Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Wanda ya mutu alhali shi yana kiran kishiya wanin Allah zai shiga wuta

عَنْ عَبْدِ اللهِ بنِ مَسْعُودٍ رضي الله عنه قال: قَالَ النَّبِيُّ صلى الله عليه وسلم كَلِمَةً وَقُلْتُ أُخْرَى، قَالَ النَّبِيُّ صلى الله عليه وسلم: «مَنْ مَاتَ وَهُوَ يَدْعُو مِنْ دُونِ اللهِ نِدًّا دَخَلَ النَّارَ» وَقُلْتُ أَنَا: مَنْ مَاتَ وَهُوَ لَا يَدْعُو لِلهِ نِدًّا دَخَلَ الْجَنَّةَ.
Daga Abdullahi Dan Mas'ud - Allah ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fadi wata kalma ni kuma na fadi wata daban, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya mutu alhali shi yana kiran kishiya wanin Allah zai shiga wuta" Ni kuma na ce: Wanda ya mutu alhali shi ba ya kiran kishiya ga Allah zai shiga aljanna.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bamu labarin cewa wanda ya karkatar da wani abu daga abinda yake wajaba ya zama na Allah ne zuwa waninSa, kamar rokon wanin Allah - Madaukakin sarki - ko neman agaji ga waninSa, ya kuma mutu akan hakan to cewa shi yana daga 'yan wuta. Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya kara cewa wanda ya mutu alhali ba ya hada wani abu da Allah to makomarsa tana aljanna.

Fa’idoji
  1. Addu'a ibada ce ba'a yinta sai ga Allah - Madaukakin sarki -.
  2. Falalar tauhidi, kuma cewa wanda ya mutu akansa zai shiga aljanna, koda an yi masa azaba akan sashin zunubai.
  3. Hadarin shirka, kuma cewa wanda ya mutu akanta zai shiga wuta.
Madogara

صحيح البخاري (6/ 23) (4497). صحيح مسلم (1/ 94) (92). فتح المجيد شرح كتاب التوحيد، لعبد الرحمن التميمي (ص76). القول المفيد على كتاب التوحيد، لابن عثيمين (1/ 120). الملخص في شرح كتاب التوحيد، لصالح الفوزان (ص47). الجديد في شرح كتاب التوحيد، لمحمد القرعاوي (ص59). التمهيد لشرح كتاب التوحيد، لصالح آل الشيخ (ص42).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
Kaɗaita Allah cikin bauta

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com