Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

MUHIMMANCIN SUNNA DA MATSAYINTA

Hadisai 9

Daya daga cikin mafi girman dalilai shi ne mutum ya yi addu'a ga wanin mahaifinsa, ko ya gani da idanunsa abin da ba ku gani ba, ko kuma ya ce wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - abin da bai fada ba

عن وَاثِلَةَ بن الأَسْقَعِ ـ رضي الله عنه ـ مرفوعاً: «إن من أعظم الفِرَى أن يَدَّعِيَ الرجلُ إلى غير أبيه، أو يُرِي عَيْنَهُ ما لم تَرَ، أو يقول على رسول الله صلى الله عليه وسلم ما لم يَقْلْ».
Daga Athilah Ibn Al-Asqa '- yardar Allah ta tabbata a gare shi - da isnadi: "Daya daga cikin mafi girman dalilai shi ne mutum ya yi addu'a ga wanin mahaifinsa, ko ya gani da idanunsa abin da ba ku gani ba, ko kuma ya ce wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - abin da bai fada ba".
Buhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

- صحيح البخاري، للإمام محمد بن إسماعيل البخاري، تحقيق محمد الناصر، دار طوق النجاة. - بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين؛ تأليف سليم الهلالي، دار ابن الجوزي- الطبعة الأولى1418ه. - نزهة المتقين شرح رياض الصالحين؛ تأليف د. مصطفى الخِن وغيره، مؤسسة الرسالة-بيروت، الطبعة الرابعة عشرة، 1407هـ. - كنوز رياض الصالحين»، لحمد بن ناصر العمار، دار كنوز إشبيليا- الطبعة الأولى1430ه. - دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين، لمحمد علي بن محمد بن علان بن إبراهيم البكري الصديقي الشافعي اعتنى بها: خليل مأمون شيحا، دار المعرفة . - شرح رياض الصالحين؛ للشيخ محمد بن صالح العثيمين، مدار الوطن، الرياض، 1426هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ku isar game da ni koda aya daya ce, kuma ku zantar game da Banu Isra'ial babu laifi, duk wanda ya yi mini karya da gangan to ya tanadi mazauninsa a wuta

عن عبد الله بن عمرو رضي الله عنهما أن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «بَلِّغُوا عَنِّي وَلَوْ آيَةً، وَحَدِّثُوا عَنْ بَنِي إِسْرَائِيلَ وَلَا حَرَجَ، وَمَنْ كَذَبَ عَلَيَّ مُتَعَمِّدًا فَلْيَتَبَوَّأْ مَقْعَدَهُ مِنَ النَّارِ».
Daga Abdullahi Dan Amr - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ku isar game da ni koda aya daya ce, kuma ku zantar game da Banu Isra'ial babu laifi, duk wanda ya yi mini karya da gangan to ya tanadi mazauninsa a wuta".
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana umarni da isar da ilimi daga gare shi na littafi ne ko Sunnah, koda abin ya zama kadan ne kamar aya daya daga Alkur’ani ko hadisi, da sharadin ya zama masani da abinda zai isarda shi kuma ya yi kira zuwa gare shi. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bayyana cewa babu laifi da akan bayanai daga Banu Isra'il da abinda ya afku gare su na al'amura da abinda ba ya karo tare da shari'a. Sannan ya yi gargadi daga yi masa karya, kuma cewa duk wanda ya yi masa karya da gangan to yariki masauki a wuta.

Fa’idoji
  1. Kwadaitarwa a isar da shari'ar Allah, kuma cewa mutum ya zama dole akansa ya bayar da abinda ya haddace kuma ya fahimta koda ya zama kadan ne.
  2. Wajabcin neman ilimi na shari'a dan ya samu ga tabbata ga bautar Allah da kuma isar da shari'arSa da inagantacciyar sura.
  3. Wajabcin tabbaci daga inagancin kowanne Hadisi kafin isar da shi ko yadashi dan kiyayewa daga shiga a wannan narkon mai tsanani.
  4. Kwadaitarwa akan gaskiyar zance da kuma kiyayewa a Hadisi dan kada ya afka a cikin karya, musamman ma a shari'ar Allah - Mai girma da daukaka -.
Madogara

صحيح البخاري (4/ 170) (3461). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 464). نزهة المتقين، لمصطفى الخن وغيره (2/ 951). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (5/ 429).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Wanda ya zantar da wani Hadisi daga gareni yana ganin cewa shi ƙarya ne to shi yana ɗaya daga cikin maƙaryata

عَنْ سَمُرَةَ بْنِ جُنْدَبٍ وَالْمُغِيرَةِ بْنِ شُعْبَةَ رضي الله عنهما قَالَا: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ حَدَّثَ عَنِّي بِحَدِيثٍ يُرَى أَنَّهُ كَذِبٌ، فَهُوَ أَحَدُ الْكَاذِبِينَ».
Daga Samura ɗan Jundub da Mugira ɗan Shu'ubah - Allah Ya yarda da su - sun ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya zantar da wani Hadisi daga gareni yana ganin cewa shi ƙarya ne to shi yana ɗaya daga cikin maƙaryata".
Muslim ne ya rawaito shi a cikin Mukaddima din saDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wanda ya riwaito wani Hadisi daga gare shi alhali shi yana sane ko yana zato ko yana rinjayar da zatansa cewa shi Hadisin ƙaryane a gare shi- tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -; to maruwaicinsa yana tarayya da mai ƙirƙirar wannan ƙaryar.

Fa’idoji
  1. Tabbatar da Hadisan da aka ruwaito daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, da tabbatar da ingancinsu kafin ruwaitosu.
  2. Siffar ƙarya ana sakinta ne ga dukkan wanda ya ƙirƙiri ƙarya da kuma wanda ya tsaya ya yadata da watsata tsakanin mutane.
  3. Ruwaito Hadisin ƙarya yana haramta akan wanda ya san kasancewarsa ƙarya ne, ko kuma ƙaryarsa ta rinjaya a zatonsa sai dai in ya kasance dan gargadi ne daga gare shi .
Madogara

صحيح مسلم (1/ 8).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ku saurara, kada wani mutum Hadisi ya je masa daga gareni alhali shi yana kishingide akan mazauninsa sai ya ce: Tsakanin mu da ku littafin Allah

عن المقدام بن معدِيْكَرِب رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «أَلَا هَلْ عَسَى رَجُلٌ يَبْلُغُهُ الْحَدِيثُ عَنِّي وَهُوَ مُتَّكِئٌ عَلَى أَرِيكَتِهِ فَيَقُولُ: بَيْنَنَا وَبَيْنَكُمْ كِتَابُ اللهِ، فَمَا وَجَدْنَا فِيهِ حَلَالًا اسْتَحْلَلْنَاهُ، وَمَا وَجَدْنَا فِيهِ حَرَامًا حَرَّمْنَاهُ، وَإِنَّ مَا حَرَّمَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَمَا حَرَّمَ اللهُ».
Daga Mikdam dan Maadikarib - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbbata agare shi - ya ce "Ku saurara, kada wani mutum Hadisi ya je masa daga gareni alhali shi yana kishingide akan mazauninsa sai ya ce: Tsakanin mu da ku littafin Allah, abinda muka samu na halal a cikinsa mu halattashi, abinda muka samu a cikinsa na haram mu haramtashi, kuma lallai abinda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya haramta to kamar abinda Allah Ya haramtane".
Abu Dawud da Tirmizi da Ibn Majah ne Suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agar shi - ya bada labarin cewa hakika wani lokaci ya kusa , wani sinfi na mutane zasu zamo acikinsa a zaune, dayansu yana kishingide akan shinfidarsa, Hadisi zai isar masa daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: Abinda zai raba tsakaninmu da ku a cikin al'amura shi ne Alkur’ani Mai girma shi ya ishemu, abinda muka samu a cikinsa na halal mu yi aiki da shi, abinda muka samu a cikinsa na haram mu nisance shi. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa duk abinda ya haramtashi ko ya yi hani gareshi a cikin sunnarsa to shi a hukunci kamar abinda Allah Ya haramtashi ne a cikin littafinSa; domin cewa shi ne mai isarwa daga Ubangijinsa.

Fa’idoji
  1. Girmama sunna kamar yadda ake girmama Alkur’ani kuma a yi riko da ita.
  2. Biyayya ga Manzo ita ce biyayya ga Allah, kuma saba masa shi ne sabawa Allah - Madaukakin sarki -.
  3. Tabbatar da hujjar sunna da kuma raddi akan wanda ya watsar da sunnoni ko ya musanta ta.
  4. Duk wanda ya bijirewa sunna ya yi da'awar takaituwa akan Alkur’ani to shi wanda ya bijire musu ne gaba dayansu, kuma makaryaci ne a cikin da'awar bin Alkur’ani .
  5. Daga cikin hujjojin Annabcinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bada labari game da wani abu da cewa zai faru a nan gaba, kuma ya faru kamar yadda ya bada labarin.
Madogara

سنن أبي داود (7/ 13) (4604)، سنن الترمذي (4/ 399) (2664)، سنن ابن ماجه (1/ 9) (12)، نخب الأفكار في تنقيح مباني الأخبار في شرح معاني الآثار (13/ 154).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Wanda ya yi mini karya da gangan to ya tanadi masaukinsa a wuta

عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «مَنْ كَذَبَ عَلَيَّ مُتَعَمِّدًا فَلْيَتَبَوَّأْ مَقْعَدَهُ مِنَ النَّارِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya yi mini karya da gangan to ya tanadi masaukinsa a wuta".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanda ya yi masa karya da gangan ta hanyar danganta masa magana ko aiki, to lallai cewa shi yana da mazauni a wuta; sakamako ne gare shi akan karyar da ya yi masa.

Fa’idoji
  1. Karya ga - Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da nufi da ganganci sababi ne na shiga wuta.
  2. Karya ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba kamar karya ce ga sauran mutane ba, saboda abinda ke tattare da hakan na barnace-barnace masu girma a Addini da duniya.
  3. Tsoratarwa akan yada hadisai kafin tabbatar da ingancin dangantasu ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 33) (110)، صحيح مسلم (1/ 10) (3)، إكمال المعلم (1/111)، شرح النووي على مسلم (1/65)، المفهم (1/32)، عمدة القاري شرح صحيح البخاري (2/ 151)، شرح مقدمة سنن ابن ماجه (5/ 8).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Na horeku da tsoron Allah, da ji da bi, koda bawa ne mutumin Habasha, za ku ga sabani mai tsanani a bayana, to na horeku da sunnata da sunnar Halifofina shiryayyu

عن العِرْباضِ بن ساريةَ رضي الله عنه قال: قام فينا رسول الله صلى الله عليه وسلم ذات يوم، فوَعَظَنا مَوعظةً بليغةً وَجِلتْ منها القلوبُ، وذَرَفتْ منها العيونُ، فقيل: يا رسول الله، وعظتَنَا موعظةَ مُودِّعٍ فاعهد إلينا بعهد. فقال: «عليكم بتقوى الله، والسمع والطاعة، وإن عبدًا حبشيًّا، وسترون من بعدي اختلافًا شديدًا، فعليكم بسنتي وسنة الخلفاء الراشدين المهديين، عَضُّوا عليها بالنواجِذ، وإياكم والأمور المحدثات، فإن كل بدعة ضلالة».
Daga Irbad dan Sariya - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wata rana Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsaya a cikinmu, sai ya yi mana wa'azi, wa'azi isasshe zukata suka ji tsoro daga gare shi, idanuwa suka zubar da hawaye daga gareshi, aka ce: Ya Manzon Allah ka yi mana wa'azin bankwana to ka yi mana alkawari. Sai ya ce: 'Na horeku da tsoron Allah, da ji da bi, koda bawa ne mutumin Habasha, za ku ga sabani mai tsanani a bayana, to na horeku da sunnata da sunnar Halifofina shiryayyu, ku rike su da turamen hakoranku, na haneku da fararrun al'amura, domin cewa kowacce bidi'a bata ce".
Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa sahabbansa wa'azi wa'azi isasshe zukata sun ji tsoro daga gare shi, kuma idanuwa sun zubar da hawaye daga gare shi, Sai suka ce : Ya Manzon Allah ! kai ka ce wannan wa'azin bankwana ne, saboda abinda suka gani ya kai matukarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wa'azi, sai suka nemi wata wasiyyar dan su yi riko da ita a bayansa, Ya ce: Ina yi muku wasicci da tsoron Allah - Mai girma da daukaka -, hakan da aikata wajibai da barin abubuwan da aka haramta, da ji da bi, wato: Ga shugabanni, koda bawa ne ya shugabanceku ko ya yi rinjaye a kanku, wato ya zama mafi kaskantar halitta sarki akanku kada ku hanu daga hakan, ku bi shi dan tsoron tada fitintinu, domin shi wanda ya rayu daga cikinku zai ga sabani mai yawa. Sannan ya bayyana musu mafita daga wannan sabanin, hakan dayin riko da sunnarsa da sunnar Halifofi shiryayyu a bayansa, Abu bakar Al-Siddik, da Umar Dan Al-khaddab, da Usman Dan Affan, da Aliyu Dan Abu Dalib - Allah Ya yarda su baki daya -, da riketa da turamen hakora wato - turamen hakora na karshe -: Yana nufi da hakan kokari a lazimtar sunna da yin riko da ita, ya kuma gargadesu daga fararrun al'amura kirkirarru a Addini, domin cewa kowacce bidi'a bata ce.

Fa’idoji
  1. Muhimmancin riko da sunna da kuma binta.
  2. Kula da wa'azuzzuka da kuma tausasa zukata.
  3. Umarni da bin Halifofi masu shiryarwa su hudu a bayansa, su ne Abubakar da Umar da Usman da Aliyu - Allah Ya yarda da su -.
  4. Hani daga kirikira a Addini, kuma cewa kowacce bidi'a bata ce.
  5. Ji da bi ga wanda ya jibinci al'amarin muminai in ba sabo ba ne.
  6. Muhimmancin tsoron Allah - Mai girma da daukaka - a dukkanin lokuta da halaye.
  7. Sabani mai afkuwane a cikin wannan al'ummar, a yayin faruwarsa to yana wajaba komawa zuwa sunnar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da Halifofinsa masu shiryarwa.
Madogara

الأربعون النووية (ص: 89) (ح28)، سنن أبي داود (7/ 16) (4607)، سنن الترمذي (4/ 408) (2676)، سنن ابن ماجه (1/ 28) (42)، مسند أحمد (28/ 367) (17142)، تحفة الأحوذي (7/ 366)، عون المعبود وحاشية ابن القيم (12/ 235)، شرح الأربعين النووية للعثيمين (ص: 278).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Za a samu wasu mutane a ƙarshen al'ummata suna zantar da ku abin da ku da iyayenku ba ku ji ba, to, kashedinku da su

عَنْ ‌أَبِي هُرَيْرَةَ عَنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنَّهُ قَالَ: «سَيَكُونُ فِي آخِرِ أُمَّتِي أُنَاسٌ يُحَدِّثُونَكُمْ مَا لَمْ تَسْمَعُوا أَنْتُمْ وَلَا آبَاؤُكُمْ، فَإِيَّاكُمْ وَإِيَّاهُمْ».
Daga Abu Huraira daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - lallai ya ce: "Za a samu wasu mutane a ƙarshen al'ummata suna zantar da ku abin da ku da iyayenku ba ku ji ba, to, kashedinku da su"
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa wasu mutane a ƙarshen al'ummata za su bayyana suna ƙirƙirar ƙarya, kuma suna faɗin abin da wani kafinsu bai faɗa ba, suna ba da labarai da hadisan ƙarya abubuwan ƙirƙira, sai (Annabi) tsira da aminci su tabbata a gareshi ya umarcemu mu nisancesu kada mu zauna da su, kuma kada mu ji hadisansu; don kada ƙirƙirarran hadisin ya tabbata a cikin zukata, sai mu kasa kuɓuta daga su.

Fa’idoji
  1. A cikinsa akwai alama daga alamonin Annabta, yayin da Annabi - tsira da aminin Allah su tabbata a gare shi ya ba da labain abin da zai afku a cikin al'ummarsa, sai ya afku kamar yadda ya ba da labari.
  2. Nisantar wanda zai yi ƙarya ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - haka kuma [da yin ta] ga Addinin Musulunci, da [buƙatar] kada a saurari ƙaryarsu.
  3. Gargaɗi game da karɓar Hadisai ko yaɗa su sai bayan tabbatarwa game da ingancinsu da tabbatarsu.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 12) (6)، قرة عين المحتاج في شرح مقدمة صحيح مسلم بن الحجاج (2/ 8).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ka rubuta, na rantse da wanda raina yake a hannunSa babu abin da zai fito daga cikinsa sai gaskiya

عن عبدِ الله بن عمرو رضي الله عنهما قال: كنتُ أكتبُ كلَّ شيءٍ أسمعُه من رسولِ الله صلَّى الله عليه وسلم أُريدُ حفْظَه، فنهتْني قريشٌ، وقالوا: أتكْتبُ كلَّ شيءٍ تَسمَعُه من رسول الله صلَّى الله عليه وسلم، ورسولُ الله صلَّى الله عليه وسلم بَشَرٌ يتكلَّمُ في الغضَبِ والرِّضا؟ فأمسَكتُ عن الكتاب، فذكرتُ ذلك لرسول الله صلَّى الله عليه وسلم، فأومأ بإصبَعِه إلى فيه، فقال: «اكتُبْ، فوالذي نفسي بيدِه، ما يَخرُجُ منه إلا حقٌّ».
Daga Abdullahi ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - ya ce: Na kasance ina rubuta dukkan abin da na ji shi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ina son haddace shi, sai Ƙuraishawa suka hana ni, suka ce: Shin ka dinga rubuta dukkan abin da ka ji shi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, alhali Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - mutum ne yana magana a cikin fushi da yarda? sai na dakata daga rubutun, sai na fadawa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, hakan sai ya yi nuni da 'yan yatsunsa zuwa bakinsa, sai ya ce: "Ka rubuta, na rantse da wanda raina yake a hannunSa babu abin da zai fito daga cikinsa sai gaskiya".
Abu Dawud ne Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Abdullah ɗan Amr - Allah Ya yarada da su - ya ce: Na kasance ina rubuta dukkanin abin da na ji shi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - don na haddace shi a rubuce, sai wasu mutane daga Ƙuraishawa suka hana ni, suka ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - mutum ne yana magana a cikin yarda da fushi, zai iya yin kuskure, sai na daina rubutun. Sai na ba wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - labarin abin da suka faɗa, sai ya yi nuni da danyatsansa zuwa bakinsa, sai ya ce; Ka rubuta, na rantse da wanda raina yake a hannunSa babu abin da yake fita daga cikinsa sai gaskiya a kowanne hali, haka a halin yarda da fushi. Haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya faɗa game da AnnabinSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: (Ba ya magana bisa son rai* shi (Alƙur'ani) ba wani abu ba ne ba ban da wahayi da ake saukar masa) [Al-najm 3-4].

Fa’idoji
  1. Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ma'asumi (wanda ba ya laifi, kuma ba ya kuskure) ne a cikin abin da yake isar da shi daga Ubangijinsa - Mai girma da ɗaukaka - a halin yarda da fushi.
  2. Kwaɗayin sahabbai - Allah Ya yarda da su - a kan kiyaye sunna da isar da ita.
  3. Halaccin rantsuwa ko da ba a sa a yi rantsuwar ba don maslaha, kamar ƙarfafa wani al'amari.
  4. Rubuta ilimi yana daga mafi muhimmancin dalilai da suke kiyaye ilimi.
Madogara

سنن أبي داود (5/ 489) (3646)، شرح سنن أبي داود للعباد (412/ 21).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
8 cikin 9
Hadisai 9
  1. Daya daga cikin mafi girman dalilai shi ne mutum ya yi addu'a ga wanin mahaifinsa, ko ya gani da idanunsa abin da ba ku gani ba, ko kuma ya ce wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - abin da bai fada ba
  2. Ku isar game da ni koda aya daya ce, kuma ku zantar game da Banu Isra'ial babu laifi, duk wanda ya yi mini karya da gangan to ya tanadi mazauninsa a wuta
  3. Wanda ya zantar da wani Hadisi daga gareni yana ganin cewa shi ƙarya ne to shi yana ɗaya daga cikin maƙaryata
  4. Ku saurara, kada wani mutum Hadisi ya je masa daga gareni alhali shi yana kishingide akan mazauninsa sai ya ce: Tsakanin mu da ku littafin Allah
  5. Wanda ya yi mini karya da gangan to ya tanadi masaukinsa a wuta
  6. Na horeku da tsoron Allah, da ji da bi, koda bawa ne mutumin Habasha, za ku ga sabani mai tsanani a bayana, to na horeku da sunnata da sunnar Halifofina shiryayyu
  7. Za a samu wasu mutane a ƙarshen al'ummata suna zantar da ku abin da ku da iyayenku ba ku ji ba, to, kashedinku da su
  8. Ka rubuta, na rantse da wanda raina yake a hannunSa babu abin da zai fito daga cikinsa sai gaskiya
  9. Ina yi muku wasicci da jin tsoron Allah, da ji da bi, ko da bawa ne ya shugabance ku, domin cewa wanda ya rayu daga cikinku zai ga saɓani mai yawa, to na horeku da sunnata da kuma sunnar halifofina shiryayyu masu shiryarwa

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com