عَنِ ابْنِ عُمَرَ رَضيَ اللهُ عنهما قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِذَا جَمَعَ اللهُ الْأَوَّلِينَ وَالْآخِرِينَ يَوْمَ الْقِيَامَةِ يُرْفَعُ لِكُلِّ غَادِرٍ لِوَاءٌ، فَقِيلَ: هَذِهِ غَدْرَةُ فُلَانِ بْنِ فُلَانٍ».
Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan Allah Ya tara mutanen farko da na ƙarshe ranar alƙiyama za'a ɗaga tuta ta dukkan wani mayaufdari, sai a ce: Wannan yaudarar wane ɗan wane ce".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - idan ya tara mutanen farko dana ƙarshe ranar alƙiyama saboda hisabi, za'a kafawa kowanne maha'incin da bai cika alƙawarin da ya dauka ba tare da Allah ko tare da mutane ba, wata alamar da za'a kunya shi da ita akan ha'incinsa, kuma za’a yi kira akan sa a wannan ranar: Wannan ha'incin wane ɗan wane ne; dan bayyanar da mummunan aikinsa a filin taron alƙiyama.
Fa’idoji
- Haramta yaudara kuma cewa ita tana daga cikin manyan zunubai; domin a cikinta ne wannan narkon mai tsanani yake.
- Yaudarar da aka yi narko a kanta ta ƙunshi dukkan wanda ya amince maka akan jini, ko mutunci, ko sirri, ko dukiya sai ka ha'ince shi, ka kuma saɓawa zatinsa a cikin amanarka.
- AlƘurɗubi ya ce: wannan magana ce daga gare shi zuwa ga larabawa da irin abinda suke aikatawa; domin su sun kasance suna ɗaga farar tuta dan cika alƙawari, suna ɗaga baƙar tuta kuma dan yaudara, dan su zargi mayaudari, sai Hadisin ya hukunta afkuwar irin haka ga mayaudari; dan ya shahara da siffarsa a taron alƙiyama, kuma al’umma da suke a filin alƙiyama su zarge shi.
- Ibnu Hajar ya ce: Kuma a cikinsa mutane za'a kirasu ranar alƙiyama (tare da sunayen) iyayen su; saboda faɗinsa: "Wannan ce yaudarar wane ɗan wane".
Madogara
صحيح البخاري (4/ 104) (3188)
صحيح مسلم (3/ 1359) (1735).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص745).
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (2/ 188).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي بكرة رضي الله عنه قال: قال النبي صلى الله عليه وسلم: «أَلَا أُنَبِّئُكُمْ بِأَكْبَرِ الْكَبَائِرِ؟» ثَلَاثًا، قَالُوا: بَلَى يَا رَسُولَ اللهِ، قَالَ: «الْإِشْرَاكُ بِاللهِ، وَعُقُوقُ الْوَالِدَيْنِ» وَجَلَسَ وَكَانَ مُتَّكِئًا، فَقَالَ: «أَلَا وَقَوْلُ الزُّورِ»، قَالَ: فَمَا زَالَ يُكَرِّرُهَا حَتَّى قُلْنَا: لَيْتَهُ سَكَتَ.
Daga Abu bakrata - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Shin ba na ba ku labarin mafi girman zunubai ba?" sau uku, suka ce: na'am ya Manzon Allah, ya ce: "Yi wa Allah shirka, da saɓawa iyaye" sai ya zauna alhali ya kasance a kishingiɗe, sai ya ce: "Ku saurara da faɗar zur" ya ce: Bai gushe ba yana maimaitata har sai da muka ce: Ina ma dai ya yi shiru.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba wa sahabbansa labari game da mafi girman zunubai, sai ya ambaci waɗannan ukun:
1. Yi wa Allah shirka: Shi ne juyar da kowanne nau'in ibada ga wanin Allah, da daidaita wanin Allah da Allah a AllantakarSa da UbangidantakarSa da sunayenSa da siffofinSa.
2. Saɓawa iyaye: Shi ne kowacce irin cutarwa ga iyayen, magana ce ko aiki, da barin kyautatawa musu.
3. Faɗin zur, shaidar zur tana daga ciki: Shi ne dukkanin maganar da take ƙarya ce da aka yi nufin tauye wanda ta faɗa kansa ta hanyar ƙwace dukiyarsa da keta mutuncinsa, ko makamancin hakan.
Haƙiƙa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya maimaita gargaɗi game da faɗin zur don faɗakarwa a kan muninta da mummunan gurbinta ga zamntakewa, har sai da sahabbansa suka ce: Ina ma dai ya yi shiru don tausaya masa, da kuma ƙin abin da zai tayar masa da hankali.
Fa’idoji
- Mafi girman zunubai shi ne yi wa Allah shirka; domin haka ya sanya shi farkon zunubai, kuma mafi girmansu, faɗinSa - maɗaukakin sarki yana ƙarfafa wannan: {Lallai Allah ba Ya gafartawa a yi shirka da shi, Yana gafarta koma bayan hakan ga wanda Ya so}.
- Girman haƙƙoƙin mahaifa, don Ya gwama haƙƙinsu da haƙƙin Allah - Maɗaukakin sarki -.
- Zunubai sun kasu zuwa manya da ƙanana, babban laifi shi ne: Dukkanin laifin da a cikinsa akwai uƙuba ta duniya, kamar haddodi da tsinuwa, ko narko na lahira, kamar narkon shiga wuta, kuma manyan zunubai hawa-hawa ne wasunsu sun fi wasu muni a haramci, ƙananan zunubai kuma su ne waɗanda ba wadannan ba.
Madogara
صحيح البخاري (3/ 172) (2654)، (8/ 4) (5976)، (8/ 62) (6273-6274).
صحيح مسلم (1/ 91) (87).
عمدة الأحكام من كلام خير الأنام صلى الله عليه وسلم (ص257) (380).
شرح النووي على مسلم (2/ 81).
الإلمام بشرح عمدة الأحكام لإسماعيل الأنصاري (2/ 149).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام للبسام (ص703).
أعلام السنة المنشورة لاعتقاد الطائفة الناجية المنصورة، لحافظ بن أحمد الحكمي (ص111).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما قَالَ: مَرَّ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بِقَبْرَيْنِ، فَقَالَ: «إِنَّهُمَا لَيُعَذَّبَانِ، وَمَا يُعَذَّبَانِ فِي كَبِيرٍ، أَمَّا أَحَدُهُمَا فَكَانَ لاَ يَسْتَتِرُ مِنَ البَوْلِ، وَأَمَّا الآخَرُ فَكَانَ يَمْشِي بِالنَّمِيمَةِ» ثُمَّ أَخَذَ جَرِيدَةً رَطْبَةً، فَشَقَّهَا نِصْفَيْنِ، فَغَرَزَ فِي كُلِّ قَبْرٍ وَاحِدَةً، قَالُوا: يَا رَسُولَ اللَّهِ، لِمَ فَعَلْتَ هَذَا؟ قَالَ: «لَعَلَّهُ يُخَفِّفُ عَنْهُمَا مَا لَمْ يَيْبَسَا».
Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wuce wasu kaburbura biyu, sai ya ce: "Lallai su ana musu azaba, kuma ba’a yi musu azaba dan wani babban laifi ba, amma dayansu ya kasance ba ya suturta daga fitsari, amma dayan ya kasance yana tafiya da annamimanci" Sannan ya dauki wani danyan itacan dabino, sai ya raba shi biyu, sai ya kafa daya a kowanne kabari, suka ce: Ya Manzon Allah, meyasa ka aikata hakan, sai ya ce: "Watakila a saukaka musu muddin dai basu bushe ba".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wuce wasu kaburbura biyu sai ya ce: Lallai masu kaburburan nan biyu ana musu azaba; kuma ba'a yi musu azaba dan wani babban laifi ku a ganinku ba, duk da yake mai girma ne a wurin Allah, amma dayansu ya kasance ba ya himmantuwa da kiyaye jikinsa da tufafinsa daga fitsari har sai ya biya bukatarsa, dayan kuma ya kasance yana tafiya da annamimanci a tsakanin mutane, sai ya dakko zancen wani da nufin cutarwa da sanya sabani da fitina a tsakanin mutane.
Fa’idoji
- annamimanci da barin tsarkaka daga fitsari yana daga manyan zunubai kuma daga sabubban azabar kabari.
- Allah - tsarki ya tabbatar maSa - ya yaye wasu sashin gaibu - kamar azabar kabari - dan bayyanar da alamar Annabinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
- Wannan aikin na tsaga itacan dabino da sanya shi akan kabari ya kebanci Annabi ne - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ; domin Allah Ya tsinkayar da shi akan halin masu kabarin su biyun, ba za’a kiyasta waninsa da shi ba domin babu wani da yasan halayen ma'abota kaburbura.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 53) (218).
صحيح مسلم (1/ 240) (292).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص43).
خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام، لفيصل آل مبارك (ص22).
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 29).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي هريرة رضي الله عنه مرفوعاً: «أتدرون من المفلس؟» قالوا: المُفْلِس فينا من لا دِرهَمَ له ولا مَتَاع، فقال: «إن المفلس من أمتي من يأتي يوم القيامة بصلاة وصيام وزكاة، ويأتي وقد شَتَمَ هذا، وقذف هذا، وأكل مال هذا، وسَفَكَ دم هذا، وضرب هذا، فيعطى هذا من حسناته، وهذا من حسناته، فإن فنيت حسناته قبل أن يُقْضَى ما عليه، أخذ من خطاياهم فَطُرِحتْ عليه، ثم طُرِحَ في النار».
Daga Abu Hurairah, yardar Allah ta tabbata a gare shi, tare da rahoto kan mai zuwa: “Shin kun san wanda ya bankare?” Suka ce: Fatara tana daga cikinmu wanda ba shi da kudi ko kaya, sai ya ce: “Fatarar daga al’ummata ita ce wani wanda ya zo ranar tashin kiyama da salla, da azumi da zakka, sai ya zo aka zagi wannan, wannan kuma aka jefa shi, kuma ya cinye wannan kudin, kuma wannan jini ya zube, kuma wannan an buge shi, kuma ana bayar da wannan ne daga kyawawan ayyukansa. Wannan yana daga cikin kyawawan ayyukansa. Idan kyawawan ayyukansa suka baci kafin a biya shi hakinsa, zai dauke zunubansu sai a jefa shi, sa'annan a jefa shi cikin Wuta. ”
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Manzon Allah SAW yana tambayar Sahabbai amincin Allah a gare su sai ya ce: lp limsam wanda yafo kowa Talaucewa? sai suka basjo labarin abunda suka sani a Al-adance, sai suka ce: shi ne talakan bashi da ko sisi kuma bashi da Kadara, sai ya basu labarin cewa Matsiyaci a cikin wannan Al-ummar shi ne wanda yazo Ranar Alkiyama da kyawawan Ayyuka Manya, da kuma kyawawan Ayyuka Masu yawa na Sallah da Azumi da zakka sai ya zo amma ya Zagi wannan kuma ya daki wancan, kuma ya cinye kuxin wancan kuma ya jefi wancan ya zubar da jinin wancan, kuma ga Mutane suna son karbar haqqinsu, saboda abunda basu iya karvarsa a Duniya ba zasu karveshi a Lahira, sai a xaukar musu fansa sai a xauka daga ladan ayyukansa a bawa wannan ladansa kuma wannan ma a biyashi da ladansa da Adalci da kisasi na gaskiya, idan suka qare ayyukansa na Alkairin sai a xauki Zunubansu sai a lafta masa su, sannan a jefashi cikin Wuta
Madogara
- رياض الصالحين من كلام سيد المرسلين؛ للإمام أبي زكريا النووي، تحقيق د. ماهر الفحل، دار ابن كثير-دمشق، الطبعة الأولى، 1428ه .
- بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين؛ تأليف سليم الهلالي، دار ابن الجوزي- الطبعة الأولى1418ه
- نزهة المتقين شرح رياض الصالحين؛ تأليف د. مصطفى الخِن وغيره، مؤسسة الرسالة-بيروت، الطبعة الرابعة عشر، 1407هـ.
- صحيح مسلم؛ للإمام مسلم بن الحجاج، حققه ورقمه محمد فؤاد عبد الباقي، دار عالم الكتب-الرياض، الطبعة الأولى، 1417هـ.
- شرح رياض الصالحين؛ للشيخ محمد بن صالح العثيمين، مدار الوطن، الرياض، 1426هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي هريرة رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «اجْتَنِبُوا السَّبْعَ الْمُوبِقَاتِ»، قَالُوا: يَا رَسُولَ اللهِ وَمَا هُنَّ؟ قَالَ: «الشِّرْكُ بِاللهِ، وَالسِّحْرُ، وَقَتْلُ النَّفْسِ الَّتِي حَرَّمَ اللهُ إِلَّا بِالْحَقِّ، وَأَكْلُ الرِّبَا، وَأَكْلُ مَالِ الْيَتِيمِ، وَالتَّوَلِّي يَوْمَ الزَّحْفِ، وَقَذْفُ الْمُحْصَنَاتِ الْمُؤْمِنَاتِ الْغَافِلَاتِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: ((Ku nisanci abubuwa bakwai masu halakarwa)) suka ce: Ya Manzon Allah, wadanne ne su? Ya ce: “Shirka da Allah, da sihiri, da kashe rai wacce Allah Ya haramta sai da gaskiya, da cin riba, da cin dukiyar maraya, da juya baya ranar yaki, da yiwa mumina katangaggiya rafkananniya kazafi".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana umartar al'ummarsa da nisantar laifuka da sabo guda bakwai masu halakarwa, yayin da aka tambaye shi game da su wadanne ne su? sai ya bayyana su da cewa su ne:
Na farko: Shirka da Allah, ta hanyar rikon kishiya da tamka gare Shi - tsarki ya tabbatar maSa - daga dukkanin wani zance da ya kasance, da kuma juyar da kowace irin ibada daga ibadu ga wanin Allah - Madaukakin sarki - kuma ya fara da shirka; domin cewa ita ce mafi girman zunubai.
Na biyu: Sihiri - shi ne wani na daga kullace-kullace da wasu magunguna da hayake-hayake -, yanayin tasiri a cikin jikin wanda aka yi wa sihirin ta hanyar kisa ko rashin lafiya, ko ya raba tsakanin ma'aurata biyu, shi aiki ne na Shaidan, kuma da yawa daga gare shi ba'a kaiwa zuwa gareshi sai ta hanyar shirka da neman kusanci zuwa ga munanan ayyuka da wani abin da suke so.
Na uku: Kashe ran da Allah Ya hana kashe ta ba da wani abinda ya halatta a shari'ance wanda shugaba zai zartar dashi.
Na hudu: Amfani da riba ta hanyar ci ko waninsa ta fuskokin amfani.
Na biyar: Barna akan dukiyar karamin yaron da babansa ya mutu alhali shi bai kai shekarun balaga ba.
Na shida: Guduwa daga yaki da ake yi da kafirai.
Na bakwai: Tuhumar 'ya'ya mata kamammu da zina, haka nan ma tuhumar maza.
Fa’idoji
- Lallai cewa manyan zunubai ba su takaitaba a guda bakwai ba, kuma kebance wadannan bakwan dan girmansu ne da kuma hadarinsu.
- Halaccin kashe rai idan ya kasance da hakki ne kamar kisasi da ridda da zina bayan katangantuwa, kuma shugaba na shari'a shi ne yake zartar da shi.
Madogara
صحيح البخاري (4/ 10) (2766).
صحيح مسلم (1/ 92) (89).
شرح صحيح البخارى لابن بطال (8/ 489).
الملخص في شرح كتاب التوحيد، للشيخ صالح الفوزان (ص201).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ سُلَيْمَانَ بْنِ صُرَدٍ رضي الله عنه قَالَ: كُنْتُ جَالِسًا مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَرَجُلاَنِ يَسْتَبَّانِ، فَأَحَدُهُمَا احْمَرَّ وَجْهُهُ، وَانْتَفَخَتْ أَوْدَاجُهُ، فَقَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِنِّي لَأَعْلَمُ كَلِمَةً لَوْ قَالَهَا ذَهَبَ عَنْهُ مَا يَجِدُ، لَوْ قَالَ: أَعُوذُ بِاللَّهِ مِنَ الشَّيْطَانِ، ذَهَبَ عَنْهُ مَا يَجِدُ» فَقَالُوا لَهُ: إِنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «تَعَوَّذْ بِاللَّهِ مِنَ الشَّيْطَانِ»، فَقَالَ: وَهَلْ بِي جُنُونٌ؟
Daga Salaiman Bin Surad - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance ina zaune tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali wasu mutane biyu suna zage-zage, ɗayansu fuskarsa ta yi jā, jijiyoyinsa sun buɗe, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: 'Lallai Ni na san wata kalmar da zai faɗeta da abinda yake ji ya tafi daga gare shi, da zaice: Ina neman tsarin Allah daga Shaiɗan, abinda yake ji zai tafi" sai suka ce masa: Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ka nemi tsarin Allah daga Shaiɗan", sai ya ce: Shin ni ina da hauka ne?
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
wasu mutane biyu sun yi zage-zage a gaban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, alhali fuskar ɗayansu ta yi jā, jijiyoyinsa da suka kewaye wuyansa sun kunbura.
Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Lallai ni na san kalmar da wannan mai fushin zai faɗeta da fushin ya tafi daga gare shi, da zai ce: Ina neman tsarin Allah daga Shaiɗan abin jefewa.
Sai suka ce masa: Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ka nemi tsarin Allah daga Shaiɗan.
Sai ya ce: Shin ni mahaukaci ne? ya yi zatan cewa ba mai neman tsari daga Shaiɗan sai wanda yake da hauka.
Fa’idoji
- Kwaɗayin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan shiryarwa da fadakarwa a yayin samuwar sababinsa.
- Fushi daga Shaiɗan ne.
- Umarni da neman tsarin Allah daga Shaɗan abin jefewa a yayin fushi, Allah Maɗaukakin sarki Ya ce: {Idan fuzga daga Shaiɗan ta fuzgeka to ka nemi tsarin Allah..} Aya.
- Gargaɗi akan zagi da abinda ke kama da shi na tsinuwa, da kuma nisanta daga garesu; domin su suna kaiwa zuwa ɓarna tsakanin mutane.
- Kawo nasiha ga wanda bai ji ta ba dan ya anfana da abinda ke cikinta.
- Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsoratar daga fushi; domin cewa shi yana kaiwa zuwa sharri da rashin tinani, tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya kasance ba ya fushi sai dai idan an keta alfarmar Allah - Maɗaukakin sarki -, shi ne fushi abin yabo.
- AlNawawi ya faɗa akan faɗinsa: "Shin kana ganin ni ina da hauka ne": Zai yiwu cewa wannan mai maganar ya kasance yana daga munafukai, ko daga larabawan ƙauye masu wauta.
Madogara
صحيح البخاري (4/ 124) (3282).
صحيح مسلم (4/ 2015) (2610).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 110).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص50).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (1/ 270).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 78).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن وَاثِلَةَ بن الأَسْقَعِ ـ رضي الله عنه ـ مرفوعاً: «إن من أعظم الفِرَى أن يَدَّعِيَ الرجلُ إلى غير أبيه، أو يُرِي عَيْنَهُ ما لم تَرَ، أو يقول على رسول الله صلى الله عليه وسلم ما لم يَقْلْ».
Daga Athilah Ibn Al-Asqa '- yardar Allah ta tabbata a gare shi - da isnadi: "Daya daga cikin mafi girman dalilai shi ne mutum ya yi addu'a ga wanin mahaifinsa, ko ya gani da idanunsa abin da ba ku gani ba, ko kuma ya ce wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - abin da bai fada ba".
Buhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara
- صحيح البخاري، للإمام محمد بن إسماعيل البخاري، تحقيق محمد الناصر، دار طوق النجاة.
- بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين؛ تأليف سليم الهلالي، دار ابن الجوزي- الطبعة الأولى1418ه.
- نزهة المتقين شرح رياض الصالحين؛ تأليف د. مصطفى الخِن وغيره، مؤسسة الرسالة-بيروت، الطبعة الرابعة عشرة، 1407هـ.
- كنوز رياض الصالحين»، لحمد بن ناصر العمار، دار كنوز إشبيليا- الطبعة الأولى1430ه.
- دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين، لمحمد علي بن محمد بن علان بن إبراهيم البكري الصديقي الشافعي اعتنى بها: خليل مأمون شيحا، دار المعرفة .
- شرح رياض الصالحين؛ للشيخ محمد بن صالح العثيمين، مدار الوطن، الرياض، 1426هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المؤْمنينَ رَضيَ اللهُ عنها قَالَت: قُلْتُ لِلنَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: حَسْبُكَ مِنْ صَفِيَّةَ كَذَا وَكَذَا، -قَالَ أَحدُ الرُّوَاةِ: تَعْنِي قَصِيرَةً- فَقَالَ: «لَقَدْ قُلْتِ كَلِمَةً لَوْ مُزِجَتْ بِمَاءِ الْبَحْرِ لَمَزَجَتْهُ» قَالَتْ: وَحَكَيْتُ لَهُ إِنْسَانًا، فَقَالَ: «مَا أُحِبُّ أَنِّي حَكَيْتُ إِنْسَانًا وَأَنَّ لِي كَذَا وَكَذَا».
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ya isheka abu kaza da abu kaza daga Safiyya, - wani daga maruwaita ya ce: Tana nufin cewa ita gajera ce - sai ya ce: «Haƙiƙa kin faɗi kalmar da za'a cakuɗata da ruwan kogi da ta canza shi» ta ce: Kuma na kwaikwayi wani mutum gare shi , sai ya ce: «Bana son ace na kwaikwayi wani mutum koda kuwa (na karɓi) abu kaza da abu kaza».
Abu Daud ne ya ruwaito shi da Kuma Tirmizi da AhmadDarajaIngantacce ne
Sharhi
Nana Aisha Uwar muminai A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ya isheka daga Safiyya - tana nufin Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - cewa daga cikin aibukanta na jiki ita gajera ce, sai ya ce: Haƙiƙa kin faɗi kalmar da da za'a cakuɗata da ruwan kogi da ta rinjaye shi ta canjashi ta kuma ɓata shi, ta ce: Kuma na aikata irin aikin wani mutum dan ɓata shi, sai Annabi - tsira da amincin Allsh su tabbata agare shi - ya ce: In ya faɗi aibinsa ba ya faranta mini rai, ko in kwaikwaye shi in aikata irin aikinsa ko in faɗi irin maganarsa ta fuskar tauyewa ko da kuwa an bani wani abu mai yawa na duniya akan haka.
Fa’idoji
- Gargaɗarwa da kuma tsoratarwa daga yi da mutum.
- Kwaikwayar yanayi da kwaikwayon mutane ta hanyar wulaƙantarwa da tauyewa yana daga yi da mutum wanda yake haramun ne.
- Siffanta aibuka na jiki wani yanki ne na yi da mutum.
- Alƙali ya ce: al-Mazju shi ne cakuɗawa da kuma canjawa ta hanyar cakuɗa waninsa da shi, ma'ana cewa wannan gibar da ace ta zama daga abinda za'a cakuɗa da ruwan kogi da ta canja shi daga yadda yake, duk da yawansa, to yaya kuwa da ace ayyuka ne kaɗan suka cakuɗa da shi.
- Bayanin abin da yake faruwa tsakanin ma'aurata na kishi.
- Rashin tabbatarwarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga wani aiki abin ƙi.
- Wulaƙantar da sha'anin duniya da abinda ke cikinta idan an haɗa da yardar Allah - Maɗaukakin sarki - da kuma rashin fushinSa.
- Musulunci Addini ne na ɗabi'u masu kyau, haƙiƙa an yi umarni da kiyaye mutunci kada a keta shi da magana ne ko da aiki; domin cewa shi yana daga abinda yake gadar da gaba da ƙiyayya tsakaknin musulmai.
Madogara
سنن أبي داود (7/ 237) (4875).
سنن الترمذي (4/ 275) (2502).
مسند أحمد (41/ 433) (24964).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (3/ 25).
مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، للقاري (7/ 3046).
التيسير بشرح الجامع الصغير، للمناوي (2/ 339).
فيض القدير شرح الجامع الصغير، للمناوي (5/ 411).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com