Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

‌Duniya kurkukun mumini ce kuma aljannar kafiri ce

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «الدُّنْيَا سِجْنُ الْمُؤْمِنِ وَجَنَّةُ الْكَافِرِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «‌Duniya kurkukun mumini ce kuma aljannar kafiri ce».
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa rayuwar duniya ga mumini kamar kurkuku ce dan wajibci ga abubuwan da shari'a da aka ɗora masa, na aikata abinda aka yi umarni da shi da kuma barin abinda aka yi gargaɗi da shi, idan ya mutu ya huta daga wannan kuma zai koma zuwa ga abinda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yi masa tanadi na ni'ima madawwamiya. ita (duniyar) kamar kuma aljanna ce ga kafiri; domin cewa shi yana aikata dukkanin abinda ransa yake sha'awarsa kuma son ransa yake umartarsa, idan ya mutu zai juya zuwa ga abinda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yimasa tanadi a ranar alƙiyama na azaba tabbatacciya.

Fa’idoji
  1. Nawawi ya ce: Dukkan mumini abin sawa a cikin kurkuku ne abin hana wa sha'awowin da aka haramta da waɗanda aka karhanta a duniya ne, kuma abin ɗorawa ayyukan ɗa'a ne masu wahala, idan ya mutu ya huta daga wannan, kuma ya koma zuwa ga abinda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yi masa tanadi na ni'ima madawwamiya, da kuma hutu tsarkakakke daga tawaya. Amma kafiri kawai yana da abinda ya samu a duniya tare da ƙarancinsa da kuma gurɓatarsa da abubuwan da suke ɓata su, idan ya mutu zai tafi zuwa ga azaba madawwamiya, da kuma taɓewa ta har abada.
  2. Sindi ya ce: Faɗinsa: (Kurkukun mumini ce) cewa shi koda ya kasance a cikin ni'ima to aljanna ce mafi alheri gare shi, (Kuma aljannar kafiri ce) cewa shi ko da ya kasance a cikin wahala to wuta ita ce mafi sharri ce gare shi.
  3. Wulaƙantar duniya ga Allah - Maɗaukakin sarki -.
  4. Duniya gidan jarraba ce ga masu imani.
  5. Kafiri an gaggauto da aljannarsa a duniyarsa; sai aka yi masa uƙuba da haramta aljannar lahira da kuma ni'imarta.
Madogara

صحيح مسلم (4/ 2272) (2956). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 535). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 419). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 367). موسوعة فقه القلوب، لمحمد التويجري (4/ 3471). كتاب العلم، لابن عثيمين (ص37).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
ZUHUDU DA TSANTSENI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com