Usman ɗan Abul Aas - Allah Ya yarda da shi - ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah lallai cewa Shaiɗan haƙiƙa ya shiga tsakanina da sallata ya hanani khushu'i a cikinta, ya cakuɗa min karatuna ya sa ni kokwanto a cikinta, Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Wannan Shaiɗan ne ana ce masa Khinzab, idan ka ka sami hakan, kuma ka ji shi ka nemi mafaka a wurin Allah, ka nemi tsarin Allah daga gare Shi, ka yi tofi a hagunka tare da yawu kaɗan sau uku, Usman ya ce: Sai na aikata abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya umarce ni da shi, sai Allah Ya tafiyar da shi daga gareni.
- Muhimmnacin khushu'i da halartowar zuciya a sallah, kuma cewa Shaiɗan yana ƙoƙari a sa ruɗu da kokwanto a cikinta.
- An so neman tsarin Allah daga Shaiɗan a yayin waswasinsa a sallah, tare da tofi a hagu sau uku.
- Bayanin abin da sahabbai - Allah Ya yarda da su - suke a kansa na komawarsu zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a cikin abin da yake faruwa garesu na matsaloli har ya warware musu su.
- Rayuwar zuciyar sahabbai, kuma cewa himmarsu (damuwarsu) ita ce lahira
صحيح مسلم (4/ 1728) (2203)، إكمال المعلم (7/110)، شرح النّووي على مسلم (14/190)، البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (36/ 136).