Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Da a ce ɗan Adam yana da kwari biyu na dukiya da sai ya nemi wani kwarin na uku, babu abinda yake cika cikin ɗan Adam sai ƙasa, kuma Allah Yana karɓar tuban wanda ya tuba».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa da a ce ɗan Adam zai samu wani kwari cike da zinari, da zai so saboda kwaɗayinsa wanda shi ne ɗabi'arsa ta zama yana da wasu kwari biyun daban, kuma cewa shi ba zai gushe ba yana kwaɗayi akan duniya har sai ya mutu cikinsa ya cika da ƙasar ƙabarinsa.
Fa’idoji
Tsananin kwaɗayin mutum akan tara dukiya da waninta na kayan jin daɗin rayuwar duniya.
Nawawi ya ce: A cikinsa akwai zargin kwaɗayi akan duniya da kuma son tara dukiya a cikinta da kuma kwaɗayinta.
Allah - Maɗaukakin sarki - Yana karɓar tuban wanda ya tuba daga siffofi ababan zargi.
Nawai ya ce: Hadisin ya zo ne akan hukuncin mafi yawancin mutane a kan kwaɗayin duniya, kuma faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: (Allah Yana karɓar tuban wanda ya tuba) yana ƙarfafarsa.
Madogara
صحيح البخاري (8/ 93) (6439).
صحيح مسلم (2/ 725) (1048).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 54).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 76).
المعجم الوسيط، (1/ 148).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com