Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agar shi - ya bada labarin cewa hakika wani lokaci ya kusa , wani sinfi na mutane zasu zamo acikinsa a zaune, dayansu yana kishingide akan shinfidarsa, Hadisi zai isar masa daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: Abinda zai raba tsakaninmu da ku a cikin al'amura shi ne Alkur’ani Mai girma shi ya ishemu, abinda muka samu a cikinsa na halal mu yi aiki da shi, abinda muka samu a cikinsa na haram mu nisance shi. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa duk abinda ya haramtashi ko ya yi hani gareshi a cikin sunnarsa to shi a hukunci kamar abinda Allah Ya haramtashi ne a cikin littafinSa; domin cewa shi ne mai isarwa daga Ubangijinsa.
- Girmama sunna kamar yadda ake girmama Alkur’ani kuma a yi riko da ita.
- Biyayya ga Manzo ita ce biyayya ga Allah, kuma saba masa shi ne sabawa Allah - Madaukakin sarki -.
- Tabbatar da hujjar sunna da kuma raddi akan wanda ya watsar da sunnoni ko ya musanta ta.
- Duk wanda ya bijirewa sunna ya yi da'awar takaituwa akan Alkur’ani to shi wanda ya bijire musu ne gaba dayansu, kuma makaryaci ne a cikin da'awar bin Alkur’ani .
- Daga cikin hujjojin Annabcinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bada labari game da wani abu da cewa zai faru a nan gaba, kuma ya faru kamar yadda ya bada labarin.
سنن أبي داود (7/ 13) (4604)، سنن الترمذي (4/ 399) (2664)، سنن ابن ماجه (1/ 9) (12)، نخب الأفكار في تنقيح مباني الأخبار في شرح معاني الآثار (13/ 154).