Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a tsakanin sujjada biyu; "Ya Ubangijina Ka gafarta mini, ya Ubangijina Ka gafarta min'

عن حُذَيْفَةَ رضي الله عنه: أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ يَقُولُ بَيْنَ السَّجْدَتَيْنِ: «رَبِّ اغْفِرْ لِي، رَبِّ اغْفِرْ لِي».
Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi -: Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a tsakanin sujjada biyu; "Ya Ubangijina Ka gafarta mini, ya Ubangijina Ka gafarta min'.
Abu Daud da Nasa'i da Ibnu Majah da Ahmad ne suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a yayin zama a tsakaknin sujjada biyu: Ya Ubangina ka gafarta min, yana maimaita ta. Ma'anar ya Ubangijina Ka gafarta min: Bawa yana neman daga Ubangijinsa ya shafe masa zunubansa ya suturta aibukansa.

Fa’idoji
  1. Shar’antuwar wannan addu'ar a tsakanin sujjada biyu a sallar farilla da nafila.
  2. An so maimaita faɗin: Ya Ubangijina Ka gafarta min, wajibi (shi ne) sau ɗaya.
Madogara

سنن أبي داود (2/ 154) (874)، سنن النسائي (2/ 231) (1145)، سنن ابن ماجه (2/ 64) (897)، مسند أحمد (38/ 392) (23375)، نيل الأوطار (2/ 305).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
SIFFAR SALLAH

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com