Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanda ya nemi sanin ilimin shari'a wanda asali a cikinsa shi ne a nufi yardar Allah - Maɗaukakin sarki - da shi ba ya nemansa ba ne kawai sai dan ya samu wani rabo da wani jin daɗi na duniya da shi na dukiya ko alfarma to ba zai ji ƙanshin aljanna ba a ranar alƙiyama.
- Wajabcin ikhlasi a cikin neman ilimi, da kuma kwaɗaitarwa akan hakan.
- Gargaɗarwa mai tsanani daga riƙo da ilimin shari'a saboda riya ko abin neman duniya, kuma cewa hakan yana daga cikin manyan zunubai.
- Cewa wanda ya nemi ilimi saboda Allah - Maɗaukakin sarki - sai duniya ta zo masa dan bi to ya halatta ya karɓeta, hakan ba zai cutar da shi ba.
- Sindi ya ce: Faɗinsa (ƙanshin aljanna): ƙanshi, kai matuƙa ne a cikin haramta aljanna; domin cewa duk wanda ba zai ji ƙanshin abu ba to ba zai same shi ba.
- Wanda ya koyi wani ilimi daga abinda ake neman zatin Allah da shi saboda neman aiki, ko saboda wasu buƙatu na duniya daban; to wajibi ne ya tuba zuwa ga Allah daga hakan, Allah zai goge masa abinda ya faru na gurɓatacciyar niyya kuma Shi Ma'abocin falala ne Mai girma - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka -.
- Wannan gargaɗarwar ga mai neman ilimin shari'a ne, amma wanda ya nemi wani ilimi daga cikin ilimummukan duniya saboda jin daɗin duniya kamar Injiniyarin ko Kimiyya da wasunsu saboda duniya to shi niyyarsa ta tabbata gare shi.
سنن أبي داود (5/ 504) (3664). سنن ابن ماجه (1/ 169) (252). مسند أحمد (14/ 169) (8457). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 477). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (16/ 507). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 957). بهجة الناظرين، لسليم الهلالي (2/ 447). عون المعبود شرح سنن أبي داود، العظيم آبادي (10/ 70). حاشية السندي على سنن ابن ماجه، لمحمد التتوي (1/ 110).