Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Lallai su ana musu azaba, kuma ba’a yi musu azaba dan wani babban laifi ba, amma dayansu ya kasance ba ya suturta daga fitsari, amma dayan ya kasance yana tafiya da annamimanci

عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما قَالَ: مَرَّ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بِقَبْرَيْنِ، فَقَالَ: «إِنَّهُمَا لَيُعَذَّبَانِ، وَمَا يُعَذَّبَانِ فِي كَبِيرٍ، أَمَّا أَحَدُهُمَا فَكَانَ لاَ يَسْتَتِرُ مِنَ البَوْلِ، وَأَمَّا الآخَرُ فَكَانَ يَمْشِي بِالنَّمِيمَةِ» ثُمَّ أَخَذَ جَرِيدَةً رَطْبَةً، فَشَقَّهَا نِصْفَيْنِ، فَغَرَزَ فِي كُلِّ قَبْرٍ وَاحِدَةً، قَالُوا: يَا رَسُولَ اللَّهِ، لِمَ فَعَلْتَ هَذَا؟ قَالَ: «لَعَلَّهُ يُخَفِّفُ عَنْهُمَا مَا لَمْ يَيْبَسَا».
Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wuce wasu kaburbura biyu, sai ya ce: "Lallai su ana musu azaba, kuma ba’a yi musu azaba dan wani babban laifi ba, amma dayansu ya kasance ba ya suturta daga fitsari, amma dayan ya kasance yana tafiya da annamimanci" Sannan ya dauki wani danyan itacan dabino, sai ya raba shi biyu, sai ya kafa daya a kowanne kabari, suka ce: Ya Manzon Allah, meyasa ka aikata hakan, sai ya ce: "Watakila a saukaka musu muddin dai basu bushe ba".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wuce wasu kaburbura biyu sai ya ce: Lallai masu kaburburan nan biyu ana musu azaba; kuma ba'a yi musu azaba dan wani babban laifi ku a ganinku ba, duk da yake mai girma ne a wurin Allah, amma dayansu ya kasance ba ya himmantuwa da kiyaye jikinsa da tufafinsa daga fitsari har sai ya biya bukatarsa, dayan kuma ya kasance yana tafiya da annamimanci a tsakanin mutane, sai ya dakko zancen wani da nufin cutarwa da sanya sabani da fitina a tsakanin mutane.

Fa’idoji
  1. annamimanci da barin tsarkaka daga fitsari yana daga manyan zunubai kuma daga sabubban azabar kabari.
  2. Allah - tsarki ya tabbatar maSa - ya yaye wasu sashin gaibu - kamar azabar kabari - dan bayyanar da alamar Annabinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  3. Wannan aikin na tsaga itacan dabino da sanya shi akan kabari ya kebanci Annabi ne - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ; domin Allah Ya tsinkayar da shi akan halin masu kabarin su biyun, ba za’a kiyasta waninsa da shi ba domin babu wani da yasan halayen ma'abota kaburbura.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 53) (218). صحيح مسلم (1/ 240) (292). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص43). خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام، لفيصل آل مبارك (ص22). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 29).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
RAYUWAR BARZAHU

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com