Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambayi sahabbansa: Shin kun san waye muflis? suka ce: Muflis a cikinmu wanda ba shi da dukiya ko kaya, sai ya ce: Lallai muflis daga al'ummata zai zo ranar lahira da ayyuka na gari na sallah da azumi da zakka. Kuma zai zo haƙiƙa ya zagi wannan, ya yi wa wannan ƙazafi a mutuncinsa, kuma ya ci dukiyar wannan ya yi musunta, kuma ya zubar da jinin wannan ya zalinci shi, ya daki wannan ya wulaƙantashi, sai a bawa wanda aka zalinta daga kyawawan ayyukansa, idan kyawawan ayyukan suka ƙare kafin ya biya abinda ke kansa na haƙƙoƙi da abubuwan da aka zalinta, sai a ɗauki zunuban wanda aka zalinta sai a sanya su a takardun azzalimin, sannan a watsa masa sai a jefa shi a cikin wuta inda babu wani kyakkyawan aiki da zai rage gare shi .
- Tsoratarwa ga afkawa a cikin abubuwan da aka haramta, musamman ma abinda ke rataye da haƙƙoƙin bayi na dukiya da na ma'ana.
- Haƙƙoƙin mutane a tsakaninsu an gina su ne akan jayayya, haƙƙoƙin Mahalicci kuwa in banda shirka ababen ginawane akan afuwa.
- Anfani da hanyar muhawara wacce zata sawa mai ji shauƙi kuma ta juyo da tunaninsa kuma ta motsa himmarsa, musamman ma dai a cikin tarbiyya da fadakarwa.
- Bayanin ma'anar muflis na haƙiƙa, shi ne wanda waɗanda suke binsa bashi suka ɗauki ayyukansa na gari a ranar lahira.
- Sakayya a lahira za ta iya zuwa a kan dukkanin kyawawan ayyuka, har sai ya zama ba zai rage wani abu ba daga cikinsu.
- Mu'amalar Allah ga halitta mai tsayuwace akan adalci da gaskiya.
صحيح مسلم (4/ 1997) (2581). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 312). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، مجموعة من الباحثين (1/ 241). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 527).