عَنْ سَمُرَةَ بْنِ جُنْدَبٍ وَالْمُغِيرَةِ بْنِ شُعْبَةَ رضي الله عنهما قَالَا: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ حَدَّثَ عَنِّي بِحَدِيثٍ يُرَى أَنَّهُ كَذِبٌ، فَهُوَ أَحَدُ الْكَاذِبِينَ».
Daga Samura ɗan Jundub da Mugira ɗan Shu'ubah - Allah Ya yarda da su - sun ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya zantar da wani Hadisi daga gareni yana ganin cewa shi ƙarya ne to shi yana ɗaya daga cikin maƙaryata".
Muslim ne ya rawaito shi a cikin Mukaddima din saDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wanda ya riwaito wani Hadisi daga gare shi alhali shi yana sane ko yana zato ko yana rinjayar da zatansa cewa shi Hadisin ƙaryane a gare shi- tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -; to maruwaicinsa yana tarayya da mai ƙirƙirar wannan ƙaryar.
Fa’idoji
- Tabbatar da Hadisan da aka ruwaito daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, da tabbatar da ingancinsu kafin ruwaitosu.
- Siffar ƙarya ana sakinta ne ga dukkan wanda ya ƙirƙiri ƙarya da kuma wanda ya tsaya ya yadata da watsata tsakanin mutane.
- Ruwaito Hadisin ƙarya yana haramta akan wanda ya san kasancewarsa ƙarya ne, ko kuma ƙaryarsa ta rinjaya a zatonsa sai dai in ya kasance dan gargadi ne daga gare shi .
Madogara
صحيح مسلم (1/ 8).