عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِنَّ الدُّنْيَا حُلْوَةٌ خَضِرَةٌ، وَإِنَّ اللهَ مُسْتَخْلِفُكُمْ فِيهَا، فَيَنْظُرُ كَيْفَ تَعْمَلُونَ، فَاتَّقُوا الدُّنْيَا وَاتَّقُوا النِّسَاءَ، فَإِنَّ أَوَّلَ فِتْنَةِ بَنِي إِسْرَائِيلَ كَانَتْ فِي النِّسَاءِ».
Daga Abu sa'id Al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai cewa duniya mai zakice koriya, kuma Allah Mai gadar daku ne a cikinta, sai ya duba yaya zaku yi aiki, don haka ku ji duniya kuma ku kiyayi mata, domin cewa farkon fitinar Banu Isra'ila ta kasance a mata ne".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa duniya mai zakice a abubuwan zaki, kuma koriya a abin gani, sai mutum ya rudu da ita ya yi zari a cikinta ya kuma sanya ta mafi girman himmarsa. Kuma cewa Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka - ya sanya shashinmu zai maye gurbin sashi a wannan duniyar, dan ya duba ya zamu yi aiki, shin zamu tsaya da biyayyarSa, ko zamu saba maSa? Sannan ya ce: Ku kiyayi jin dadin duniya ya rudeku da kawarta, sai ya doraku akan barin abinda Allah Ya umarceku da shi, da kuma afkawa a cikin abinda ya haneku daga gareshi. Daga mafi girman abinda ya wajaba a kiyaya daga gare shi daga fitintinun duniya (su ne) mata, cewa ita ce farkon fitinar da Banu Isra'ila suka afka a cikinta.
Fa’idoji
- Kwadaitarwa akan lazimtar tsoron Allah, da barin shagaltuwa da zahirin duniya da kawarta.
- Kiyayewa daga fitinuwa da mata, na kallo ko sakaci da cakuduwarsu da maza manisanta, ko wanin hakan.
- Fitinar mata tana daga mafi girman fitintinu a duniya.
- Wa'azantuwa da daukar izina daga al'ummun da suka gabata, abinda ya faru ga Banu isra'ila zai iya faruwa ga wasunsu.
- Fitinar mata idan ta kasance mata ce to ita zata iya dorawa mutum ciyarwar da ba zai iya ba, sai ta shagaltar da shi daga neman al'amuran Addini, ta kuma dora masa halaka a neman duniya, idan kuma manisanciya ce to fitinarta da rudar da maza ne da karkatar dasu daga gaskiya idan sun fita sun cakuda dasu, musanmama dai idan sun zama matsiraita masu shiga ta nuna tsiraici, wannan zai iya kaiwa zuwa afkawa a cikin zina a girmansa, to yana kamata ga mumini ya yi riko ga Allah, da kuma kwadayi gareShi don kubuta daga fitinarsu.
Madogara
صحيح مسلم (4/ 2098) (2742).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 146).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 173).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 103).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «الدُّنْيَا سِجْنُ الْمُؤْمِنِ وَجَنَّةُ الْكَافِرِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Duniya kurkukun mumini ce kuma aljannar kafiri ce».
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa rayuwar duniya ga mumini kamar kurkuku ce dan wajibci ga abubuwan da shari'a da aka ɗora masa, na aikata abinda aka yi umarni da shi da kuma barin abinda aka yi gargaɗi da shi, idan ya mutu ya huta daga wannan kuma zai koma zuwa ga abinda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yi masa tanadi na ni'ima madawwamiya.
ita (duniyar) kamar kuma aljanna ce ga kafiri; domin cewa shi yana aikata dukkanin abinda ransa yake sha'awarsa kuma son ransa yake umartarsa, idan ya mutu zai juya zuwa ga abinda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yimasa tanadi a ranar alƙiyama na azaba tabbatacciya.
Fa’idoji
- Nawawi ya ce: Dukkan mumini abin sawa a cikin kurkuku ne abin hana wa sha'awowin da aka haramta da waɗanda aka karhanta a duniya ne, kuma abin ɗorawa ayyukan ɗa'a ne masu wahala, idan ya mutu ya huta daga wannan, kuma ya koma zuwa ga abinda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yi masa tanadi na ni'ima madawwamiya, da kuma hutu tsarkakakke daga tawaya. Amma kafiri kawai yana da abinda ya samu a duniya tare da ƙarancinsa da kuma gurɓatarsa da abubuwan da suke ɓata su, idan ya mutu zai tafi zuwa ga azaba madawwamiya, da kuma taɓewa ta har abada.
- Sindi ya ce: Faɗinsa: (Kurkukun mumini ce) cewa shi koda ya kasance a cikin ni'ima to aljanna ce mafi alheri gare shi, (Kuma aljannar kafiri ce) cewa shi ko da ya kasance a cikin wahala to wuta ita ce mafi sharri ce gare shi.
- Wulaƙantar duniya ga Allah - Maɗaukakin sarki -.
- Duniya gidan jarraba ce ga masu imani.
- Kafiri an gaggauto da aljannarsa a duniyarsa; sai aka yi masa uƙuba da haramta aljannar lahira da kuma ni'imarta.
Madogara
صحيح مسلم (4/ 2272) (2956).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 535).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 419).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 367).
موسوعة فقه القلوب، لمحمد التويجري (4/ 3471).
كتاب العلم، لابن عثيمين (ص37).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن سهل بن سعد الساعدي ـرضي الله عنه- قَالَ رَسُول اللَّه -صَلّى اللهُ عَلَيْهِ وسَلَّم-: «لو كانت الدنيا تَعدل عند الله جَناح بَعوضة، ما سَقَى كافراً منها شَرْبَة ماء».
Daga Sahl n Sa'ad Al-Sa'idi -Allah ya yarda da shi- Manzon Allah SAW ya ce: "Da ace Duniya tana da kimar Fuffuken Saura, da Kafiri bai sha Ruwa Makwarwa daya ba a cikinta"
Al-Tirmithi Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara
كنوز رياض الصالحين أ. د . حمد بن ناصر بن عبد الرحمن العمار - دار كنوز اشبيليا ـ الطبعة الأولى : 1430 هـ.
بهجة الناظرين - الشيخ: سليم بن عيد الهلالي - دار ابن الجوزي.
نزهة المتقين - د . مصطفى سيعد الخن، د. مصطفى البغا، محي الدين مستو، علي الشرجبي، محمد أمين لطفي، مؤسسة الرسالة ، بيروت - الطبعة الأولى : 1397 هـ 1977 م الطبعة الرابعة عشر 1407هـ 1987م.
شرح رياض الصالحين - المؤلف: محمد بن صالح بن محمد العثيمين - الناشر: دار الوطن للنشر، الرياض
الطبعة: 1426 هـ.
رياض الصالحين د. ماهر بن ياسين الفحل - الناشر: دار ابن كثير للطباعة والنشر والتوزيع، دمشق - بيروت
الطبعة: الأولى، 1428 هـ - 2007 م.
صحيح مسلم- مسلم بن الحجاج القشيري النيسابوري - المحقق: محمد فؤاد عبد الباقي
الناشر: دار إحياء التراث العربي - بيروت.
سنن الترمذي- المؤلف: محمد بن عيسى الترمذي، أبو عيسى - تحقيق وتعليق: أحمد محمد شاكر (جـ 1، 2) ومحمد فؤاد عبد الباقي (جـ 3) وإبراهيم عطوة عوض المدرس في الأزهر الشريف (جـ 4، 5) الناشر: شركة مكتبة ومطبعة مصطفى البابي الحلبي - مصر - الطبعة: الثانية، 1395 هـ - 1975 م.
صحيح وضعيف سنن الترمذي - المؤلف: محمد ناصر الدين الألباني- مصدر الكتاب: برنامج منظومة التحقيقات الحديثية - المجاني - من إنتاج مركز نور الإسلام لأبحاث القرآن والسنة بالإسكندرية
تيسير الكريم الرحمن في تفسير كلام المنان - المؤلف: عبد الرحمن بن ناصر بن عبد الله السعدي - المحقق: عبد الرحمن بن معلا اللويحق - الناشر: مؤسسة الرسالة -الطبعة: الأولى 1420هـ -2000 م.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ حَكِيمِ بْنِ حِزَامٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: سَأَلْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَأَعْطَانِي، ثُمَّ سَأَلْتُهُ فَأَعْطَانِي، ثُمَّ قَالَ لِي: «يَا حَكِيمُ، إِنَّ هَذَا المَالَ خَضِرٌ حُلْوٌ، فَمَنْ أَخَذَهُ بِسَخَاوَةِ نَفْسٍ، بُورِكَ لَهُ فِيهِ، وَمَنْ أَخَذَهُ بِإِشْرَافِ نَفْسٍ لَمْ يُبَارَكْ لَهُ فِيهِ، وَكَانَ كَالَّذِي يَأْكُلُ وَلاَ يَشْبَعُ، وَاليَدُ العُلْيَا خَيْرٌ مِنَ اليَدِ السُّفْلَى»، قَالَ حَكِيمٌ: فَقُلْتُ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، وَالَّذِي بَعَثَكَ بِالحَقِّ لاَ أَرْزَأُ أَحَدًا بَعْدَكَ شَيْئًا حَتَّى أُفَارِقَ الدُّنْيَا، فَكَانَ أَبُو بَكْرٍ يَدْعُو حَكِيمًا لِيُعْطِيَهُ العَطَاءَ، فَيَأْبَى أَنْ يَقْبَلَ مِنْهُ شَيْئًا، ثُمَّ إِنَّ عُمَرَ دَعَاهُ لِيُعْطِيَهُ، فَيَأْبَى أَنْ يَقْبَلَهُ، فَقَالَ: يَا مَعْشَرَ المُسْلِمِينَ، إِنِّي أَعْرِضُ عَلَيْهِ حَقَّهُ الَّذِي قَسَمَ اللَّهُ لَهُ مِنْ هَذَا الفَيْءِ، فَيَأْبَى أَنْ يَأْخُذَهُ. فَلَمْ يَرْزَأْ حَكِيمٌ أَحَدًا مِنَ النَّاسِ بَعْدَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ حَتَّى تُوُفِّيَ رَحِمَهُ اللَّهُ.
Daga Hakim ɗan Hizam - Allah Ya yarda da shi - ya ce:: Na roki Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya bani, sannan na sake rokonsa sai ya bani, sannan ya ce da ni: «Ya Hakim lallai ita wannan dukiyar koriya ce mai zaƙi, wanda ya karɓeta da wadatar rai, za’a yi masa albarka a cikinta, wanda ya karɓeta da ɗaukakar rai ba za’a yi masa albarka a cikinta ba, sai ya zama kamar wanda yake ci ne ba ya ƙoshi, hannu maɗaukaki shi ne mafi alheri daga hannu maƙasƙanci». Hakim ya ce: Sai na ce: Ya Manzon Allah, na rantse da wanda ya aikoka da gaskiya ba zan taɓa tauye wa wani, wani abu ba a bayanka har na bar duniya, Abubakar ya kasance yana kiran Hakim dan ya bashi kyauta (daga Baitul mali), sai ya ƙi karɓar komai daga gurinsa, sannan Umar ya kira shi dan ya ba shi, sai ya ƙi karɓa, sai ya ce: Yaku jama'a musulmai, lallai cewa ni ina ba shi haƙƙinsa wanda Allah Ya raba masa daga wannan ganimar, sai ya ƙi karɓarsa, Hakim bai tauyewa wani mutum daga cikin mutane ba bayan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ba - har sai da ya rasu - Allah ya yi masa rahama -.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Hakim ɗan Hizam - Allah Ya yarda da shi - ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - wani abu na jin daɗin duniya sai ya ba shi, sannan ya roke shi karo na biyu sai ya ba shi, sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce masa: Ya Hakim, lallai cewa wannan dukiyar abar sha'awace abar so ce, wanda ya sameta ba tare da roƙo ba kuma ya karɓeta ba tare da zari da kuma naci ba, za’a yi masa albarka a cikinta, wanda ya karɓeta da tsinkayar rai da kuma kwaɗayi ba za’a yi masa albarka a cikinta ba, zai zama kamar wanda yake ci ba ya ƙoshi, hannu maɗaukaki mai bayarwa shi ne mafi alheri a wurin Allah daga hannu maƙasƙanci mai roƙo. Hakim ya ce: Sai na ce: Ya Manzon Allah, na rantse da wanda Ya aikoka da gaskiya ba zan karbi dukiyar wani ba ta hanyar roko daga gare shi ba a bayanka har na bar duniya. Halifan Manzon Allah Abubakar - Allah Ya yarda da shi - ya kasance yana kiran Hakim dan ya ba shi rabonsa daga baitul mali, sai ya ƙi karɓar komai daga gare shi, sannan sarkin muminai - Umar - Allah Ya yarda da shi - ya kira shi dan ya ba shi ita, sai ya ƙi karɓarta, sai Umar ya ce: Yaku taron jama'ar musulmai, lallai ni ina ba shi haƙƙinsa wanda Allah Ya raba masa daga ganimar da musulmai suka samu daga kafirai ba tare da ya ƙi ba, sai ya ƙi karɓarta, bayan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - Hakim bai rage dukiyar kowa ba ta hanyar nemanta har ya yi wafati - Allah Ya yarda da shi -.
Fa’idoji
- Karɓar dukiya da tarata ta hanyar da aka shara'anta ba ya cin karo da gudun duniya; domin gudun duniya wadatuwar zuciya ne da kuma rashin rataya zuciya da dukiya.
- Bayanin girman karamcin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma cewa shi yana bada kyautar wanda ba ya jin tsoron talauci har abada.
- Yin nasiha da kuma kwaɗayi akan amfanar da 'yan uwa a lokacin neman taimako; domin zuciya tana kasancewa mai shirin karɓar amfani ta hanyar zantuttuka masu daɗi.
- Kamewa daga roƙon mutane da kuma kore shi musamman ma dai in babu wata buƙata.
- A cikinsa akwai zargin kwaɗayi akan dukiya da kuma yawan roƙo.
- Mai roƙo idan ya nace akan roƙon, to babu laifi idan an ƙi ba shi, da taɓar da shi da kuma yi masa wa'azi, da umartarsa da kamewa da kuma barin kwaɗayi akan karɓa.
- Ba wanda ya cancanci karɓar wani abu daga baitul mali sai bayan shugaba ya ba shi shi, amma kafin raba ganima to hakan ba haƙƙinsa ba ne.
- Halaccin roƙo saboda buƙata.
- Ibnu Hajar ya ce: A cikinsa yana kamata ga shugaba kada ya bayyanawa mai roko abinda ke cikin roƙonsa na ɓarna sai bayan ya biya masa buƙatarsa, dan wa'azinsa ya dace da gurbinsa, dan kada ya riya cewa hakan wani sababi ne na hana shi buƙatarsa.
- A cikinsa akwai falalar Hakim - Allah Ya yarda da shi - da kuma dorawa kansa alƙawarin da ya yi tare da Allah da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
- Ishaƙ ɗan Rahuwaih ya ce: Hakim - Allah Ya yarda da shi - ya rasu, a lokacin da ya rasu yana daga cikin mafiya yawan Ƙuraishwa a dukiya.
Madogara
صحيح البخاري (4/ 5) (2750).
صحيح مسلم (2/ 717) (1035).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (8/ 13).
بهجة الناظرين، لسليم الهلالي (1/ 584).
نزهة المتقين، لمجموعة من الباحثين (1/ 459).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 386).
منار القاري، لحمزة قاسم (3/ 45).
المنهاج شرح صحيح مسلم، للنووي (7/ 126).
إكمال المعلم بفوائد مسلم، للقاضي عياض (3/ 566).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضيَ اللهُ عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنَّهُ قَالَ: «اللهُمَّ لَا عَيْشَ إِلَّا عَيْشُ الْآخِرَهْ، فَاغْفِرْ لِلْأَنْصَارِ وَالْمُهَاجِرَهْ».
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ya Allah babu wata rayuwa sai rayuwar lahira, ka gafartawa Mutanen Madina da waɗanda suka yi hijira».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa babu wata rayuwa ta haƙiƙa sai rayuwar lahira, a cikin yardar Allah da rahamarSa da kuma aljannarSa; domin rayuwar duniya mai gushewa ce, rayuwar lahira kuwa ita ce dawwamammiya mai wanzuwa, sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi addu'ar gafara da girmamawa da gyaruwa ga mutanen Madina waɗanda suka kawo ɗauki ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da Muhajirun, suka taimakesu, suka raba musu dukiyoyinsu, kuma (ya yi addu'a) ga Muhajirun waɗanda suka bar gidajensu da dukiyoyinsu suna neman falala daga Allah da kuma yarda.
Fa’idoji
- Gudun duniyarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a duniya da kuma fuskantowarsa ga lahira.
- Gargaɗawar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga al'ummarsa a jin daɗin rayuwar duniya mai gushewa.
- Bayanin darajar Muhajirai da Ansar, inda suka rabauta da addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - garesu da gafara.
- Kada bawa ya yi farin ciki da abinda yake samu na duniya, ita mai saurin gushewa ce tare da abinda ke cikinta na gurɓacewa, kaɗai gidan tabbata shi ne gidan lahira.
Madogara
صحيح البخاري (8/ 88) (6413).
صحيح مسلم (3/ 1431) (1805).
مرقاة المفاتيح، لعلي القاري (7/ 3016).
فتح الباري شرح صحيح البخاري، لابن حجر (11/ 231).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 362).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (7/ 223).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 529).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 412).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضيَ اللهُ عنهُ سمعتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يقولُ: «أَلاَ إِنَّ الدُّنْيَا مَلْعُونَةٌ، مَلْعُونٌ مَا فِيهَا، إِلاَّ ذِكْرُ اللهِ وَمَا وَالاَهُ وَعَالِمٌ أَوْ مُتَعَلِّمٌ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Ku saurara lallai cewa duniya tsinanniya ce, kuma abinda ke cikinta ma tsinanne ne, sai ambatan Allah da abinda ke jiɓintarsa da malami ko mai neman ilimi".
Tirmizi ne ya Rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa duniya da abinda ke cikinta abin ƙine a wurin Allah abin zargi abin bari abin nisantarwa, kuma abinda ke cikinta abin bari ne ba abin yabo bane; dan kasancewarta da dukkan abinda ke cikinta yana shagaltarwa daga barin Allah, kuma yana nisantarwa daga gare shi, saidai ambatan Allah da abinda ya kusance shi ya zama yana da jinsi da shi, cikin abinda Allah Ya so shi, ko masanin ilimi na shari'a wanda yake koyar da mutane, ko mai neman ilimin shari'a ɗin.
Fa’idoji
- La'antar duniya ba ta halatta kai tsaye; dan zuwan hadisan da suke hani daga hakan, saidai la'antar abinda ke nisantarwa daga Allah - Maɗaukakin sarki - a cikinta kuma yake shagaltarwa daga biyayyrSa to yana halatta.
- Dukkan abinda ke cikin duniya to wasa ne kuma shagala ne sai ambatan Allah da abinda yake sababi kuma mai taimako a cikin hakan.
- Bayanin falalar ilimi da ma'abotansa da kuma ɗalibansa.
- Ibnu Taimiyya ya ce: Kaɗai ana zargin haramun ne bata fuskarsa ba, ko halal ta hanyar neman yawaitawa da alfahari, da abinda ake riƙa dan nufin fariya da gasa, to wannan shi ne wanda yake abin ƙi gurin masu hankali.
Madogara
سنن الترمذي (4/ 151) (2322).
سنن ابن ماجه (5/ 231) (4112).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 542).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 424).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (7/ 325).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 374).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي هريرة رضي الله عنه عن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «لو كان لي مِثْلُ أحدٍ ذهبًا، لسرني أن لا تمر عليَّ ثلاث ليالٍ وعندي منه شيءٌ إلا شيء أرْصُدُهُ لِدَيْنٍ».
Daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - a kan manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wanda ya ce: "Idan ina da kwatankwacin zinare, da na yi farin ciki da cewa darare uku ba za su wuce ni ba alhali ina da wani abu daga ciki sai wani abu da nake bi bashi."
Bukhari da Muslim Suka Rawaito shi amma lafazin na Bukhari neDarajaIngantacce ne
Sharhi
Idan da a ce ina da kudin adadin Dutsen Uhud na zinare tsantsa, da na kashe su duka saboda Allah, ban bar komai ba sai abin da nake bukata domin biyan hakkoki da biyan bashin da ke kaina.
Madogara
كنوز رياض الصالحين، أ.د. حمد بن ناصر بن عبد الرحمن العمار، دار كنوز اشبيليا، الطبعة الأولى : 1430 هـ.
منار القاري شرح مختصر صحيح البخاري، المؤلف: حمزة محمد قاسم، راجعه: الشيخ عبد القادر الأرناؤوط، عني بتصحيحه ونشره: بشير محمد عيون، الناشر: مكتبة دار البيان، دمشق - الجمهورية العربية السورية، مكتبة المؤيد، الطائف - المملكة العربية السعودية عام النشر: 1410 هـ - 1990 م.
نزهة المتقين، د. مصطفى سعيد الخن، د. مصطفى البغا، محي الدين مستو، علي الشرجبي، محمد أمين لطفي، مؤسسة الرسالة، بيروت، الطبعة الأولى : 1397 هـ 1977 م، الطبعة الرابعة عشر 1407 هـ 1987م.
شرح رياض الصالحين، المؤلف: محمد بن صالح بن محمد العثيمين، الناشر: دار الوطن للنشر، الرياض، الطبعة: 1426 هـ.
رياض الصالحين، د. ماهر بن ياسين الفحل، الناشر: دار ابن كثير للطباعة والنشر والتوزيع، دمشق - بيروت، الطبعة: الأولى، 1428 هـ - 2007 م.
صحيح مسلم، المؤلف: مسلم بن الحجاج القشيري النيسابوري، المحقق: محمد فؤاد عبد الباقي، الناشر: دار إحياء التراث العربي - بيروت.
صحيح البخاري، المؤلف: محمد بن إسماعيل أبو عبدالله البخاري الجعفي، المحقق: محمد زهير بن ناصر الناصر، الناشر: دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى، 1422هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن جابر رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم مر بالسوق والناس كَنَفَتَيَهِ، فمر بِجَدْيٍ أَسَكَّ ميت، فتناوله فأخذ بأذنه، ثم قال: «أيكم يحب أن يكون هذا له بدرهم؟» فقالوا: ما نحب أنه لنا بشيء وما نصنع به؟ ثم قال: «أتحبون أنه لكم؟» قالوا: والله لو كان حيا ًكان عيباً، إنه أسك فكيف وهو ميت! فقال: «فو الله للدنيا أهون على الله من هذا عليكم».
A kan Jaber, yardar Allah ta tabbata a gare shi, cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya wuce ta kasuwa kuma mutane sun kasance kamarsa. Suka ce: Me muke so da muke da wani abu kuma me za mu yi da shi? Sannan ya ce: "Shin kuna son shi a gare ku?" Suka ce: Wallahi da yana raye, da ya zama aibi. Ya ce: "Gama Allah na duniya ne, ya fi muku sauki ga Allah."
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara
- رياض الصالحين من كلام سيد المرسلين؛ للإمام أبي زكريا النووي، تحقيق د. ماهر الفحل، دار ابن كثير-دمشق، الطبعة الأولى، 1428ه.
- بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين؛ تأليف سليم الهلالي، دار ابن الجوزي- الطبعة الأولى1418ه.
- نزهة المتقين شرح رياض الصالحين؛ تأليف د. مصطفى الخِن وغيره، مؤسسة الرسالة-بيروت، الطبعة الرابعة عشر، 1407هـ.
- صحيح مسلم؛ حققه ورقمه محمد فؤاد عبد الباقي، دار عالم الكتب-الرياض، الطبعة الأولى، 1417هـ.
- شرح رياض الصالحين؛ للشيخ محمد بن صالح العثيمين، مدار الوطن، الرياض، 1426هـ.
- كنوز رياض الصالحين، لحمد بن ناصر العمار، دار كنوز إشبيليا- الطبعة الأولى1430ه.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com