Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar da Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - Tahiyar da ake fada a cikin sallah, hakika ya sanya hannunsa a cikin hannayensa, dan ya karkato da hankalin Dan Mas'ud gare shi, kamar yadda yake sanar da shi sura daga Alkur’ani abinda yake nuni akan kulawar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da wannan Tahiyar lafazi da ma'ana. Sai ya ce: "(Tsarkakan) Gaisuwa sun tabbata ga Allah": Su ne kowacce magana ko aiki mai shirayrwa akan girmamawa, dukkaninsu ababen cancantane ga Allah - Mai girma da daukaka -. "Salloli": Ita ce sananniyar sallah ta farilla da ta nafila, sun tabbata ga Allah - Madaukakin sarki -. "Tsarkakan Maganganu": Su ne maganganu da ayyuka da siffofi tsarkaka masu nuni akan cika, dukkaninsu ababen cancanta ne ga Allah - Madaukakin sarki -. "Aminci ya tabbata agareka Ya kai wannan Annabi da rahamar Allah da albarkarSa': Addu'ace gare shi da aminta daga dukkanin cututtuka da abin ki, da kari da yawaita a kowanne alheri. "Aminci ya tabbata agaremu da bayin Allah na gari": Addu'ace da aminta daga mai sallah da kuma kowanne bawa na gari a sama da kasa. "Ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah': Wato ina tabbatarwa tabbatarwa a yanke cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. "Kuma cewa Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne": Ina tabbatarwa a gare shi da bauta da Manzanci na karshe. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwadaitar da mai yin sallah ya zabi abinda yaso na addu'a ya roka.
- Bigiren wannan Tahiyar shi ne zama bayan sujjada ta karshe a kowacce sallah, da kuma bayan raka'a ta biyu a sallah mai raka'a uku da mai raka'a hudu.
- Wajabcin gaishe-gaishe a Tahiya, yana halatta ya yi tahiya da kowanne lafazi daga lafazan tahiya daga abinda ya tabbata daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
- Halaccin addu'a da abinda mutum ya so muddin dai ba sabo ba ne.
- An so farawa da kai a cikin addu'a.
صحيح البخاري (8/ 59) (6265). صحيح مسلم (1/ 301) (402). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 168). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص206). خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام، لفيصل آل مبارك (ص94).