Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Lallai masu yawaita tsinuwa ba sa zama masu shaida ko masu ceto a ranar alƙiyama

عَنْ أَبِي الدَّرْدَاءِ رضي الله عنه: سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «إِنَّ اللَّعَّانِينَ لَا يَكُونُونَ شُهَدَاءَ وَلَا شُفَعَاءَ يَوْمَ الْقِيَامَةِ».
Daga Abu Darda'i - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Lallai masu yawaita tsinuwa ba sa zama masu shaida ko masu ceto a ranar alƙiyama".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda yake yawaita tsinuwa akan wanda bai cancanteta ba to shi ya cancanci uƙuba biyu: Ta farko: Ba zai zama mai shaida ba a ranar alƙiyama akan al'ummu na isarwar Manzanninsu ga saƙonni zuwa garesu, kuma ba za'a karɓi shaidarsa ba a duniya; dan fasiƙancinsa, kuma ba za'a azurta shi da shahada ba ita ce mutuwa a tafarkin Allah. Ta biyu: Ba zai yi ceto ba a ranar alƙiyama lokacin da muminai suke yin ceto ga 'yan uwansu waɗanda suka cancanci (shiga) wuta.

Fa’idoji
  1. Haramta tsinuwa, kuma cewa yawaita ta yana daga manyan zunubai.
  2. Uƙuba a cikin hadisin kawai ita ga wanda tsinuwa ta yawaita daga gare shi ne, badan sau ɗaya ba ko waninsa ba, kuma akwai tsinuwar da ta halatta tana fitowa daga gare shi, shi ne wanda shari'a ta zo da ita da tsinuwar ma'abota siffofi ababen zargi ba tare da ayyanawa ba kamar faɗinka: "Allah Ya la'anci Yahudawa da Nasara", "Tsinuwar Allah ta tabbata akan azzalumai", "Allah Ya tsinewa masu ɗaukar hotuna (yin mutum-mutumi), "Allah Ya tsinewa wanda ya yi aiki irin aikin mutanen (Annabi) Luɗ", "Allah Ya tsinewa wanda ya yi yanka ga wanin Allah", "Allah Ya tsinewa mazan da suke kamanceceniya da mata, da matan da suke kamaceceniya da maza", da makamancin hakan.
  3. Tabbatar da ceton muminai a ranar alƙiyama.
Madogara

صحيح مسلم (4/ 2006) (2598). توضيح الأحكام من بلوغ المرام، لعبد الله البسام (7/ 469). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (10/ 297). فتح ذي الجلال والإكرام، لابن عثيمين (6/ 412).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
HALAYE ABIN ZARGI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com