Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Ku ji tsoron zalunci, domin zalunci duhu ne ranar Alkiyama, Ku ji tsoron kwauro, domin kwauro shi ne ya hallaka wadanda suka gabaceku,

عَنْ جَابِرِ بْنِ عَبْدِ اللهِ رضي الله عنهما أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «اتَّقُوا الظُّلْمَ، فَإِنَّ الظُّلْمَ ظُلُمَاتٌ يَوْمَ الْقِيَامَةِ، وَاتَّقُوا الشُّحَّ، فَإِنَّ الشُّحَّ أَهْلَكَ مَنْ كَانَ قَبْلَكُمْ، حَمَلَهُمْ عَلَى أَنْ سَفَكُوا دِمَاءَهُمْ وَاسْتَحَلُّوا مَحَارِمَهُمْ».
Daga Jabir Dan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ku ji tsoron zalunci, domin zalunci duhu ne ranar Alkiyama, Ku ji tsoron kwauro, domin kwauro shi ne ya hallaka wadanda suka gabaceku, har ya kaisu sun zubar da jininsu, suka halarta abinda aka haramta musu".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargadi daga zalinci. Daga cikin Nau’ukansa akwai: Zalintar mutane da zalintar kai, da zalinci a hakkin Allah - Madakakin sarki -, Shi ne kin baiwa dukkanin mai hakki hakkinsa, kuma zalinci duffai ne ga ma'abotansa a ranar Alkiyama daga faruwar tsanani da tsorace-tsorace, kuma ya yi hani daga kwauro, da shi ne tsananin rowa tare da kwadayi, daga gareshi akwai takaitawa a bada hakkokin dukiya da tsananin kwadayi akan duniya, wannan nau'in na zalinci shi ne ya halakar da wanda suka gabacemu na al'ummai, ta inda ya ja su ga kashe sashinsu, da halarta abinda Allah Ya haramta na abubuwan haram.

Fa’idoji
  1. Bada dukiya da taimakawa 'yan uwa yana daga sabubban soyayya da sada (zumunci).
  2. Rowa da kwauro suna kaiwa zuwa ga sabo da alfasha da zunubai.
  3. Izina da halayen al'ummun da suka gabata.
Madogara

صحيح مسلم (4/ 1996) (2578). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، مجموعة من الباحثين (1/ 484). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 614).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALOLI DA LADUBBA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com