Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Na yi sallah tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya kasance yana yin sallama a damansa: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh. "Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa", kuma a hagunsa: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh. "Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah

عَنْ وَائِل بن حُجرٍ رضي الله عنه قَالَ: صَلَّيْتُ مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَكَانَ يُسَلِّمُ عَنْ يَمِينِهِ: «السَّلَامُ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَةُ اللَّهِ وَبَرَكَاتُهُ»، وَعَنْ شِمَالِهِ: «السَّلَامُ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَةُ اللَّهِ».
Daga Wa'il ɗan Hujur - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na yi sallah tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya kasance yana yin sallama a damansa: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh. "Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa", kuma a hagunsa: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh. "Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah".
Abu Dawud ne Ya Rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi

Annabin - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya yi nufin ya juya daga sallarsa zai yi sallama a damansa da hagunsa shi ne ya juyar da fuskarsa ɓangaren dama, tare da faɗinsa: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh. (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa), kuma yana yin sallama a hagunsa, shi ne ya juyar da fuskarsa ɓangaren hagu, tare da faɗinsa: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh. (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah).

Fa’idoji
  1. Halaccin sallama biyu a sallah, kuma ita tana daga rukunanta.
  2. An so zuwa da ƙarin faɗin: (Da albarkarSa), a sashin lokuta; domin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance yana dawwama akanta ba.
  3. Furta sallama biyu a cikin sallah rukuni ne na wajibi, amma yin waiwaye a tsakiyar furta su to (Mustahabbi ne) abin so ne.
  4. Yana kamata ya ce: (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah) a tsakiyar yin waiwaye ba kafinsa ko bayansa ba.
Madogara

سنن أبي داود (2/ 239) (997). المجموع شرح المهذب (مع تكملة السبكي والمطيعي) النووي (3/ 479). المنهاج شرح صحيح مسلم بن الحجاج، النووي (4/ 153). توضيح الأحكام شرح بلوغ المرام، لعبد الله البسام (2/ 291).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
SIFFAR SALLAH

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com