Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Mafi munin mutane sata shi ne wanda yake satar sallarsa" sai ya ce: Ta yaya zai saci sallarsa? sai ya ce: "Ya zamo ba ya cika ruku'unta, ba ya cika sujjadarta

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَسْوَأُ النَّاسِ سَرَقَةً الَّذِي يَسْرِقُ صَلَاتَهُ» قَالَ: وَكَيْفَ يَسْرِقُ صَلَاتَهُ؟ قال: «لَا يُتِمُّ رُكُوعَهَا، وَلَا سُجُودَهَا».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mafi munin mutane sata shi ne wanda yake satar sallarsa" sai ya ce: Ta yaya zai saci sallarsa? sai ya ce: "Ya zamo ba ya cika ruku'unta, ba ya cika sujjadarta".
Ibnu Hibban ne ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa mafi tsananin mutane muni a sata shi ne wanda yake satar sallarsa; hakan ya kasance ne domin karɓar dukiyar wani wataƙila zai iya amfani da ita a duniya, saɓanin wannan satar, domin ya saci haƙƙin kansa na sakamako da lada, suka ce: Ya Manzon Allah, ta yaya zai saci sallarsa? sai ya ce: Ba ya cika ruku'unta kuma ba ya cika sujjadarta; hakan yana nufin ya yi gaggwa a ruku'u da sujjada, ba zai zo da su ba a kan cikkakkiyar fuskar su ba.

Fa’idoji
  1. Muhimmancin kyautata sallah da zuwa da rukunanta da nutsuwa da ƙanƙar da kai.
  2. Siffanta wanda ba ya cika ruku'unsa da sujjadarsa da cewa shi ɓarawo ne; kyamatar hakan ne gami da faɗakarwa a kan haramcinsa.
  3. Wajabcin cika ruku'u da sujjada a sallah da daidaito a cikinsu.
Madogara

صحيح ابن حبان (5/ 209) (1888)، الشّافي في شرح مسند الشّافعي (1/613)، الكاشف عن حقائق السنن (3/1020)، التنوير (2/373)، نيل الأوطار (2/ 311).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
Rukunan Sallah

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com