Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Lallai wasu mutane suna kutsawa a dukiyar Allah ba tare da wani haƙƙi ba, to, wuta ta tabbata a garesu ranar al-ƙiyama

عن خَولة الأنصاريةِ رضي الله عنها قالت: سمعت النبي صلى الله عليه وسلم يقول: «إِنَّ رِجَالًا يَتَخَوَّضُونَ فِي مَالِ اللهِ بِغَيْرِ حَقٍّ، فَلَهُمُ النَّارُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ».
Daga Khaulat Al-Ansariyya - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Lallai wasu mutane suna kutsawa a dukiyar Allah ba tare da wani haƙƙi ba, to, wuta ta tabbata a garesu ranar al-ƙiyama".
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labari game da wasu mutane da suke tasarrufi a dukiyoyin musulmai da ɓarna, suna ɗaukarsu ba tare da wani haƙƙi ba, wannan ma'ana ce mai gamewa game da dukiya ta hanyar tara ta da kasuwanci da ita ba tare da halaccinta ba, da ciyar da ita ba ta ingantacciyar hanya ba, cin dukiyoyin marayu da dukiyoyin waƙafi da musanta amanoni da ƙwace ba tare da cancanta ba daga dukiyoyi game gari, to, duk suna shiga cikin wannan. Sannan (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ba da labarin cewa sakamakonsu (shi ne) wuta a ranar al-ƙiyama.

Fa’idoji
  1. Dukiyoyin da ke hannun mutane su ne dukiyar Allah, Ya sanyasu mamaya a kansu don su ciyar da su ta hanyar da aka shara'anta, kuma su nisanci tasarrufi a cikinsu da ɓarna, wannan ya game shugabanni da wasunsu cikin ragowar mutane.
  2. Tsanantawar shari'a a dukiyar al'umma, kuma cewa wanda ya jiɓinci wani abu daga cikinta, to, za a yi masa hisabi a ranar al-ƙiyama a kan samota da kuma ciyar da ita.
  3. Wanda yake tasarrufi tasarrufin da ba na shari'a ba a cikin dukiya ya shiga cikin wannan narkon, duka ɗaya ne dukiyar ta kasance tasa ce ko ta waninsa ce.
Madogara

صحيح البخاري (4/ 85) (3118). فتح ذي الجلال والاكرام بشرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (6/ 372). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (10/ 231). توضيح الأحكام من بلوغ المرام، للبسام (7/ 424).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALOLI DA LADUBBA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com