komai ba"
Ahmad ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya mutu kuma ya gamu da Allah yana mai kaɗaita Allah ba ya hada wani da abu da shi to shi yana daga cikin 'yan aljanna, ko da an yi masa uƙuba da zunubinsa a cikin wuta. Wanda ya mutu alhali yana hada wani abu da shi to wani kyakkyawan aiki ba zai yi amfani tare da shirkarsa ba; kuma aljanna haramun ce gare shi .

Fa’idoji
  1. Gargaɗarwa daga shirka, kuma cewa ita ce mafi girman zunubai da kurakurai, kuma cewa Allah baYa gafarta ta.
  2. Falalar tauhidi, kuma shi Tauhidi yana wajabta shiga aljanna; ko da bayan an yi azaba ne.
  3. Muhimmancin tabbata akan tauhidi har zuwa mutuwa, da kuma rashin aikata kishiyarsa na shirka.
Madogara

مسند أحمد (11/ 155- 156) (11/ 157) (6586). فيض القدير شرح الجامع الصغير (6/220).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
Kaɗaita Allah cikin bauta

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com