Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Mun kasance a wurin Umar, sai ya ce: An hana mu ƙaƙale

عن أنس رضي الله عنه قال: كُنَّا عِنْدَ عُمَرَ فَقَالَ: «نُهِينَا عَنِ التَّكَلُّفِ».
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi ya ce: Mun kasance a wurin Umar, sai ya ce: An hana mu ƙaƙale.
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Umar Allah Ya yarda da shi yana ba da labarin Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana su yin abin da zai kawo wahala ba tare da wata buƙata a kan hakan ba, hakan magana ce ko aiki.

Fa’idoji
  1. Yana daga cikin ƙaƙalen da aka hana: Yawaita tambaya, ko ɗorawa kai abin da ba shi da iliminsa, ko tsanantawa a abinda Allah Ya sauƙaƙa a cikin sa.
  2. Ya kamata ga Musulmi ya koyawa kansa sauƙi, da rashin tsananta wa kai a magana, ko a aiki, a abin cinsa, ko abin sha, da maganganunsa da sauran ayyukansa.
  3. Musulunci addinin sauƙi ne.
Madogara

صحيح البخاري (9/ 95) (7293). نزهة المتقين، لمصطفى الخن وغيره (2/ 1136). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (6/ 391). فتح الباري شرح صحيح البخاري، لابن حجر (13/ 270). النهاية في غريب الحديث والأثر، لابن الأثير (4/ 196). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص930).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
HALAYE ABIN ZARGI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com