Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Idan zaka yi sujjada, to ka sanya tafukanka ka kuma ɗaga gwiwowin hannunka

عَنِ الْبَرَاءِ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِذَا سَجَدْتَ، فَضَعْ كَفَّيْكَ وَارْفَعْ مِرْفَقَيْكَ».
Daga Bara'u - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce -: "Idan zaka yi sujjada, to ka sanya tafukanka ka kuma ɗaga gwiwowin hannunka".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana halin hannaye a cikin sujjadar sallah, hakan da ya tabbatar da tafukansa a ƙasa kuma ya ɗora yatsun a ɗunƙule a fuskantar alƙibla, kuma gwiwowin hannaye - sune mararrabar zira'i da damutse - a ɗage daga taɓ ƙasa kuma a buɗe daga sasanni.

Fa’idoji
  1. Wajibi akan mai sallah ya ɗora tafukansa akan ƙasa, tafuka biyu gaɓɓai ne daga gaɓɓan sujjada guda bakwai.
  2. An so ɗaga zira'i biyu daga ƙasa, da karhancin shinfiɗasu kamar yadda zaki yake shinfiɗa zira'ansa biyu.
  3. Halaccin bayyanar da nishaɗi da ƙarfi da kwaɗayi a cikin ibada.
  4. Mai yin sallah idan ya dogara akan dukkan gaɓɓan sujjada, to kowace gaɓa zata riƙi haƙƙinta na ibada.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 356) (494). سبل السلام شرح بلوغ المرام، لمحمد الصنعاني (1/ 273). توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، لعبد الله البسام (2/ 235). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص162).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
SIFFAR SALLAH

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com