Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana faɗa a tsakanin sujjada biyu; "Ya Ubangiji ka gafarta min, ka yi min rahama, ka ba ni lafiya, ka shiryar da ni, ka azurta ni

عن ابن عباس رضي الله عنهما: كان النبي صلى الله عليه وسلم يقول بين السجدتين: «اللَّهمَّ اغْفِرْ لي، وارْحَمْنِي، وعافِني، واهْدِني، وارزقْنِي».
Daga Ɗan Abbas Allah Ya yarda da su: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana faɗa a tsakanin sujjada biyu; "Ya Ubangiji ka gafarta min, ka yi min rahama, ka ba ni lafiya, ka shiryar da ni, ka azurta ni.
Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shiDarajaHasan ne a baki dayan Riwayoyin sa
Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya kasance yana yin Addu’a tsakanin sujjada biyu a Sallarsa, da waɗannan addu’o’in biyar, wacce Musulmi yake da matuƙar buƙatar su, kuma sun ƙunshi alheran duniya da lahira, kamar neman gafara, da ɓoye zunubi, da kuma yafe su, da malalo rahama da waraka daga shubuhohi da abubuwan sha’awe-sha’awe da rashin lafiya da cututtuka , da kuma roƙon Allah samun shiriya a kan gaskiya da kuma tabbata a kanta, da arziki na imani da ilimi da aiki na ƙwarai da kuma dukiya ta halal mai daɗi.

Fa’idoji
  1. Shar’antuwar wannan Addu’ar a zaman dake tsakanin sujjada biyu.
  2. Falalar wannan Addu’ar saboda abin da ta ƙunsa na alheran duniya da lahira.
Madogara

سنن أبي داود (2/ 138) (850). سنن الترمذي (1/ 317) (284). سنن ابن ماجه (2/ 64) (898). مسند أحمد (5/ 72) (2895). مشكاة المصابيح، للتبريزي (1/ 283). سبل السلام شرح بلوغ المرام، لمحمد الصنعاني (1/ 274). توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، لعبد الله البسام (2/ 240).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
SIFFAR SALLAH

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com