Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Zuciyar babba ba zata gushe ba tana budurwa a kan abubuwa biyu: A son duniya da tsawon buri

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «لاَ يَزَالُ قَلْبُ الكَبِيرِ شَابًّا فِي اثْنَتَيْنِ: فِي حُبِّ الدُّنْيَا وَطُولِ الأَمَلِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Zuciyar babba ba zata gushe ba tana budurwa a kan abubuwa biyu: A son duniya da tsawon buri".
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa dattijo yana girma jikinsa yana rauni, sai dai zuciyarsa budurwa ce akan son abubuwa biyu: Na farko: Son duniya da yawan dukiya. Na biyu: Tsawon rayuwa da shekaru da buri.

Fa’idoji
  1. Bayanin abinda aka halicci mutum a kansa, shi ne son duniya da tsawon buri.
  2. Nuni akan zargin yawan buri, da kwaɗayi akan tara dukiya, hakan yana hukunta tanadi ga mutuwa da falalar sadaka ga mawadaci, da kamewa ga talaka.
  3. Mafi soyuwar abubuwa ga ɗan Adam shi ne ransa, shi mai kwaɗayi ne a akan wanzuwarsa, saboda haka sai ya so tsawon rayuwa, kuma ya so dukiya; domin cewa shi yana daga mafi girman sabubba a dawwamar lafiya da jin daɗi, a duk lokacin da ya ji kusancin ƙarewar hakan sai sonsa gare shi ya tsananta, da kuma kwaɗayinsa a kan dawwamarsa.
Madogara

صحيح البخاري (8/ 89) (6420). البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (20/ 36). إرشاد الساري لشرح صحيح البخاري (9/ 242).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
ZARGIN SON DUNIYA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com