Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

An umarceni in yi sujjada akan gabbai bakwai

عن ابنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما عن النبيِّ صلى الله عليه وسلم قال: «أُمِرْتُ أَنْ أَسْجُدَ عَلَى سَبْعَةِ أَعْظُمٍ: عَلَى الْجَبْهَةِ وَأَشَارَ بِيَدِهِ عَلَى أَنْفِهِ، وَالْيَدَيْنِ، وَالرُّكْبَتَيْنِ، وَأَطْرَافِ الْقَدَمَيْنِ، وَلَا نَكْفِتَ الثِّيَابَ وَالشَّعَرَ».
Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "An umarceni in yi sujjada akan gabbai bakwai: Akan goshi sai ya yi nuni da hannunsa akan hancinsa, da hannaye, da gwiwoyi, da gefunan diga-digai, kuma kada ka tufke tufafi ko gashi".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa Allah Ya umarce shi a yayin sallah ya yi sujjada akan gabbai bakwai na jiki; su ne: Na farko: Goshi: Shi ne: Fatar fuska a saman hanci da idanuwa, Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi nuni zuwa hancinsa, yana mai bayyana cewa goshi da hanci gaba daya ce daga bakwan, da kuma karfafa cewa mai sujjada yana shafar kasa da hancinsa. Gaba ta biyu da ta uku: Hannaye. Ta hudu da ta biyar: Gwiwoyi. ta shida da ta bakwai: 'Yan yatsun diga-digai. Kuma ya umarcemu kada mu daure gashin mu, ko mu tattaro tufafinmu sashinsu akan sashi a yayin sujjada akan kasa dan karesu; kai ya sake su har su sauka a kasa, sai ka yi sujjada tare da gabbai.

Fa’idoji
  1. Wajabcin yin sujjada a cikin sallah akan gabbai bakwai.
  2. Karhancin tattaro tufafi da gashi a cikin sallah.
  3. Yana wajaba akan mai sallah ya natsu a cikin sallarsa, hakan ya sanya gabban sujjada guda bakwai akan kasa, ya tabbata akansu har ya zo da zikirin da aka shara'anta.
  4. Hani daga kame gashi (wannan) ya kebanci maza banda mata; domin cewa mace a cikin sallah abar umarta ce da sutaurtawa.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 162) (812). صحيح مسلم (1/ 354) (490). المنهاج شرح صحيح مسلم، للنووي (4/ 206). مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي القاري (2/ 718). سبل السلام شرح بلوغ المرام، للصنعاني (1/ 270). توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، لعبد الله البسام (2/ 229). فتح ذي الجلال والإكرام شرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (2/ 115). منار القاري، لحمزة قاسم (2/ 202).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
SIFFAR SALLAH

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com