Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Na kasance ina ganin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana yin sallama a damansa da kuma hagunsa, har ina ganin farin kundukukinsa

عَنْ سَعْدٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: كُنْتُ أَرَى رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُسَلِّمُ عَنْ يَمِينِهِ، وَعَنْ يَسَارِهِ، حَتَّى أَرَى بَيَاضَ خَدِّهِ.
Daga Sa'ad - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance ina ganin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana yin sallama a damansa da kuma hagunsa, har ina ganin farin kundukukinsa.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Sa'ad Ibnu Abi Waƙas - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa shi ya kasance yana ganin farin kundukukin (kumatun) Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - saboda tsananin waiwayensa idan zai sallame daga sallarsa a damansa a sallamar farko, haka a hagunsa a (sallama) ta biyu.

Fa’idoji
  1. Halaccin kai matuƙa a cikin waiwaye zuwa ɓangaren dama da kuma ɓangaren hagu.
  2. Halaccin sallama biyu zuwa dama da hagu.
  3. Nawawi ya ce: Da a ce zai yi sallama biyu a damarsa ko a hagunsa ko ta ɓangaren fuskarsa, ko ta farkon a hagunsa, ta biyun kuma a damansa sallarsa ta inganta kuma sallama biyun ta tabbata, sai dai ya rasa falala ta yadda ake yinsu .
Madogara

صحيح مسلم (1/ 409) (582). البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (13/ 99). مرقاة المصابيح شرح مشكاة المصابيح (4 /30).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
SUNNONIN SALLAH

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com