Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

SIFFAR SALLAH

Hadisai 42

Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana ɗaga hannayensa daura da kafaɗunsa in zai fara sallah,

عَن ابْنِ عُمَرَ رضي الله عنهما: أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ يَرْفَعُ يَدَيْهِ حَذْوَ مَنْكِبَيْهِ إِذَا افْتَتَحَ الصَّلَاةَ، وَإِذَا كَبَّرَ لِلرُّكُوعِ، وَإِذَا رَفَعَ رَأْسَهُ مِنَ الرُّكُوعِ، رَفَعَهُمَا كَذَلِكَ أَيْضًا، وَقَالَ: «سَمِعَ اللَّهُ لِمَنْ حَمِدَهُ، رَبَّنَا وَلَكَ الحَمْدُ»، وَكَانَ لاَ يَفْعَلُ ذَلِكَ فِي السُّجُودِ.
Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su -: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana ɗaga hannayensa daura da kafaɗunsa in zai fara sallah, haka nan in zai yi kabbara dan ruku'u, haka idan kuma zai ɗago kansa daga ruku'u sai ya ɗagasu, kuma ya ce: "Allah Ya ji wanda ya gode maSa, ya Ubangijinmu godiya ta tabbata gare ka, ya kasance ba ya yin haka a cikin sujjada.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya kasance yana ɗaga hannayensa agurare uku a sallah, daura da kafaɗa wanda shi ne: Matattarar ƙashin kafaɗa da damtse. Guri na farko: Idan zai buɗe sallah yayin kabbarar harama. Na biyu: Idan Zai yi kabbara dan ruku'u. Na uku: Idan ya ɗago kansa daga ruku'u kuma ya ce: Allah Ya ji wanda ya gode maSa, Ya Ubangijinmu godiya ta tabbata gareka. Ya kasance ba ya ɗaga hannayensa a lokacin fara sujjada, ko lokacin ɗagowa daga sujjada.

Fa’idoji
  1. Daga hikimomin ɗaga hannaye a cikin sallah cewa hakan ado ne ga sallah da kuma girmama Allah - tsarki ya tabbatar maSa -.
  2. Ɗaga hannaye ya tabbata daga gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - aguri na huɗu a cikin riwayar Abu Humaid al-Sa'idi a wajen Abu Dawud da waninsa, shi ne lokacin tasowa daga tahiyar farko a sallah mai raka'a uku da mai raka'a huɗu.
  3. Ya tabbata daga gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi yana ɗaga hannayensa daura da kunnuwansa ba tare da shafa ba, kamar yadda yake a cikin riwayar Malik ɗan Huwairis a cikin Bukhari da Muslim: "Cewa manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai yi kabbara yana ɗaga hannayensa har sai ya zo dasu daura da kunnuwansa".
  4. Haɗawa tsakanin Tasmi'i da Tahmidi wannan ya keɓanci liman da mai sallah shi kaɗai ne kawai, amma mamu sai ya ce: Ya Ubangijinmu godiya ta tabbata gareKa.
  5. Faɗin: "Ya Ubangijinmu godiya ta tabbata gareKa" bayan ruku'u ne kamar yadda ya inganta daga annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikinsa akwai sigogi huɗu, wannan ɗaya ce daga cikinsu, abin da yafi nutum ya bibiyi wadannan sigogin ya zo da wannan wani lokaci, wani lokacin kuma da wannan.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 148) (735). صحيح مسلم (1/ 292) (390). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 122). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص151). تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (2/ 192).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar dani Tahiya, tafukana tsakanin tafukansa, kamar yadda yake sanar dani sura daga Alkur’ani

عَنِ ابْنَ مَسْعُودٍ رضي الله عنه قَالَ: عَلَّمَنِي رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، وَكَفِّي بَيْنَ كَفَّيْهِ، التَّشَهُّدَ، كَمَا يُعَلِّمُنِي السُّورَةَ مِنَ القُرْآنِ: «التَّحِيَّاتُ لِلَّهِ، وَالصَّلَوَاتُ وَالطَّيِّبَاتُ، السَّلاَمُ عَلَيْكَ أَيُّهَا النَّبِيُّ وَرَحْمَةُ اللَّهِ وَبَرَكَاتُهُ، السَّلاَمُ عَلَيْنَا وَعَلَى عِبَادِ اللَّهِ الصَّالِحِينَ، أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، وَأَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّدًا عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ». وفي لفظ لهما: «إِنَّ اللهَ هُوَ السَّلَامُ، فَإِذَا قَعَدَ أَحَدُكُمْ فِي الصَّلَاةِ فَلْيَقُلْ: التَّحِيَّاتُ لِلَّهِ وَالصَّلَوَاتُ وَالطَّيِّبَاتُ السَّلَامُ عَلَيْكَ أَيُّهَا النَّبِيُّ وَرَحْمَةُ اللهِ وَبَرَكَاتُهُ، السَّلَامُ عَلَيْنَا وَعَلَى عِبَادِ اللهِ الصَّالِحِينَ، فَإِذَا قَالَهَا أَصَابَتْ كُلَّ عَبْدٍ لِلَّهِ صَالِحٍ فِي السَّمَاءِ وَالْأَرْضِ، أَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، وَأَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّدًا عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ، ثُمَّ يَتَخَيَّرُ مِنَ الْمَسْأَلَةِ مَا شَاءَ».
Daga Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar dani Tahiya, tafukana tsakanin tafukansa, kamar yadda yake sanar dani sura daga Alkur’ani : "(Tsarkakan) Gaisuwa ta tabbata ga Allah, da salloli da tsarkake-tsarkake, aminci ya tabbata agareka Ya kai wannan Annabi da rahamar Allah da albarkarSa, aminci ya tabbata agaremu da bayin Allah na gari, ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina shaida cewa Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne". Acikin wani lafazi na su: "Lallai cewa Allah Shi ne aminci, idan dayanku ya zauna a cikin sallah to ya ce: (Tarakakan) Gaisuwa sun tabbata ga Allah da salloli da tsarkake-tsarkake, aminci ya tabbata agreka Ya kai wannan Annabi da rahamar Allah daalbarkarSa, aminci ya tabbata agaremu da bayin Allah na gari. Idan ya fadeta za ta samu kowanne bawan Allah nagari a sama da kasa, ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah ina shaida cewa Annabi Muhammad bawanSa ne kuma manzonsa ne, sannan ya zabi abin yake so ya roka".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar da Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - Tahiyar da ake fada a cikin sallah, hakika ya sanya hannunsa a cikin hannayensa, dan ya karkato da hankalin Dan Mas'ud gare shi, kamar yadda yake sanar da shi sura daga Alkur’ani abinda yake nuni akan kulawar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da wannan Tahiyar lafazi da ma'ana. Sai ya ce: "(Tsarkakan) Gaisuwa sun tabbata ga Allah": Su ne kowacce magana ko aiki mai shirayrwa akan girmamawa, dukkaninsu ababen cancantane ga Allah - Mai girma da daukaka -. "Salloli": Ita ce sananniyar sallah ta farilla da ta nafila, sun tabbata ga Allah - Madaukakin sarki -. "Tsarkakan Maganganu": Su ne maganganu da ayyuka da siffofi tsarkaka masu nuni akan cika, dukkaninsu ababen cancanta ne ga Allah - Madaukakin sarki -. "Aminci ya tabbata agareka Ya kai wannan Annabi da rahamar Allah da albarkarSa': Addu'ace gare shi da aminta daga dukkanin cututtuka da abin ki, da kari da yawaita a kowanne alheri. "Aminci ya tabbata agaremu da bayin Allah na gari": Addu'ace da aminta daga mai sallah da kuma kowanne bawa na gari a sama da kasa. "Ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah': Wato ina tabbatarwa tabbatarwa a yanke cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. "Kuma cewa Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne": Ina tabbatarwa a gare shi da bauta da Manzanci na karshe. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwadaitar da mai yin sallah ya zabi abinda yaso na addu'a ya roka.

Fa’idoji
  1. Bigiren wannan Tahiyar shi ne zama bayan sujjada ta karshe a kowacce sallah, da kuma bayan raka'a ta biyu a sallah mai raka'a uku da mai raka'a hudu.
  2. Wajabcin gaishe-gaishe a Tahiya, yana halatta ya yi tahiya da kowanne lafazi daga lafazan tahiya daga abinda ya tabbata daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  3. Halaccin addu'a da abinda mutum ya so muddin dai ba sabo ba ne.
  4. An so farawa da kai a cikin addu'a.
Madogara

صحيح البخاري (8/ 59) (6265). صحيح مسلم (1/ 301) (402). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 168). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص206). خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام، لفيصل آل مبارك (ص94).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Manzon Allah ya kasance in zaiyi salla sai yayi kabbara yayin da yake mikewa, sannan kuma yana yin kabbara yayin da yake yin ruku'u, sannan yana cewa: Allah ya ji mai gode masa, yayin da yake dago bayansa daga raka'a

عن أبي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قال: كان رسول الله صلى الله عليه وسلم إذا قام إلى الصلاة يُكَبِّرُ حين يقوم، ثم يُكَبِّرُ حين يركع، ثم يقول: سَمِعَ اللَّه لِمَنْ حَمِدَهُ، حين يَرْفَعُ صُلْبَهُ من الرَّكْعَةِ، ثم يقول وهو قائم: ربنا ولك الحمد، ثم يُكَبِّرُ حين يَهْوِي، ثم يُكَبِّرُ حين يَرْفَعُ رأسه، ثم يُكَبِّرُ حين يَسْجُدُ، ثم يُكَبِّرُ حين يَرْفَعُ رأسه، ثم يفعل ذلك في صلاته كلها حتى يقضيها، ويُكَبِّرُ حين يقوم من الثِّنْتَيْنِ بعد الجلوس، ثم يقول: أبو هريرة «إني لأشَبَهُكم صلاة برسول الله صلى الله عليه وسلم ».
Daga Abu Huraira-Allah ya yarda da shi- yace: Manzon Allah ya kasance in zai yi salla sai ya yi kabbara yayin da yake mikewa , sannan kuma yana yin kabbara yayin da yake yin ruku'u, sannan yana cewa-Allah ya ji mai gode masa, yayin da yake dago bayansa daga raka'a,sannan bayan ya mike yana cewa': ya Ubangijinmu a gare ka dukkanin godiya ta tabbata gare ka, sannan sai ya yi kabbara lokacin da yake tafiya zuwa sujjada, sannan sai ya yi kabbara liokacin sdago kansa daga sujjada, sannansai yayi kabbara yayin da yake yin sujjada, sannan sai yayi kabbara yayinda yake dago kansa, sannan sai ya aikata irin haka a cikin sallarsa dukanta har zuwa karshe, haka kuma yana yin kabbara yayin da yake mike wa daga tahiyar farko, sannan yace: "lallai nine na fiko iya kamant a sallar Manzo tsira da aminci su tabbata a gare shi"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Salla dukkaninta girmama Allah ne ta hanyar zance da aiki, acikin wannan hadisin madaukaki akwai bayanin shiar na salla, shine tabbatar da girma ga Allah madaukaki, babban abin da ya kara nuna girmanta shi ne shar'anta ta da aka yi don girmama Allah da daukaka shi. A lokacin da masallaci zai fara salla sai ya yi kabbarar harama yana tsaye ya daidaita.bayan ya gama karatu ya tafi zuwa ruku'u,sai yayi kabbar, idan ya dago daga ruku'u, sai yace: Allah ya ji mai gode masa ,sai ya mike sosai sai ya godewa Allah ya yabe shi a tsayen,sai ya sake kabbara don kai goshi sujjada, sannan sai ya yi kabbara yayin da yake dago kansa daga sujjada,sai ya aikata haka a cikin dukkan salarsa, har ya kammala,idan ya mike don ciko raka'oi biyu bayan tahiya ta farko sa i ya yi kabbara yayin da yake mikewa. kuma shari'a ta sanya yin kabbara a kowane guri sai dai a waje dagowa daga ruku'u

Madogara

الإلمام بشرح عمدة الأحكام لإسماعيل الأنصاري، ط1، دار الفكر، دمشق، 1381ه تيسير العلام شرح عمدة الأحكام للبسام، حققه وعلق عليه وخرج أحاديثه وصنع فهارسه: محمد صبحي بن حسن حلاق، ط10، مكتبة الصحابة، الإمارات - مكتبة التابعين، القاهرة، 1426 هـ تنبيه الأفهام شرح عمدة لأحكام لابن عثيمين، ط1، مكتبة الصحابة، الإمارات، 1426ه عمدة الأحكام من كلام خير الأنام صلى الله عليه وسلم لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، ط2، دار الثقافة العربية، دمشق ، بيروت، مؤسسة قرطبة، 1408 هـ صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422ه. صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، 1423 هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ku daidaita a cikin sujjada, kar ku shimfida zira'oinku irin yadda kare ke shimfida nasa.

عن أَنَس بن مالك رضي الله عنه عَنْ النَّبِيِّ صلى الله عليه وسلم قَالَ: «اعْتَدِلُوا في السجود، ولا يَبْسُطْ أحدكم ذِرَاعَيْهِ انْبِسَاطَ الكلب».
Daga Anas Dan Malik -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Ku daidaita a cikin sujjada, kar ku shimfida zira'oinku irin yadda kare ke shimfida nas
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi tsira da aminci yayi umarni da a daidaita cikin sujjada, ta yadda mai yin salla zai kasance cikin kyakkyawar kama a lokacin sujjada, ta yadda zai sa tafukansa a kasa, ya daga zirao'insa ya nesanta su da d kuibukansa, saboda wannan yanayin shi ne alamar karsashi dakwadayi wadanda ake nema a cikin salla, kuma irin wannan yanayin kan bada dama ga ko wace gaba ta sami nata rabon na ibada, an yi hani ga shimfida hannaye a cikin sujjada, don yana jawo lalaci da kosawa, kuma yinsa yin kama da kare ne, wanda bai dace ga mai yin salla ba.

Madogara

- صحيح البخاري -الجامع الصحيح-؛ للإمام أبي عبد الله محمد بن إسماعيل البخاري، عناية محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة، الطبعة الأولى، 1422هـ. - صحيح مسلم؛ للإمام مسلم بن الحجاج، حققه ورقمه محمد فؤاد عبد الباقي، دار عالم الكتب، الرياض، الطبعة الأولى، 1417هـ. - الإلمام بشرح عمدة الأحكام للشيخ إسماعيل الأنصاري -مطبعة السعادة- الطبعة الثانية 1392ه. - تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام -محمد بن صالح العثيمين -رحمه الله- مكتبة الصحابة -الشارقة- الإمارات العربية المتحدة، الطبعة الأولى، 1426هـ. - تيسير العلام شرح عمدة الأحكام -عبد الله البسام- تحقيق محمد صبحي حسن حلاق -مكتبة الصحابة- الشارقة، الطبعة العاشرة، 1426هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Na lura da sallar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- sai na sami tsayuwarsa, da ruku'unsa, da daidaitonsa bayan ruku'u,da sujjadarsa, da zamansa tsakanin sujjada biyu, da zamansa tsakanin sallama da juyawa: kusan daidai da daidai.

عن الْبَرَاءِ بْنِ عَازِبٍ رضي الله عنهما قال: «رَمَقْتُ الصلاة مع محمد صلى الله عليه وسلم فوجدت قيامه، فَرَكْعَتَهُ، فاعتداله بعد ركوعه، فسجدته، فَجِلْسَتَهُ بين السجدتين، فسجدته، فَجِلْسَتَهُ ما بين التسليم والانصراف: قريبا من السَّوَاء». وفي رواية: «ما خلا القيام والقعود، قريبا من السَّوَاءِ».
Daga Bara'u Dan Azib - Allah ya yarda da shi- yace: "Na lura da sallar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- sai na sami tsayuwarsa, da ruku'unsa, da daidaitonsa bayan ruku'u,da sujjadarsa, da zamansa tsakanin sujjada biyu, da zamansa tsakanin sallama da juyawa: kusan daidai da daidai
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Bara'u Dan Azib -Allah ya yarda da su- yana sifanta sallar Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi- lokacin da yake lura da sallar Annabi yake kwaikwayonsa, ya ambata mana cewa kusan daidai da daidai ayyukansa suke, saboda tsayuwarsa don karatun salla da zamansa na tahiya kusan daidai suke ga ruku'u da daidaito da sujjada baya dadewa a tsaye kuma yayi gajeren ruku'u, ko ya tsawaita sujjada, sannan kuma ya yi gajeriyar tsayuwa ko zama ba, a'a yana yin ko wane rukuni ya dace da ko wanne. Ba ana nufin : tsayuwa da zaman tahiya su yi daidai da ruku'u ko sujjada ba. Abin nufi ba ya yin wani kadan ya dade a wani.

Madogara

تيسير العلام، للبسام، الناشر: مكتبة الصحابة، الإمارات، مكتبة التابعين، القاهرة، الطبعة العاشرة، 1426هـ - 2006 م. تنبيه الأفهام، للعثيمين، طبعة مكتبة الصحابة الإمارات، مكتبة التابعين، القاهرة، الطبعة الأولى، 1426. تهذيب اللغة, المؤلف: محمد بن أحمد بن الأزهري الهروي، المحقق: محمد عوض مرعب, الناشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت, الطبعة: الأولى، 2001م. - تأسيس الأحكام، لأحمد بن يحيى النجمي, طبعة دار المنهاج. صحيح البخاري، لأبي عبد الله محمد بن إسماعيل البخاري، تحقيق محمد زهير بن ناصر الناصر، الناشر: دار طوق النجاة، الطبعة: الأولى 1422هـ. صحيح مسلم، المحقق: محمد فؤاد عبد الباقي - الناشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Koma ka yi sallah domin cewa kai baka yi sallah ba

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه: أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ دَخَلَ المَسْجِدَ فَدَخَلَ رَجُلٌ، فَصَلَّى، فَسَلَّمَ عَلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَرَدَّ وَقَالَ: «ارْجِعْ فَصَلِّ، فَإِنَّكَ لَمْ تُصَلِّ»، فَرَجَعَ يُصَلِّي كَمَا صَلَّى، ثُمَّ جَاءَ، فَسَلَّمَ عَلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: «ارْجِعْ فَصَلِّ، فَإِنَّكَ لَمْ تُصَلِّ» ثَلاَثًا، فَقَالَ: وَالَّذِي بَعَثَكَ بِالحَقِّ مَا أُحْسِنُ غَيْرَهُ، فَعَلِّمْنِي، فَقَالَ: «إِذَا قُمْتَ إِلَى الصَّلاَةِ فَكَبِّرْ، ثُمَّ اقْرَأْ مَا تَيَسَّرَ مَعَكَ مِنَ القُرْآنِ، ثُمَّ ارْكَعْ حَتَّى تَطْمَئِنَّ رَاكِعًا، ثُمَّ ارْفَعْ حَتَّى تَعْدِلَ قَائِمًا، ثُمَّ اسْجُدْ حَتَّى تَطْمَئِنَّ سَاجِدًا، ثُمَّ ارْفَعْ حَتَّى تَطْمَئِنَّ جَالِسًا، وَافْعَلْ ذَلِكَ فِي صَلاَتِكَ كُلِّهَا».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Cewa Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -ya shiga masallaci, sai wani mutum ya shigo, sai ya yi sallah, sannan (ya zo) ya yi sallama ga Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata agare shi-sai ya amsa masa kuma ya ce: Koma ka yi sallah domin cewa kai baka yi sallah ba", sai ya koma ya yi sallah kamar yadda ya yi sallar, sannan ya zo ya yi sallama ga-Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: "Koma ka yi sallah, domin cewa kai baka yi sallah ba" sau uku, sai ya ce: Na rantse da wanda ya aikoka da gaskiya ba zan iya yin wacce ta fita ba, to ka koya mini, sai ya ce: "Idan ka tashi zuwa sallah to ka yi kabbara, sannan ka karanta abinda ya sawwaka tare da kai na Alkur'ani, sannan ka yi ruku'u har sai ka natsu kana mai ruku'u, sannan ka dago har sai ka daidaita a tsaye, sannan ka yi sujjada har sai ka natsu kana mai sujjada, sannan ka dago har sai ka natsu a zaune, kuma ka aikata hakan acikin sallarka gaba dayanta".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiga masallaci, sai wani mutum ya shigo a bayansa sai ya yi sallah raka'a biyu da gaggawa, bai nutsu a cikin tsayuwarsa da ruku'unsa da sujjadarsa ba, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana lura da shi a cikin sallarsa, sai ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a lokacin Ma’aikin Allah yana zaune a gefen masallaci sai ya yi masa sallama, sai ya amsa masa sallamar, kuma ya ce masa: Ka koma ka sake sallarka, domin kai baka yi sallah ba. Sai ya dawo yana sallah da gaggawa kamar yadda ya yi sallar, sannan ya zo sai ya yi sallama ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce masa: Ka koma ka yi sallah; domin kai baka yi sallah ba, ya aikata haka sau uku. Sai mutumin ya ce: Na rantse da wanda Ya aikoka da gaskiya, ba zan iya yin wacce tafi wannan ba to ka koya mini, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Idan ka tashi zuwa sallah to ka yi kabbarar harama, sannan ka karanta Fatiha da kuma abinda Allah Ya so ka karanta, sannan ka yi ruku'u har sai ka natsu kana mai ruku'u, shi ne ka sanya tafukanka biyu akan gwiwoyinka sai ka miƙar da bayanka ka tabbata dan yin ruku'inka, sannan ka ɗago ka daidaita bayanka har sai ƙasusuwa sun koma mararrabarsu kuma ka daidaita a tsaye, sannan ka yi sujjada har sai ka natsu kana mai sujjada, shi ne ka tabbatar da goshi tare da hanci, da hannaye da gwiwoyi da geffan diga-digai akan ƙasa, sannan ka ɗago har sai ka natsu kana zaune tsakanin sujjada biyu, sannan ka aikata hakan a kowace raka'a ta sallarka.

Fa’idoji
  1. Waɗannan rukunan na sallah, ba sa faɗuwa ba da rafkanuwa ba ba kuma da jahilci ba, saboda dalilin umartar mai sallar da sakewa, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai isu da koyar dashi ba (saida ya sashi ya sake).
  2. Natsuwa rukuni ce daga cikin rukunan sallah.
  3. Nawawi ya ce: A cikinsa cewa wanda ya ɓata wasu wajiban sallah to sallarsa ba ta inganta ba.
  4. Nawawi ya ce: Kuma a cikinsa akwai sauƙaƙawa ga mai neman sani da kuma jahili da sassauta masa, da bayyanar da masa'alar gare shi da rairaye manufofi, da taƙaitawa a matakinsa akan manyan mihimmai banda wadanda suke cikawa waɗanda halinsa ba zai iya ɗaukar iya kiyayesu da kuma tsayuwa da su ba.
  5. Nawawi ya ce: Kuma a cikinsa cewa mai bada fatawa idan an tambaye shi game da wani abu, kuma a nan akwai wani abu daban da mai tambayar yake buƙatuwa zuwa gare shi kuma bai tambaye shi ba to an so ga matawar ya faɗa masa shi, kuma wannan ya zama daga nasiha ne ba daga zancen da bai shafe shi ba ne.
  6. Falalar iƙirari da kasawa saboda faɗinsa; "Ba zan iya yin wacce ta fi ta ba to ka koya mini".
  7. Ibnu Hajar ya ce: Kuma a cikinsa akwai horo da aikin alheri da kuma hani daga abin ƙi, da kuma neman mai neman sani daga malami cewa ya koya masa.
  8. An so yin sallama a lokacin haɗuwa, da kuma wajabcin amsa ta, kuma an so maimaitata idan haɗuwa ta maimaitu koda ba'ajima ba, kuma cewa wajibi ne ya amsa masa a kowane lokaci.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 152) (757). صحيح مسلم (1/ 298) (397). تيسير العلام، للبسام (ص167). تنبيه الأفهام، للعثيمين (2/ 213). الإفهام في شرح عمدة الأحكام، عبد العزيز بن باز (ص203). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 138).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Lallai cewa Annabi ya kasance yana Sallah kuma ya na dauke da Umama Yar Zainab Yar Annabi

عن أبي قَتَادَةَ الأَنْصَارِيِّ رضي الله عنه قال: «أن رسول الله صلى الله عليه وسلم كان يُصَلِّي وهو حامل أُمَامَةَ بنت زينب بنت رسول الله صلى الله عليه وسلم ». ولأبي العاص بن الربيع بن عبد شَمْسٍ رضي الله عنه : «فإذا سجد وضعها، وإذا قام حملها».
Daga Katada Al'ansary ya ce: "allai cewa Annabi ya kasance yana Sallah kuma ya na dauke da Umama Yar Zainab Yar Annabi"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi ya kasance yana Daukar Yar Diyarsa kuma ita Umama Diyar Zainab kuma a halin yana cikin Sallah, yadda yake sanya ta a kafarsa idan ta tsaya, to idan yai ruku'i ko yayi sujada sai ya ajiye ta a kasa don son da yake mata da kuma tausayawa

Madogara

تيسير العلام للبسام الناشر: مكتبة الصحابة، الأمارات - مكتبة التابعين، القاهرة الطبعة- العاشرة، 1426 هـ - 2006 م . تنبيه الأفهام للعثيمين -طبعة مكتبة الصحابة الامارات - مكتبة التابعين- القاهرة- الطبعة الأولى 1426. صحيح البخاري -أبو عبد الله محمد بن إسماعيل بن إبراهيم بن المغيرة الجعفي البخاري، تحقيق محمد زهير بن ناصر الناصر - الناشر : دار طوق النجاة -الطبعة : الأولى 1422هـ. صحيح مسلم المحقق: محمد فؤاد عبد الباقي - الناشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت. تأسيس الأحكام -أحمد بن يحيى النجمي- دار المنهاج- القاهرة- مصر -الطبعة الأولى.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Na yi salla tare da Abu Bakr, Omar da Othman, kuma ban ji ɗayansu ya karanta "Da sunan Allah ba, Mai jin ƙai, Mai jin ƙai."

عن أَنَس بن مالك رضي الله عنه «أنّ النبي صلى الله عليه وسلم وأبا بكر وعمر رضي الله عنهما : كانوا يَسْتَفْتِحُونَ الصلاة بـ"الحمد لله رب العالمين"». وفي رواية: « صَلَّيْتُ مع أبي بكر وعمر وعثمان، فلم أسمع أحدا منهم يقرأ "بسم الله الرحمن الرحيم"». ولمسلم: « صَلَّيْتُ خلف النبي صلى الله عليه وسلم وأبي بكر وعمر وعثمان فكانوا يَسْتَفْتِحُونَ بـ"الحمد لله رب العالمين"، لا يَذْكُرُونَ "بسم الله الرحمن الرحيم" في أول قراءة ولا في آخرها».
Daga Anas bn Malik - yardar Allah ta tabbata a gare shi - "Annabi mai tsira da amincin Allah, da Abubakar da Omar - Allah ya yarda da su - sun kasance suna gabatar da salla da" Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai ". Kuma a cikin wani labari: "Na yi Sallah tare da Abubakar, Umar da Othman, kuma ban ji wani daga cikinsu yana karantawa ba" Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai. " Kuma ga Muslim: "Na yi addu'a a bayan Annabi - Salatin Allah da amincin Allah su tabbata a gare shi - da Abu Bakr, Umar da Othman, kuma suka bude da" Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai, "ba za su ambaci" Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai, "a farkon ko ƙarshen karatun.
Muslim ne ya rawaito shi - Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

تيسير العلام للبسام، الناشر: مكتبة الصحابة، الغمارات - مكتبة التابعين، القاهرة الطبعة- العاشرة، 1426 هـ - 2006 م . تنبيه الأفهام للعثيمين -طبعة مكتبة الصحابة الإمارات - مكتبة التابعين- القاهرة- الطبعة الأولى 1426. الإفهام في شرح عمدة الأحكام –عبد العزيز بن باز-اعتناء سعيد بن علي بن وهف القحطاني –الرياض –الطبعة الأولى -1435. الإلمام بشرح عمدة الأحكام لإسماعيل الأنصاري -طبعة دار الفكر- دمشق -الأولى 1381. خلاصة الكلام –فيصل المبارك الحريملي -الطبعة: الثانية، 1412 هـ - 1992 م. صحيح البخاري -أبو عبد الله محمد بن إسماعيل البخاري، تحقيق محمد زهير بن ناصر الناصر -الناشر : دار طوق النجاة -الطبعة : الأولى 1422هـ. صحيح مسلم - المحقق: محمد فؤاد عبد الباقي - الناشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
8 cikin 42
Hadisai 42
  1. Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana ɗaga hannayensa daura da kafaɗunsa in zai fara sallah,
  2. Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar dani Tahiya, tafukana tsakanin tafukansa, kamar yadda yake sanar dani sura daga Alkur’ani
  3. Manzon Allah ya kasance in zaiyi salla sai yayi kabbara yayin da yake mikewa, sannan kuma yana yin kabbara yayin da yake yin ruku'u, sannan yana cewa: Allah ya ji mai gode masa, yayin da yake dago bayansa daga raka'a
  4. Ku daidaita a cikin sujjada, kar ku shimfida zira'oinku irin yadda kare ke shimfida nasa.
  5. Na lura da sallar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- sai na sami tsayuwarsa, da ruku'unsa, da daidaitonsa bayan ruku'u,da sujjadarsa, da zamansa tsakanin sujjada biyu, da zamansa tsakanin sallama da juyawa: kusan daidai da daidai.
  6. Koma ka yi sallah domin cewa kai baka yi sallah ba
  7. Lallai cewa Annabi ya kasance yana Sallah kuma ya na dauke da Umama Yar Zainab Yar Annabi
  8. Na yi salla tare da Abu Bakr, Omar da Othman, kuma ban ji ɗayansu ya karanta "Da sunan Allah ba, Mai jin ƙai, Mai jin ƙai."
  9. Lallai cewa Annabi ya aika Wani Mutum a wani yaki sai ya kasane yana" karantawa abokansa in yana jansu Sallah, Sai yake cika karatunsa da: Kulhuwa.
  10. Manzon Allah mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi ya kasance yana bude salla da yin kabbara, da karatu, da fadar Alhamdu lillahi rabbil aalamina, ya kasance idan yayi ruku`u baya dago kansa, baya kuma mikar da shi saidai tsaka tsaki
  11. Ni da Imran bn Husayn mun yi salla a bayan Ali bin Abi Dalib, don haka idan ya yi sujjada, sai ya ce takbire, idan ya daga kansa sai ya ce takbire, idan kuma ya tashi daga rakaoin biyu, zai ce takbire.
  12. Na ji Annabi -tsira da amincin Allah- yana karanta Suratuddur a Sallar Magariba.
  13. Lallai ni wallahi zan yi muku sallah , amma ba sallar nake nufi ba, ina yin sallah ne yadda naga manzon Allah mai tsira da aminchi yake yin sallah.
  14. Idan liman ya ce Ameen kuma ku ce Ameen ,domin duk wanda Ameen dinsa ta dace da ta Mala'iku to an gafarta masa abunda ya gabata na zunubansa.
  15. Allah ka kuvutar da Ayyash Bn Abi rabi'a Ya Ubanhiji ka kuvutar da Sakamah Bn Hisham Ya Ubangiji ka kuvutar da Al-walid Bn Alwalid, Ya Ubangiji ka kuvutar da raunanan Muminai, Ya Ubangiji ka tsananta Kamunka ga Mudhar, Allah ka sanya musu yinwa kamar Shekarun Annabi Yusuf
  16. Naga Manzon Allah SAW yana yiwa Mutane limanci kuma umama Bint Abi Al-as ita ce Xiyar Zainab Xiyar Manzon Allah SAW tana kan kafaxarsa, idan yayi Ruku'u sai ya Ajiye ta, kuma idan ya Xago daga Sujada sai ya Mayar da ita
  17. Ku Kashe Baqaqe biyu ko a cikin Sallah ne: Macijiya da kuma Kunama
  18. Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana buɗe sallah da kabbara, da kuma karatu, da (faɗar) Alhamdu lillahi rabbil aalamina (Dukkan yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai)
  19. Cewa Manzon Allah SAW ya kasance idan zai kabbara yana xaga Hannayensa har sai sunkai daidai Kunnuwansa, kuma idan yayi ruku'u yana xaga Hannayensa har sukai daidai kunnuwansa
  20. Nayi Sallah tare da Manzon Allah SAW ya sanysa Hannunsa na Dama kan Hannunsa na Hagu akan Qirjinsa
  21. Abin da na yi a bayan wani kamar addu’ar Manzon Allah ne, amincin Allah ya tabbata a gare shi, daga haka-da-haka.
  22. An umarceni in yi sujjada akan gabbai bakwai
  23. Idan zaka yi sujjada, to ka sanya tafukanka ka kuma ɗaga gwiwowin hannunka
  24. Cewa Manzon Allah SAw ya kasance ian ya yayi Ruku'u yana rarraba 'Yanyatsunsa kuma idan yayi Sujada sai ya haxe su
  25. Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana faɗa a tsakanin sujjada biyu; "Ya Ubangiji ka gafarta min, ka yi min rahama, ka ba ni lafiya, ka shiryar da ni, ka azurta ni
  26. Lallai cewa Manzon Allah SAW idan ya kasanc a Wuturin Sallarsa baya tashi har sai ya daidaita a zaune
  27. Lallai cewa Manzon Allah SAW yayi Al-qunuti Wata xaya bayan Ruku'u yana Addu'a ga wasu Mutane daga Qabilar Bani Sulaim
  28. Lallai cewa Manzon Allah SAW ya kasance baya Al-qunuti sai in zai Addu'a ga wasu Mutane, ko yayi Addu'a kan wasu Mutane
  29. Ya Babana lallai kai kayi Sallah bayan Manzon Allah SAW da kuma Abubakar da Umar da Usman da Ali a nan Kufa, wajen Shekara Biyar, shin sun kasance suna Al-qunuti a Asuba? sai ya ce: Ai Xana Wannan fararre ne
  30. Idan Xayanku zai yi Sujada kada ya Durkusa kamar yadda Raqumi yake Durqusawa, ya fara sanya Hannayensakafin Guiwoyinsa
  31. Lallai cewa Ibn umar ya kasance yana sanya Hannayensa kafin guiwoyinsa, kuma ya ce: Manzon Allah SAW ya kasance yana yin hakan
  32. Manzon Allah SAW ya kasance idan ta zauna yana Addu'a, kuma yana sanya Hannunsa na dama akan cinyarsa ta dama kuma Hannunsa na Hagu kan cinyarsa ta Hagu, kuma yana nuni da Xanyatsansa na nuni, kuma yana sanya Babban Xanyatsansa a kan na tsakiya, kuma yana xora tafin Hannunsa na Hagu kan kan Guiwarsa
  33. Na yi sallah tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya kasance yana yin sallama a damansa: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh. "Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa", kuma a hagunsa: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh. "Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah
  34. Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya karanta {قل يأيها الكافرون} da {قل هو الله أحد} a raka'o'i biyu (kafin sallar) Asuba
  35. ya ku mutane, kawai na aikata haka ne don ku yi koyi da ni, kuma ku san sallata
  36. Idan za ku yi sallah, to, ku daidaita sahunku, sannan ɗayanku ya yi muku limanci, idan ya yi kabbara sai ku yi kabbara
  37. na rantse da wanda raina yake a hannunSa lallai ni ne mafi kusancinku kamanceceniya da sallar manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wannan ita ce sallarsa har ya bar duniya
  38. Mafi munin mutane sata shi ne wanda yake satar sallarsa" sai ya ce: Ta yaya zai saci sallarsa? sai ya ce: "Ya zamo ba ya cika ruku'unta, ba ya cika sujjadarta
  39. Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance idan ya ɗago bayansa daga ruku'u sai ya ce: "Allah Ya ji wanda ya gode maSa
  40. Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a tsakanin sujjada biyu; "Ya Ubangijina Ka gafarta mini, ya Ubangijina Ka gafarta min'
  41. Wannan wani Sahiɗan ne ana ce masa khinzab, idan ka ji shi ka nemi tsarin Allah daga gare shi, ka yi tofi a hagunka sau uku
  42. Na kasance ina ganin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana yin sallama a damansa da kuma hagunsa, har ina ganin farin kundukukinsa

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com