Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Idan Allah Ya tara mutanen farko da na ƙarshe ranar alƙiyama za'a ɗaga tuta ta dukkan wani mayaufdari, sai a ce: Wannan yaudarar wane ɗan wane ce

عَنِ ابْنِ عُمَرَ رَضيَ اللهُ عنهما قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِذَا جَمَعَ اللهُ الْأَوَّلِينَ وَالْآخِرِينَ يَوْمَ الْقِيَامَةِ يُرْفَعُ لِكُلِّ غَادِرٍ لِوَاءٌ، فَقِيلَ: هَذِهِ غَدْرَةُ فُلَانِ بْنِ فُلَانٍ».
Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan Allah Ya tara mutanen farko da na ƙarshe ranar alƙiyama za'a ɗaga tuta ta dukkan wani mayaufdari, sai a ce: Wannan yaudarar wane ɗan wane ce".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - idan ya tara mutanen farko dana ƙarshe ranar alƙiyama saboda hisabi, za'a kafawa kowanne maha'incin da bai cika alƙawarin da ya dauka ba tare da Allah ko tare da mutane ba, wata alamar da za'a kunya shi da ita akan ha'incinsa, kuma za’a yi kira akan sa a wannan ranar: Wannan ha'incin wane ɗan wane ne; dan bayyanar da mummunan aikinsa a filin taron alƙiyama.

Fa’idoji
  1. Haramta yaudara kuma cewa ita tana daga cikin manyan zunubai; domin a cikinta ne wannan narkon mai tsanani yake.
  2. Yaudarar da aka yi narko a kanta ta ƙunshi dukkan wanda ya amince maka akan jini, ko mutunci, ko sirri, ko dukiya sai ka ha'ince shi, ka kuma saɓawa zatinsa a cikin amanarka.
  3. AlƘurɗubi ya ce: wannan magana ce daga gare shi zuwa ga larabawa da irin abinda suke aikatawa; domin su sun kasance suna ɗaga farar tuta dan cika alƙawari, suna ɗaga baƙar tuta kuma dan yaudara, dan su zargi mayaudari, sai Hadisin ya hukunta afkuwar irin haka ga mayaudari; dan ya shahara da siffarsa a taron alƙiyama, kuma al’umma da suke a filin alƙiyama su zarge shi.
  4. Ibnu Hajar ya ce: Kuma a cikinsa mutane za'a kirasu ranar alƙiyama (tare da sunayen) iyayen su; saboda faɗinsa: "Wannan ce yaudarar wane ɗan wane".
Madogara

صحيح البخاري (4/ 104) (3188) صحيح مسلم (3/ 1359) (1735). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص745). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (2/ 188).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
HALAYE ABIN ZARGI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com