Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Ya ku Mutane babu abunda ya ragu daga cikin Alamomin Annabta sai Kyakkyawan Mafarkin da Musulmi zai ganshi, ko a ganar masa, ku saurara kuma lallai ni ina hana karanta Al-qur'ani a a Ruku'u ko a Sujada

عن ابن عباس -رضي الله عنهما- قال: كَشف رسول الله صلى الله عليه وسلم السِّتَارة والناس صُفوف خَلف أبي بَكر، فقال: «أيها الناس، إنه لم يَبْق من مُبَشِّرَاتِ النُّبُوَّةِ إلا الُّرؤيا الصَّالحة، يَراها المُسلم، أو تُرى له، ألا وإنِّي نُهِيت أن أقْرَأ القرآن راكِعا أو ساجِدا، فأما الرُّكوع فعظِّموا فيه الرَّب عز وجل ، وأما السُّجود فَاجْتَهِدُوا في الدُّعاء، فَقَمِنٌ أن يُستَجاب لكم».
Daga Ibn Abbas -Allah ya yarda da su- ya ce Manzon Allah ya buxe mana labule kuma Mutane sunyi Sahu a bayan Abubakar sai ya ce: "Ya ku Mutane babu abunda ya ragu daga cikin Alamomin Annabta sai Kyakkyawan Mafarkin da Musulmi zai ganshi, ko a ganar masa, ku saurara kuma lallai ni ina hana karanta Al-qur'ani a a Ruku'u ko a Sujada amma a Ruku'u ku girmama Allah kuma a Sujada to kuyi qoqrin Addu'a an kusa a amsa Muku"
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Manzon Allah SAW ya buxe labule da iqanin abunda ya faru, a haqyake qofar Xakinsa da gidan kuma Mutane sunyi sahu bayan Abubakar -Allah ya yarda da shi- suna sallah cikin jam'i,kuma shi bai iya yin Sallah tare da su ba saboda rashin lafiya sai ya Umarci Abubakar da yayi sallah da Mutane, sai ya ce: "yaku mutane cewa shi babu abunda ya ragu na Alamomin Annabta sai kawai Mafarki nagari" to bayan Mutuwar Manzon Allah SAW da yankewar wahayi babu abunda ya Sai kyakkyawan Mafarki ai wanda yake dacewa da abunda ya faru sai ya tiqa dacewa da abunda ya faru sai Masu Imani su gani don suyi Bushara kuma suyi farin ciki da shi, su qara tabbaci kan tabbaci, da kuma kasancewarsa yana daga yankin Annabta; saboda Manzon Allah SAW ya zauna farkon Annabtarsa yana ganin Mafarki sai kuma abun ya faru kamar walqiyar Asuba, saboda haka wani Vangare ne na Annabtar sa -Amincin Allah a gare shi- da kuma faxinsa: "Sai Busharori" yin bayani da Bushara ya rinjayar da mafi yawa, in kuma ba haka ba to ai akwai Mafarkin da jan kunne ne daga allah kuma gaskiya ne da Mu,ini yake gani don sauqaqawa a gare shi, don ya shirya abunda zai faru kafin faruwarsa, kan haka Mafarki ya za,anto kodai bushara ga Mumini ko kuma nusarwa gare shi daga waya Gafala da kuma yace Mumini zai ganshi ko a hanar masa, duk xaya ne Musulmi ne ya gani ko ganar masa akai, faxinsa kuma: "Cewa ni na hana Karanta Qur'ani a Ruku'u ko Sujada" yana nufin cewa Allah SWT ya hana Manzonsa ya karanta Qur'ani a halin Rku'u ko Sujada, kuma duk abunda aka hana SAW wannan yana nufin cewa Al-ummarsa ma tana cikin wannan hanin sai in an smu Dalilin da ya kevance shi SAW wannan idan ya nufi karatu a ruku'un ko sujadar amma idan ya nufi yin Addu'a ne to babu laifi akansa kuma ya zo cikin Hadisi "Kuma kowane Mutum da abunda yayi niyya" hikimar hanin -Allah shi ne Mafi sani- cewa Ruku'u da Sujada sune halin Qasqanta da kuma risinawa, sannan cewa Sujada tana kasancewa a Qasa bata dace da Qur'ani a karanta shi a wannan Yanayin ba kuma faxinsa: "amma a Ruku' ku girmama Allah " ai kuce Tsarki ya tabbata ga Allah mai girma, da makamancinsa na Tasbihai waxanda aka samu daga Suuna, amma faxinsa: "Kuma a cikin Sujada to kuyi qoqarin yin Addu'a" ai ya dace ga Mai Sallah da yawaita Addu'a a lokacin sujada; saboda wuri ne da ake amsa Addua, kuma ya zo a cikin Muslim cewa SAW cewa ya ce: "Mafi kusancin lokacin da Bawa yake kusantar Ubangijinsa shi ne lokacin da yake Sujada , to ku yawaita Addu'a" sai dai haxe da faxin tsarki ya tabbata ga Ubangiji Mafi xaukaka; saboda Wajibi ne kuma faxinsa: " ankusa a amsa muku" ai ana sa ran samun amsar Addu'aku; Saboda shi ne lokaci mafu kusancin bawa da Ubangijinsa a halin yana Sujada, kuma shi ne wurin da ke so ya tsawaita Addu'a da yawaitawa, idan Mutum ya kasance

Madogara

صحيح مسلم، تأليف: مسلم بن الحجاج النيسابوري، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي الناشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت. معالم السنن، تأليف: حمد بن محمد بن إبراهيم الخطابي، الناشر: المطبعة العلمية، الطبعة: الأولى 1351هـ. إكمال المعلم بفوائد مسلم، تأليف: عياض بن موسى بن عياض، تحقيق: د/ يحي بن اسماعيل، الناشر: دار الوفاء للطباعة والنشر والتوزيع، الطبعة: الأولى، 1419هـ. المنهاج شرح صحيح مسلم، تأليف: محيي الدين يحيى بن شرف النووي، الناشر: دار إحياء التراث العربي، الطبعة: الثانية 1392هـ. الفتاوى الكبرى لابن تيمية، تأليف: تقي الدين أبو العباس أحمد ابن تيمية، الناشر: دار الكتب العلمية الطبعة: الأولى، 1408هـ - 1987م. مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، تأليف: علي بن سلطان القاري، الناشر: دار الفكر، الطبعة: الأولى، 1422هـ. التيسير بشرح الجامع الصغير، تأليف: محمد عبد الرؤوف بن زين العابدين المناوي، الناشر: مكتبة الإمام الشافعي، الطبعة: الثالثة، 1408هـ - 1988م. سبل السلام شرح بلوغ المرام، تأليف: محمد بن إسماعيل بن صلاح الصنعاني، الناشر: دار الحديث الطبعة: بدون طبعة وبدون تاريخ. توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، تأليف: عبد الله بن عبد الرحمن بن صالح البسام، الناشر: مكتبة الأسدي، مكة المكرّمة الطبعة: الخامِسَة، 1423 هـ - 2003 م. تسهيل الإلمام بفقه الأحاديث من بلوغ المرام، تأليف: صالح بن فوزان بن عبد الله الفوزان، الطبعة: الأولى، 1427 هـ _ 2006 م. فتح ذي الجلال والإكرام، شرح بلوغ المرام، تأليف: محمد بن صالح بن محمد العثيمين، الناشر: المكتبة الإسلامية، تحقيق: صبحي بن محمد رمضان، وأُم إسراء بنت عرفة.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
SUNNONIN SALLAH

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com